AREWA INFO TV

AREWA INFO TV Arewa Info Tv Kafa ce da aka Ƙirƙira Domin Yaɗa Sahihan Labarai, Al'adu, Nishaɗi Cikin Harshen Hausa.

Wani Bincike Da Aka Gudanar an gano Wani kifi Wanda Yayi Shekaru Miliyan 70 Wanda Har yanzu Yana Raye, An gano kifin da ...
21/08/2025

Wani Bincike Da Aka Gudanar an gano Wani kifi Wanda Yayi Shekaru Miliyan 70 Wanda Har yanzu Yana Raye, An gano kifin da aka ɗauka cewa ya shuɗe tun shekaru miliyan 70 da ta wuce

Masu bincike a gabar tekun Indonesia sun yi nasarar ɗaukar hoto na wani kifi mai suna Latimeria menadoensis (coelacanth), wanda aka yi tunanin ya ɓace tun kafin dinosaur su shuɗe. An ga kifin ne a cen cikin ruwa a zurfin sama da mita 140, inda tawagar masana s**a yi amfani da kayan bincike na musamman. Gano kifin ya tabbatar da cewa har yanzu yana raye a cikin tekun duniya.
AREWA INFO TV

RAHOTO: Masu yi mana rashin kunya a social media, ku sani muna da yara da za mu iya sakawa su yi wa mutum duka. Kai ko r...
21/08/2025

RAHOTO: Masu yi mana rashin kunya a social media, ku sani muna da yara da za mu iya sakawa su yi wa mutum duka. Kai ko ran mutum muka ce muna so za su ɗauko mana - Sheikh Musa Asadussunah ya gargaɗi 'yan media.
AREWA INFO TV

DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji ba zasu iya magance rashin tsaron arewa ba ~ Gwamnan KadunaGwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayya...
20/08/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji ba zasu iya magance rashin tsaron arewa ba ~ Gwamnan Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa yaƙin sojoji da sauran hukumomin tsaro kaɗai ba zai wadatar wajen kawo ƙarshen ta’addanci da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a Arewacin Najeriya ba.

Yayin wani taron ƙoli na jihohin Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna kan rige tsattsauran ra’ayi, gwamnan wanda kwamishinan tsaro na cikin gida, Sule Shuaibu, ya wakilta ya ce tushen matsalar rashin tsaro ya samo asali ne daga talauci, rashin adalci, cin hanci, rashin shugabanci nagari da kuma rashin damar samun aiki ga matasa.

Sani ya jaddada cewa har sai an magance waɗannan dalilai, nasarorin soji za su kasance. Ya yi kira da a ɗauki matakan haɗin gwiwa, haɗa kan al’umma, girmama haƙƙin ɗan adam da tabbatar da adalci wajen yaki da ta’addanci.

Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Adamu Laka, ya goyi bayan wannan ra’ayi, inda ya ce ana bukatar tsari na al’umma da ya dogara da bayanan sirri wajen magance matsalar.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin shekaru biyu da Gwamna Sani ya shafe a kan mulki, mutane 485 aka kashe yayin da sama da 1,700 aka yi garkuwa da su a Kaduna.

Me zaku ce dangane da wannan furucin nasa??

Imam Junaidu Abubakar ya Ziyaran sayyidah fadimatul anwar bint hasan bin zaid bin hasan bin Aliyu bin abi dalib.Wani Fat...
20/08/2025

Imam Junaidu Abubakar ya Ziyaran sayyidah fadimatul anwar bint hasan bin zaid bin hasan bin Aliyu bin abi dalib.

Wani Fata Zaku masa?

Muhimman abubuwa 6 da ka iya faruwa idan da Rana zata ɓace ɓat daga sararin samaniya.1.  Idan da zata ɓace da tsakar Ran...
20/08/2025

Muhimman abubuwa 6 da ka iya faruwa idan da Rana zata ɓace ɓat daga sararin samaniya.

