
19/07/2025
KANO TA DABO CI GARI.
SARKIN KANO WARISI DAN BAGAUDA (1063-1095) SARKIN KANO NA BIYU.
Bayan mutuwar Bagauda sai dansa Warisi ya dauki ragamar mulki. A wannan lokaci ne aka ba Warisi shawarar ya matsa lamba a kan Gazarzawa in dai har yana son ya mallaki kasa duka. An ce akwai wani babban gunki a Gazarzawa wanda mutanen wurin ke bautawa. Idan an ruguje gunkin, za a mallaki mutanen wurin da nasarori masu yawa wurin kafa Kano. Duk da haka Warisi bai wani yunkuri ba saboda manyanci na shekaru. Warisi ya mutu a nan Sheme bayan ya yi shekaru talatin da uku (33) a kan mulki.
SARKIN KANO GAJIMASU DAN WARISI (1095-1134) SARKIN NA UKU.
Ko da Gajimasu ya zama Sarki sai ya bar Sheme ya tafi Gazarzawa ya gina gida a wurin inda ya zauna da iyalansa. A wannan lokaci ne ya yaudari mazauna wurin da kyaututtuka wurin kokarinsa na sanin sirrin da s**a boye game da Tsumburbura. Da ya fara fahimtar abubuwa da ke lullube sai ya shammaci jama'a ya fara gina ganuwar Kano daga kofar Mazugal zuwa kofar Ruwa, sunnan ya dauko gini daga kofar Adama zuwa kofar Gadon kaya. Daga nan sai ya kara daukan gini daga kofar kansa Kali zuwa kofar Tuji inda ya zarce har zuwa kawankari da kofar Tuji.
A wannan lokaci ne aka fara gina harsashin Birnin Kano. A wannan lokaci ne kuma Gajimas ya fara kokarin fadada kasar Kano inda ya mallaki Gano da Dabai da Ringim da Kuma Danbakon Yaki. An ce ya sami nasaran mallakar al'ummomi da ke Dala da wadansu da ke gewaye da ita. A wannan lokaci ne alamun kafuwar Birnin ya kanama inda baki s**a fara shiga Kano. Ya yi shekaru arba'in (40) a kan mulki ya mutu
SARAKUNAN KANO NAWATA DA GAWATA (1134-1136) SARAKUNAN KANO NA HUDU.
Nawata da Gawata tagwayen 'ya'ya NE ga Sarkin Kano Gajimasu wadanda s**a yi Sarautar a lokacin guda. Babu wani bayani a rubuce yanda aka yi mutane biyu s**a yi Sarauta a lokaci guda amma tarihi ya tabbatar da hawa mulkinsa a lokaci daya. An tabbatar da cewa kowane guda daga cikinsu yana rike mashi idan zai fito Fada. Wadannan masu guda biyu su ne aka game su wuri guda a Zamanin mulkin Sarkin Kano Abdullahi Bayero (1926-1953), aka sami Tagwayen Masu. An ce daya daga cikin Tagwayen ya mutu bayan sun hau Sarauta da watanni goma Sha daya. Daga bisani kuma sai dayan ya mutu bayan ya yi shekara biyu akan karagar mulki.