15/06/2025
Farfesa Abdullahi Sale Usman yayi Nasarar gudanar da aikin hajji bana
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban hukumar aikin hajji ta ƙasa, (NAHCON) farfesa Abdullahi Sale Usman yayi gagarumar nasara a gudanar da aikin hajjin bana ta shekarar 2025/1446.
Nasarar ta ƙunshi yadda aka kwashe alhazai cikin sauri a lokacin tafiya, da ya yadda aka fara dawo da su a lokacin dawowa.
Kazalika shugaban yayi tsari mai kyau a lokacin zaman Mina na ranar 8 ga wata, da ranar Arfa wato 9 ga wata, da dawowa Mina bayan arfa, inda aka samu wadatuwar abinci da abun sha, gami da wuraren kwanciya na alfarma ba tare da ko wane irun ƙorafi ba. Suma manyan jami’an gwamnatin tarayya inda aka karrama su da waɗannan abubuwa na more rayuwa, ƙarshe akayi ta murna ana barka barka.
Shugaban na NAHCON Farfesa Usman, haka ya dinga zaga tanti tanti yana tambayar ko akwai matsala da ya shafi wani alhaji, ba tare da girman kai ko nuna isa ba, har aka kammala zaman Mina ba’a samu matsala ko wace iri ba.
Farfesa ya ɗebo malamai daga sassan ƙasa domin su karantar da malamai haƙiƙanin aikin Hajji, kuma sunyi ƙoƙari wurin aikin da aka su, haka aka ɗauki likitoci s**ayi ta faɗi tashi domin kula da lafiyar alhazai.
Suma ‘yan uwa ‘yan jarida basu tsaya wasa ba, sunbi diddigin aikin inda s**a dinga ɗebo labaran gaskiya suna yaɗa shi a faɗin duniya, kuma al’umma sun gani sun yaba, jinjina ga shugaban Labaru ta NAHCON mataimakiyar Darakta Fatima Sanda Usara da masu taimaka mata daga hukumar, Allah ya sakawa kowa da alheri.
Shugaban NAHCON bai tsaya anan ba, ya samar da masauƙai masu kyau a zaman Madina da makkah, waɗanda ke kusa da harami, in ka ɗebe guda ɗaya dake makkah wanda sai an shiga taxi za’a iso harami, amma shima Hotel ne na kece raini in ka duba irin Hotel din da ake sauke masu ruwa da tsaki da ma’aikatan da NAHCON take ɗauka su tayata aiki a baya.
A Daidai wannan lokaci muke yabawa shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Sale Usman a wannan namijin ƙoƙari da yayi, kuma dama haka muke tsammani, domin an aje kwarya ne a gurbinta, kasancewarsa Malami mai wa’azi, wanda yasan dokoki da hakki na amanar da aka ɗora masa.
Fatan mu dai shine Allah ya bada ikon kammala dawowar alhazai cikin aminci. Amin
Ibrahim Baba Suleiman
National Director Media
Jibwis Nigeria
Jibwis Nigeria