03/04/2023
Daga Halayen Manzon Allah SAW (001)
Bismillah!
1. A Suratu Ali Imran aya ta 59 Allah madaukakin sarki yake yabon halin Manzon Allah SAW da cewa
âDomin rahmar Allah gareka ya sanya ka zamto mai taushin muâamala ga sahabbai, da ka kasance mai kaushin dabiâa, mai zafin hali da duk sun watse daga garekaâ.
2. A Sahihul Bukhari 2038, Anas dan Malik, wanda yake hadimin Manzon Allah SAW ne yake cewa
âNa hidimtawa Manzon Allah SAW tsawon shekaru goma, amma bai taba ce dani tir akan wani abu da nayi ba, bai taba ce dani me yasa kayi kaza ko me yasa baka yi kaza ba?â.
3. A Sahihul Bukhari 4971, Anas dan Malik ya rawaito cewa
âManzon Allah SAW ya kasance yakan zo inda muke domin ya duba mu. Anas yace ni kuma ina da wani kani karami da ake yiwa alkunya da Abu Umair, shi kuma yana da wani karamin tsuntsu (kanari) da yake wasa dashi. Kwatsam sai tsuntsun nan ya mutu! Yaro ya shiga damuwa har ya dena fita. Wata rana Manzon Allah SAW bai ganshi ba sai ya tambaya ina wannan yaro, sai aka ce dashi ai ya dena fita domin tsuntsun shi ya mutuđ. Manzon Allah SAW yace da sahabbai ku tashi muje mu yiwa yaron nan taâaziyyar tsuntsun shi. Suna shiga s**a same shi ya bata rai, sai Manzon Allah SAW yace dashi ya Abu Umair me ya faru da Nughair?â Manzon Allah SAW ya kira tsuntsun da nughair ne saboda yayi masa raha ya rage masa radadin abin dake damun sa.
Ya ku yan uwa, wannan fa shine Annabin mu. Tambayar ita ce;
To mu a ina muka samo halayen da muke dasu a yau?
Wassalaamu Alaykum.