1. Idan da zata ɓace da tsakar Rana, to ba zamu iya gane hakan ba har sai bayan mintuna 8 da faruwa, domin yana ɗaukan haske mintuna 8 ya riskemu daga Rana.
2. Duniyarmu zata daskare saboda tsananin sanyi, yanayin zafi zai zama tarihi.
3. Tsirrai/bishiyoyi zasu rasa sinadarin photosynthesis da suke samu daga Rana, wanda hakan zai sa rayuwarsu ta tagayyara.
4. Duniyarmu zata rasa tauraruwar da zata ke kewayewa, zata koma gallafiri a sarari babu gurin zuwa.
5. Duniyarmu zata iya rasa maganaɗisun magnetic field da ke kare ta daga haɗarurruka da ke cikin kaunu.
6. Za'a rasa rayukan halittu da tsirrai bila adadi, ko ma dukkanin su da mu baku ɗaya.

AREWA INFO TV

RAHOTO: Babbar kotun jihar Plateau da ke Jos ta ba da belin mutane 20 da ake zargi da kashe matafiya ɗaurin Aure su 13 a...
20/08/2025

RAHOTO: Babbar kotun jihar Plateau da ke Jos ta ba da belin mutane 20 da ake zargi da kashe matafiya ɗaurin Aure su 13 a ƙauyen Mangun na karamar hukumar Mangu.

An ɗage shara'ar sai zuwa ranar 13 ga watan Oktoba, 2025.

DA ƊUMI-ƊUMI: Yawan mutanen da s**a mutu a harin masallaci a Malumfashin jihar Katsina ya kai 30.“An kashe mutane tara a...
20/08/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Yawan mutanen da s**a mutu a harin masallaci a Malumfashin jihar Katsina ya kai 30.

“An kashe mutane tara a wurin nan take, sannan wasu da dama sun mutu a yinin ranar. Adadin yanzu ya kai 32,” in ji wani mazaunin yankin mai suna Nura Musa a ranar Laraba.

Abubuwa 5 masu matuƙar hatsari a Kaunun nan ta Maliki yaumiddini1. Black hole: Wannan shi ake ƙira da Bakin rami ko kuma...
20/08/2025

Abubuwa 5 masu matuƙar hatsari a Kaunun nan ta Maliki yaumiddini

1. Black hole: Wannan shi ake ƙira da Bakin rami ko kuma maƙabartar taurari. Zuƙo taurari yake yana haɗiye su kamar yadda ka ke zuƙe taliya.
2. Supernova: Wannan shine tarwatsewar narkekiyar tauraruwa dangin Rana. Irin wanga al'amari yana kawo ƙarshen duk wata duniya da ke ɗawafi ga ita tauraruwar. Sun ƙonewa ƙurmus su zagwanye gaba ɗaya.
3. Neutron Star: Yayin da tauraruwa irin Rana ta tarwatse, tsakiyan tumbin ta ke komawa Neutron Star. Yana da matuƙar haɗari, domin yana fitar da wani haske mai lauje/bindi, wannan bindi kaɗai idan ya sauƙa kan duniyarmu, zai iya yanka ta gida biyu nan take.
4. Asteroids/Comets: Waɗannan sune narka narkan duwatsu da ƙanƙara masu shawagi a sararin samaniya. Akwai hasashe mai ƙarfi cewa an taɓa yin ruwansu a wanga duniyar tamu, wanda hakan ya janyo rasa rayuka bila adadi.
5. Solar flares: Wannan kuma shine hucin Rana. Shi kaɗai ya isa ya ƙone duniyarmu, amma maganaɗisun magnetic field da hijabai na iska na duniyarmu na matukar ƙoƙari wajen tace wannan huci mai haɗari, iya marar haɗari ke samun damar shigowa garemu.

AREWA INFO TV


゚viralシfypシ゚viralシalシ

Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe mutane 13 a yayin sallar Asuba ranar Talata, a wani h...
19/08/2025

Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe mutane 13 a yayin sallar Asuba ranar Talata, a wani harin ramuwar gayya da s**a kai Unguwar Mantau a karamar hukumar Malumfashi.

Kakakin ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina.

Ya ce, “Lamarin ya faru ne lokacin da miyagu s**a kai hari domin ramuwar gayya a kan al’ummar garin. Mambobin al’umma Musulmi na cikin masallaci suna yin sallar Asuba, sai waɗannan ’yan ta’adda s**a fara harbe-harbe cikin masallacin.”

Kwamishinan ya kara da cewa harin ramuwar gayya ne kan yadda al’ummar unguwar s**a yi nasarar dakile su a kwana biyu da s**a gabata.

A cewarsa, mutanen Unguwar Mantau sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna inda s**a kashe da dama daga cikinsu.

