12/01/2026
TUNABAYA
Fahimta Fuska-Dokar Aure A Danbatta Ina Ma da Sauran Garuruwa Za Su Yi Koyi Da Ita
Cikakken bayanin kundin takaita al'adun aure da aka kaddamar a ranar 2-01-2017 a fadar mai girma sarkin ban Kano hakimin Dambatta. Dakta Mukhtar Adnan wanda mataimakin shugaban kwamitin Alh. Ado Muhammad ya karanta kamar haka
Mu mutanen Dambatta bisa jagorancin mai girma Sarkin Ban Kano Hakimin Dambatta Alhaji Dakta Muhktar Adnan tare da shugabancin qaramar
hukumar Dambatta Dagatai da masu Unguwanni Limamai da Dattawan gari da sauran al'umma maza da mata mun yarda mun amince da kundin doka wanda zai takaita al'adu wajen neman aure tsakanin samari da yammata da zawarawa.
-Sashe na 1 kudin Aure/Baiko.
Dubu goma zuwa Dubu Ashirin.
Mutum daya ko biyu za a tura domin yin baiko bayan iyayen mace sun karbi kudi sun amince.
Ba a yarda a dorawa wanda aka yi wa baiko
wata wahala ba.
An haramta neman auren yarinya bayan an yi mata baiko.
Idan aka samu iyaye sun saba wannan doka, ko wani saurayi ko bazawari ya saba alhali yana sani, zai fuskanci hukuncin dauri ko zabin
biyan tara adadin kudin Aure/baiko a gaban
kuliya.
-Sashe na 2 kayan lefe.
Idan mutum ya zabi yin lefe to an taqaita lefensa
kamar haka:
Hijabi, mayafi, takalmi, jaka, sarqa, awarwaro,
'yan kunne, da man gashi, guda biyu-biyu.
Jagira, jambaki, hoda, agogo saiti daya-daya
(set).
Turare 3, Sabulu saiti 3.
Bireziya da shimi hur-hudu.
Tufafi turmi 6, fant 6, man shafawa 6.
Akwatu daya zuwa biyu.
An taqaita lefen bazawara qasa dana budurwa, kuma kada ya wuce na budurwa.
-Sashe na 3 Sadaki.
Sadaki gwargwadon nisabin shara'ar musulunci wato Rubuid-dinar.
An yarda iyaye su yi yarjejeniya akan sadaki ko biya a dunqule a auren budurwa ko bazawara tare da sa idon kwamitin unguwa.
-Sashe na 4 kayan daki.
A taqaita kayan daki, dana kichin, a guje wuce
gona da iri, alfahari da gasa.
Za a iya yin walima kamar yadda addinin
musulunci ya tanada, ba tare da cudanyar maza
da mata ba.