
12/08/2025
Rahoton rashin lafiyar Tinubu ƙarya ne - Fadar shugaban ƙasa
Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta musanta rahotannin da ke nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya kuma ana shirin fitar da shi zuwa asibiti a ƙasar waje.
BBC Hausa ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne dai cibiyar aikin jarida mai binciken ƙwaƙwaf ta Najeriya, ICIR ta rawaito cewa wasu majiyoyinta sun tabbatar mata da cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na ta shirye-shiryen fitar da shugaba Tinubu zuwa ƙasar wajen domin neman magani.
Cibiyar k**ar dai yadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce "rahotanni na nuna cewa shugaba (Tinubu) na kwance a gado ba ya iya zuwa ko'ina abin da ya janyo rashin gudanar da al'amuran shugabanci. Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban a wasu ayyukan gwamnati."
ICIR ta kuma rawaito wani jami'i a fadar shugaban ƙasar da ke cewa an soke aikace-aikace da dama da ya k**ata shugaban ya gudanar a farkon makon da ya gabata.
Mai magana da yawun shugaba Tinubu, Abdu'aziz Abdul'aziz ya shaida wa BBC cewa rahotannin ba gaskiya ba ne.
Babu ƙanshin gaskiya a waɗannan maganganun. Yanzu haka ma yana ofis", in ji Abdul'aziz.
Da ma dai tun a farkon makon da ya gabata sai da Bayo Onanuga mai taimaka wa shugaba Tinubun kan harkokin watsa labarai shi ma ya musanta batun a tattaunawarsa da ICIR.
" Shugaba Tinubu yana aikinsa. Yana da salon gudanar da aiki iri-iri. Wataran ma yana iya yin aiki daga gida. Zancen gaskiya ma ya fi yin aiki daga gida a kan na ofis. Duk mutumin da ke yin wannan batu to lallai ya sani labarin ƙanzon kurege yake yaɗawa.