Bayan wannan mummunan lamari, Muazu ya bayyana cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Ya ce, “Kwamandan bangaren sojojin sama na FOB da kuma ’yan sandan Najeriya sun isa wajen domin kawar da wadannan ’yan bindiga. A lokacin damina, ’yan bindiga kan ɓuya a cikin amfanin gona domin aiwatar da munanan hari. Muna aiki tukuru domin ganin mun kamo su tare da hukunta su.”

Gwamnatin jihar ta yaba da jarumtar al’ummar Unguwar Mantau, tare da bayyana aniyar ta na ci gaba da yaki da ’yan bindiga da tabbatar da tsaro a dukkan al’ummomi.

“Hakika gwamnati na mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa,” in ji Muazu.

AREWA INFO TV

RAHOTO: Ga masu lissafin cewa duniyarmu a shimfiɗe take kamar tabarma. Duk da cewa tabbas a shimfiɗe take, amma ba irin ...
19/08/2025

RAHOTO: Ga masu lissafin cewa duniyarmu a shimfiɗe take kamar tabarma. Duk da cewa tabbas a shimfiɗe take, amma ba irin yadda yake a hoton nan ba. Yanzu idan mutun ya samu ƙwallon tamola da takai girman garin Kano ya ɗaura tururuwa a kanta, duk yawon da wannar tururuwa zata yi, to a shimfiɗe zata ga wannan tamola saboda bambancin girma da ke tsakaninsu. To kamar haka muke akan duniyarmu, girmanta ya wuce mutum ya fahimci a mulmule take kai tsaye. Shi yasa muke kallonta kamar a shimfiɗe.

Ɗaya daga cikin abubuwan da wannan hoto ba zai iya fayyacewa ba shine.
Shigan Rana cikin yini, da kuma yini cikin rana.

Yanzu haka da muke farkon dare, to Rana bata faɗi ba a ƙasar America, ƙasar China kuma gari na ƙoƙarin wayewa. Idan duka duniya a shimfiɗe take kamar yadda hoton nan yake, to duka duniya zata kasance cikin rana lokaci guda, haka nan dare zai yi lokaci guda duk duniya, wanda kuma ba hakan ne ke faruwa ba a zahiri.

AREWA INFO TV

DA ƊUMI-ƊUMI: Albashin N70,000 na Gwamnatin Tinubu bai yi tasiri ba saboda faduwar Naira -inji AmurkaMa’aikatar Harkokin...
19/08/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Albashin N70,000 na Gwamnatin Tinubu bai yi tasiri ba saboda faduwar Naira -inji Amurka

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Amurka ta ce sabon albashin ƙasa na N70,000 da Najeriya ta amince da shi bai yi tasiri ba saboda faduwar darajar Naira da kuma hauhawar farashi.

Masu sharhi sun nuna cewa ko da albashin ya ƙaru, ƙarancin ƙarfin saye da tsadar rayuwa sun sa bai wadatar ba.

Me zaku ce?

Shin dubu N70,000 na iya ciyar da magidanci?

TIRƘASHI: Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya amince da rage kuɗin wankin ƙoda daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 a manyan as...
19/08/2025

TIRƘASHI: Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya amince da rage kuɗin wankin ƙoda daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan bayanai, Daniel Bwala, ya bayyana cewa wannan sauƙi zai taimaka wa dubban marasa lafiya da ke fama da cututtukan ƙoda.

Sai dai asibitocin tarayya da ke jihohin Arewa maso Yamma Kano, Kaduna, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi babu su a cikin jerin asibitocin da za a fara aiwatar da tallafin.

Rahotanni sun nuna cewa Jigawa na daga cikin jihohin da ke da yawan masu fama da cutar ƙoda a Nijeriya.

Daga cikin asibitocin da aka fara aiwatar da wannan rangwame sun haɗa da, FMC Ebute-Metta (Lagos), FMC Jabi (Abuja), UCH Ibadan, FMC Owerri, UMTH Maiduguri, LUTH Lagos, FMC Abeokuta, FMC Azare, UBTH Benin, da UCTH Calabar.

Jama'a Me zaku ce akan wannan Mataki??

Address

Kaduna
80026

Telephone

+2348081217123

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA INFO TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AREWA INFO TV:

Share