21/12/2025
An Saki Sauran Dalibai da Malaman Makarantar St. Mary’s da Aka Sace a Jihar Niger
Rahotanni dake fitowa na nuni da cewa an saki sauran dalibai da malamai na makarantar St. Mary’s Catholic School, Papiri, da ke karamar hukumar Rafi a jihar Niger, wadanda aka sace a kwanakin baya.
Muhimmiya ta gano cewar sakin nasu ya biyo bayan kiran gaggawa da iyayen yaran s**a yi ga gwamnatin tarayya da ta jihar Niger, inda s**a bukaci a tabbatar da ‘ya’yansu sun dawo gida kafin ranar Kirsimeti, 25 ga Disamba.
Wani jami’in tsaro da ke da masaniya kan aikin ceto ya shaida wa jaridar Premium Times cewa, dukkan mutanen da aka sace a harin yanzu sun samu ‘yanci. Sai dai ya ce ba a tantance adadin wadanda aka saki a sabon rukunin ba.
Idan ba'a manta ba ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar da tsakar dare a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, inda s**a shiga harabar makarantar a kan babura.
Rahotanni sun ce sun shafe kusan awanni uku suna zagaya ɗakunan kwanan dalibai kafin su tafi da wadanda s**a sace zuwa dazuzzuka da ke kusa.
Har zuwa lokacin hada wannan labari, gwamnatin tarayya da ta jihar Niger ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan batun.
Lamarin ya sake tunatar da jama’a irin hare-haren satar dalibai da s**a taba faruwa a wasu sassan Najeriya, ciki har da shahararren harin Chibok a jihar Borno.
Muhimmiya – Labarai Masu Ma’ana.