12/09/2025
YADDA IYALIN WANI LADANIN MASALLACI S**A SAMU KANSU BAYAN RASUWARSA 😭😭😭
Ina tsaye a wata majalisa sai na hango yarinya ƙarama yar shekara 9 zuwa 10 tana tallar mangwaro tana kuka, tana tafiya da kyar.
Na tambayi mutane a wurin me ya sa yarinyar ke kuka? S**a ce wai ba ta da kirki, duk lokacin da aka ɗora mata tallah haka take kuka.
Amma zuciyata ta ce “Bari inji dalili.” Na kusanto ta, sai na tambaye ta farashin mangwaron. Ta ce guda ɗaya ₦50 ne. Duk da haka, fuskarta babu annuri sai kuka kawai.
Na sayi dukkan mangwaron da kudinsa ya k**a ₦2,300. Nan take fuskarta ta chanza. Mun jima muna hira, sai ta ce min ba tallah ke sata kuka ba, ciwon ciki ne da take fama da shi tsawon watanni uku.
Na tambaye ta inda iyayenta suke. Ta ce mahaifinta ya rasu, mahaifiyarta kuma tana kwance a gida babu lafiya.
Na ce mu tafi gidan su. A mintuna kaɗan muka isa. Ashe uwar ma tana kwance tsawon lokaci, ba lafiya, gidan kuma k**ar bola ga kazanta, babu katanga.
An ce mahaifinsu mutumin kirki ne mai kiran Sallah. Amma duk da haka babu wanda ya taɓa kula da iyalansa ko kai musu taimako.
Na ɗauke su zuwa asibiti. Bayan gwaje-gwaje aka gano cewa hanjin yarinyar ya lalace saboda rashin kula da typhoid, ita kuma uwar tana da fibroid mai tsanani.
Aka yi musu aiki da kuɗi ₦560,000, cikin kwana biyu aka kammala. Bayan mako guda aka sallame su daga asibiti, aka ci gaba da basu abinci da magani har s**a murmure.
Bayan haka aka gyara gidan su gaba ɗaya ya koma sabo, aka saka yaran makaranta, aka kawo musu kayan sana’a don kada su sake komawa tallah.
Amma abin takaici, sai na ji maganganun mutanen gari wai dan majalisa ne ya turoni na yi musu taimako. 😔 Alhali basu taɓa zuwa ko kai musu magani ko bulo don rufe katangar gida ba.
Yarinya da aka ce “ba ta da kirki”, ashe rashin lafiya ce ke damunta. Mahaifiyar da take kwance a gida, babu wanda ya taɓa tunanin kai ta asibiti.
Rayuwa ta lalace idan har zuciyar mutane ta bushe da tausayi haka. Allah ya kyauta.
✍🏽Sani Rogo Aikawa
CEO/ Aikawa Charity Foundation
08082744019