Hankaka News

Hankaka News Domin Samun Ingantattun Labarai.....
(4)

🚨YANZU-YANZU : Alummar Kano Na Cigaba DA Shirye-shiryen tarbo Sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero , Wanda Ake sa ran saukan...
31/07/2026

🚨YANZU-YANZU : Alummar Kano Na Cigaba DA Shirye-shiryen tarbo Sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero , Wanda Ake sa ran saukan Shi a gobe Bayan dogo tafiya DA yayi zuwa kasan waje...

🚨TIRKASHI : Yadda gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tsaya domin sayan gyaɗa a bakin wani kasuwar ƙauye...
31/07/2026

🚨TIRKASHI : Yadda gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tsaya domin sayan gyaɗa a bakin wani kasuwar ƙauye kan hanyarsa ta komawa Maiduguri bayan ya kai ziyarar aiki wasu garuruwa da za a maida ƴan gudun hijira gidajensu.

DA ƊUMI-ƊUMI: Shahararren Jarumin Kannywood Adam A. Zango ya saki Matarsa Maimuna Pretty, bayan saɓani da s**a samu.Arew...
31/07/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Shahararren Jarumin Kannywood Adam A. Zango ya saki Matarsa Maimuna Pretty, bayan saɓani da s**a samu.

Arewa Update ta ruwaito cewa tuni Mainuna ta soma kwaso kayanta daga gidan.

Makusantansu sun tabbatar da faruwar lamarin, inda s**a ce sakin ya biyo bayan saɓanin da maʼauratan s**a samu.

Kazalika, an yi ƙoƙarin samun daidaiti kan lamarin amma abin ya ƙi yiwuwa.

Me za ku ce?

🚨 YANZU-YANZU : An Mayarwa Da Iyalan Ummulkhairi Da Aka Ƙona A Kaduna Da Hijabi, Takalmi Da WayartaWasu matasa ne s**a k...
30/07/2026

🚨 YANZU-YANZU : An Mayarwa Da Iyalan Ummulkhairi Da Aka Ƙona A Kaduna Da Hijabi, Takalmi Da Wayarta

Wasu matasa ne s**a kashe Ummulkhairi a Marabar Jos bisa zargin satar yara a watan da ya gabata

🚨 ALLAHU AKBAR : Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima tare da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ...
30/07/2026

🚨 ALLAHU AKBAR : Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima tare da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, sun halarci Jana’izar marigayi Alhaji Sardaunan Sokoto, wanda ya rasu a daren ranar Laraba.

An gudanar Da Jana'izar ne a Masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello da ke Kanwuri a garin Sokoto, inda manyan jami’ai da shugabanni s**a halarta.

🚨 WATA SABUWA : Wata Kotu Ta Yankewa Saudat Hukuncin Kisa Kan Kashe Mijinta Da Wuka A KanoBabbar kotun jihar Kano ta yan...
30/07/2026

🚨 WATA SABUWA : Wata Kotu Ta Yankewa Saudat Hukuncin Kisa Kan Kashe Mijinta Da Wuka A Kano

Babbar kotun jihar Kano ta yanke Saudat Jibrin hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same ta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris.

Mai shari'a Maryam Sabo, wadda ta jagoranci shari'ar, ta ce kotun ta gamsu da hujjoji da shaidun da masu gabatar da kara s**a gabatar inda s**a tabbatar da laifin wadda ake tuhuma.

Kotun ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya karkashin sashi na 221 .

🚨 ALLAHU AKBAR : Tsohon jakadan Najeriya a Birtaniya kuma Sardaunan Sakoto, Alhaji Abubakar Alhaji, ya rasu yana da shek...
30/07/2026

🚨 ALLAHU AKBAR : Tsohon jakadan Najeriya a Birtaniya kuma Sardaunan Sakoto, Alhaji Abubakar Alhaji, ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.

Ya rasu ne da safiyar Alhamis a Asibitin Alliance da ke Abuja bayan shafe makonni yana jinya, inda aka mayar da shi daga Asibitin Koyarwa na Jami'ar Usmanu Danfodiyo (UDUTH) da ke Sakoto kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

🚨 DA DUMI-DUMI : Yan Bidinga Sunkai Hari Kotu a Katsina Inda Alkali Ya Gudu Ta TagaWasu da ake zargin 'yan bindiga ne su...
30/07/2026

🚨 DA DUMI-DUMI : Yan Bidinga Sunkai Hari Kotu a Katsina Inda Alkali Ya Gudu Ta Taga

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari a kotun Shari'a da ke ƙauyen Gwarjo, ƙaramar hukumar Matazu a Jihar Katsina, yayin da ake tsaka da shari'a.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga harabar kotun suna harbe-harbe tare da neman Alƙali Mohammed Muktar. Sai dai alƙalin ya hango zuwansu tun kafin su isa kotun, lamarin da ya ba shi damar tserewa ta taga. An kuma ce wani ɗan acaba ne ya taimaka masa ya fice daga yankin cikin gaggawa.

Bayan sun kasa samun alƙalin, maharan sun yi barazanar kashe shi idan ya sake komawa gudanar da aikinsa a wannan al'umma. Harin ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin game da matsalar rashin tsaro da ke addabar wasu sassan Jihar Katsina.

🚨 LABARI : Yadda Peter Obi ya gana da ObasanjoƊan takarar shugaban kasa na jam'iyyarNDC, Peter Obi, ya gana da tsohon sh...
29/07/2026

🚨 LABARI : Yadda Peter Obi ya gana da Obasanjo

Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyarNDC, Peter Obi, ya gana da tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan rawar da Obasanjo zai iya takawa a zaɓen 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito wannan na zuwa ne bayan ƙungiyar Yoruba Ronu Leadership Forum ta yi zargin cewa Obasanjo na aiki a ɓoye domin ganin Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zaɓe, duk da cewa a fili yana goyon bayan wasu ’yan adawa irin su Peter Obi.

Me za ku ce?

DA DUMI-DUMI : Akwai alamar Jahilci a tattare da Shugaban kasar Burkina Faso, ba zaka iya fada sa Sunna da Addini baHawa...
29/07/2026

DA DUMI-DUMI : Akwai alamar Jahilci a tattare da Shugaban kasar Burkina Faso, ba zaka iya fada sa Sunna da Addini ba

Hawainiyarka ta kiyayi ramar Addini, idan kace baka son shari'ar Musulunci to ka daina Sallah mana.

Inji Sheikh Muhammad Bn Usman

Address

Kaduna
2234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hankaka News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share