
07/06/2025
Sakonnin Babbar Sallah da aka gabatar jiya Juma’a 10 Ga Watan Zhul-Hajj 1446 wanda yayi daida 06 June, 2025 na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamati Sunnah ta Jihar Katsina
1. GODIYA GA ALLAH:
Muna godiya ga Allah (S.W.A) da ya kawo mu wannan rana ta idin babbar salla ta shekarar 1446/2025. Muna rokon shi da ya karbi ibadun mu, ya sanya mun dace da dukkanin alkahiran da ke cikin ranar Arfah da ta gabata ranar Alhamis
Alhazan da ke cikin aikin hajji muna rokon Allah ya sanya su yi cikin nasara, su gama lafiya ya kuma maida su gida lafiya
2. MUMMUNAR AKIDA:
Kira ga Malamai akan kara maida hankali wajen karantar da alumma musamman abinda ya shafi Akida domin kaucewa fadawa tarkon zindikai masu amfani da sunan Malunta suna 6atar da alummah
Musamman yanzu da aka samu bayyanar masu akidar batanci ga Hadisan Manzon (S.A.W) da sunan Akidar Kur’ani Zalla a wannan Jiha ta mu ta Katsina
Lallai malamai su kara kokari domin yakar wannan mummunar akida domin kubutar da al’ummar mu daga dukkanin wani sharri da ke cikin ta
3. FATTUN LAYYA:
Kamar yadda aka sani cewa duk shekara Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamati Sunnah ta kan neme gudummuwar sadakar fatun layya daga hannun al’ummar musulmai a fadin Najeriya
A saboda haka ne a wannan shekarar 1446/2025 itama muna kira ga al’ummar musulmai da ke fadin wannan Jiha ta mu mai albarka Jihar Katsina da su bada gudummuwar fatun layyarsu ga wannan Kungiya kaman yadda su ka saba domin cigaba da ayyukan alkhairi da wannan ta ke gudanarwa musamman yanzu da ake aikin ginin Jami’ar As-Salam da ke garin Hadejia Jihar Jigawa mallakar Kungiyar
Za’a iya kai gudummuwar fatun a dukkanin masallatan juma’a/ kamsus salawat na Kungiyar da ke fadin Jihar Katsina
Ga wadan da Allah bai ba su damar yin layya baa kwai rasidi na kudi N100, 200 da N500 da za su iya bada ta su gudummuwar da shi domin a hadu cikin lada
4. TSARO:
Muna yaba ma Gwamnatin Jihar Katsina akan yadda ta dauki maganar matsalar tsaro da muhimmanci wanda mun gani a aikace yadda aka dauki ma’aikatan jami’an tsaron cikin gida (C-Watch) har sau biyu duk domin ganin an magance matsalar rashin tsaron. Kuma muna ganin irin kokarin da jami’an ke yi tun lokacin da su ka fara aiki a yan kunan da ake fama da wannan matsala har zuwa yanzu
Dan haka muna kira ga Gwamnati akan kara daukar matakan da duk su ka kamata domin ganin an magance wannan matsala
Haka kuma muna kara kira ga al’umma lallai su ci gaba da bada ta su gudummuwar ga jami’an tsaro da ita kan ta gwamnati wajen ganin an magance matsalar rashin tsaro
5. YAN SIYASA:
Muna kira ga yan siyasar mu musamman wadan da ke akan madafun iko a halin yanzu da su ji tsoron Allah wajen tabbatar da sun sauke nauyin da Allah ya daura masu na al’ummar da su ka zabe su wajen kawo masu ayyukan alkhairi da samar masu abubuwan more rayuwa da dogaro da kai ba wai zuwa ana ba su abinda bai taka kara ya karya ba wanda ko kishirwa ba zai kashe masu ba da sunan tallafi
6. IYAYE:
Muna kira ga iyaye da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin amanar da Allah ya ba su ta yaransu musamman wajen kula da abinda ya shafi tarbiyarsu
Dole ne a sanya idanu akan su yayin da ake hidimar sallah saboda kada su je su na akaita abinda zai janyo fushin Allah. A kwaidatar da su wajen kai ziyarori wajen yan'uwa da abokan arziki da kuma ja masu kunne na kauce ma wajajen da ake haduwa domin sharholiya
7. DOGARO DA KAI:
Wajibi ne alummarmu su maida hankali kan neman ilimin addini da na boko da koyon sanaoin hannu musamman ga matasan mu. Da yin niyyar yin aiki da abinda aka koya din, wannan zai taimaka wajen dogaro da kai da rage zaman banza musamman ga matasan mu
8. TALLAFAWA MASU RAUNI DOMIN RAGE RADADIN HALIN DA AKE CIKI:
Muna kira akan tallafa ma masu rauni daga cikinmu musamman marayu da zawarawa da nakasassu da gajiyayyu don rage masu radadin talauci da tsadar rayuwa da ake fama da ita a wannan lokaci
Kuma tallafawar kada ta tsaya kadai ga abinci ta hade duk wani abu da dan Adam ke bukata
9. IFTILA’IN AMBALIYAR RUWAN SAMA:
Muna amfani da wannan dama domin jajantama al’ummar garin Mokwa na Jihar Niger akan iftila’in ambaliyar ruwan da ya samesu a satin da ya gabata.
Muna rokon Allah ya jikan wanda da su ka rasu, ya ba iyalansu hakurin rashi, wadan da s**a rasa dukiyarsu ko muhallin su ya maida masu da mafi alkhairi ya kuma kare faruwar hakan a gaba
10. KOMA WA GA ALLAH:
Wajibi ne dukkanmu mu koma ga Allah, mu tuba zuwa gare shi musamman cikin wannan yana yi da muke ciki na fargabar rashin tsaro, tsadar rayuwa. Domin babu wata musiba da ke samun mutane sai dalilin abubuwan da s**a aikata da hannuwansu. Don haka kuma, hanya daya wadda za mu bi Allah ya yaye wandannan musibu shine ta hanyar tuba da koma zuwa gareshi
11. ADDUA:
Kira ga Limaman Juma'a da na Khamsus Salawat da wajen darussa akan cigaba da gabatar da addu'o'in zaman lafiya da kuma yana yin da ake ciki, akan Allah ya kawo mana saukin shi ta hanyar da ba mu tsammani
12. Daga karshe muna kira ga Yan Agaji da Yan Hisbah su yi shiri a wannan lokaci dan kaucewa da kuma magance duk wata fitsara da za'a kawo da sunan bukukuwan sallah a fadin wannan Jiha ta mu ta Katsina baki daya
Muna rokon Allah (S.W.A) ya kara mana zaman lafiya da lumana a wannan Jiha ta mu da ma kasa baki daya. Muna rokon ya aza dukkannin ayyukan mu a mizanin ayyukan alkhairiya saka ma kowa da mafificiyar sakayya ta jannatul Firdausi. Amin
Wassalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuhu
Yusuf Hassan Buhari
Darakta JIBWIS Social Media
Na Jihar Katsina