19/07/2025
Dala dubu dari da hamsin kacal ($150,000) a asusun kansa, da kuma naira miliyan 30 ( ) a asusun Union, hannayen jari, shanu, fili biyu da ba a gina ba, da gidaje biyu. Babu asusun waje, babu dukiya a ƙasashen waje.
Mutumin da ya yayi shugaban ƙasa na dimokradiyya sau biyu, shugaban ƙasa a mulkin soja, shugaban PTF, da kuma minista a tarayyar Najeriya.
Mutum ne da ba za ka iya kiransa da barawo ba,
Mutum da ba za ka iya kiransa da mayen mata ba,
Mutum da ba za ka iya kiransa da makaryaci ba,
Mutum da ba za ka iya kiransa da munafuki ba.
Kuma shine mutumin da kake rawa saboda mutuwarsa, asara ce babba.
Ba mamaki, Ibo (Inyamirai) suke kiranka ABOKI,
Ba mamaki, suna kiran ku jahilai,
Ba mamaki, suna kiran ku akuya.
Kai JAHILCI MUSIBA NE.
Allah, wallahi, jahilci yafi hauka wuyar magani!
Allah ya kara rahama ga kabarinka Baba .