07/09/2026
🌹 DAN UWA! 🌹
Karka daina tambayar kanka:
Yaya matsayin Annabi Muhammad ﷺ yake a cikin zuciyarka?
Idan ka ji a cikin zuciyarka cewa ka fi son iyayenka, ’yan uwanka, matanka, abokanka, dukiyarka, kasuwancinka, aikinka, ko wani abu daga cikin abubuwan duniya — har ma da rayuwarka gaba ɗaya — fiye da yadda kake son Annabi Muhammad ﷺ, to ka tsaya ka sake duba kanka.
Domin ƙaunar Manzon Allah ﷺ tana daga cikin manyan alamomin imani.
Idan har zuciyarka ta tabbatar maka cewa kana fifita wani abu a kan Annabi ﷺ, to idan ana maganar masu imani, ka yi shiru, kada ka yi gaggawar sa baki.
Idan kuwa za ka yi magana, ka ce:
🤲 “Ya Allah, Ka azurta mu da albarkacin bayinka salihai, Ka sanya ƙaunar Annabi Muhammad ﷺ ta fi komai a cikin zukatanmu.”
🌹 Allah Ya cika zukatanmu da ƙaunar Sayyadina Rasulullahi ﷺ. Ameen. 🌹