Vidia.ng Hausa

Vidia.ng Hausa Kafar yada labarai ta zamani, sahihiya wajen kawo labaran siyasa, tsegumi, nishadi, wasanni, al'adu

Tinubu ya gabatar da manyan ayyuka tun hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.Daga ciki akwai cire tallafin man fetur da...
12/06/2023

Tinubu ya gabatar da manyan ayyuka tun hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Daga ciki akwai cire tallafin man fetur da kuma nada sabbin muk**ai da dama.

A mako na biyu ya dora da muhimman ayyuka da s**a hada da dakatar da Emefiele na CBN.

Shugaba Tinubu ya gudanar da wasu manyan sauye-sauye a makonsa na biyu da darewa kan karagar mulki. Da yawa daga cikin matakan nasa sun yi wa 'yan Najeriya.

Farashin Man Fetur na Gab da Faduwa - NNPCShugaban Ma'aikatan Kamfanin Matatar Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari,...
01/06/2023

Farashin Man Fetur na Gab da Faduwa - NNPC

Shugaban Ma'aikatan Kamfanin Matatar Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, a ranar Alhamis, ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya kan tsoron cigaba da hauhawar farashin man fetur a fadin kasar.

Shugaban NNPC ya ce, gasar dake tsakanin manyan 'yan kasuwar man fetur ne zai jawo saukar farashin da ya tada hankalin 'yan kasa.

Punch ta ruwaito yadda gidajen mai s**a cika makil da layi a fadin kasa, bayan karin kudin bututun man fetur da aka yi cikin kwanakin nan bayan cire tallafin man fetur din.

Yayin jawabi a wata tattaunawa da Arise TV a shirin safe, Kyari ya ce, cire tallafin zai ba sabbin 'yan kasuwa damar shiga kasuwancin tare da taimakawa wajen jawo gasa tsakanin 'yan kasuwa.

Kamar yadda ya ce, "Wani abu mai kyau game da cire tallafin shi ne, za a samu sabbin 'yan kasuwa a harkar, wanda hakan zai zaburar da kamfanonin da basu da niyyar sauke farashinsu a kasuwanin mai su rage farashi.

"Daga lokacin da aka fara gasa, mutane zasu fi zuwa inda yafi saukin farashi, sannan 'yan kasuwa zasu maida hankali kan kasuwancinsu yadda zasu jawo hankalin jama'a da dama. "

Likitan Da ke Dirkawa Marasa Lafiya Ciki ya Rasa Ransa a Hatsarin Jirgin Sama Wani likita, Morris Wortman da ke zaune a ...
31/05/2023

Likitan Da ke Dirkawa Marasa Lafiya Ciki ya Rasa Ransa a Hatsarin Jirgin Sama

Wani likita, Morris Wortman da ke zaune a Rochester, New York, Amurka, ya rasa ransa a jirgin gwajin da ya yi hatsari a harabar alkaryar Orleans ranar Lahadi.

An zargi likitan mai shekaru 72 da amfani da ruwan maniyyinsa wajen dirkawa marasa lafiya juna biyu.

Wortman ya mutu cikin wani jirgin saman da matukin jirgin, Earl Lucr Jnr na Brockport, ya kera da hannunsa, k**ar yadda jaridun Amurka s**a bayyana.

Hukumomin sun bayyana yadda jirgin saman ya fado yana tsaka da yawo a sararin samaniya gami da tarwatsewa, k**ar yadda Hukumar Kula da Sufuri na Kasa ya bayyanasa a jirgin saman Wittman W-5 Buttercup.

Yayin aka gudanar da wani bincike ranar Talata, an gano yadda "fuka-fukan jirgin s**a rabu da gangar jikinshi gami da dirowa kasa kan wata bishiya."

Sheriff Christopher Bourke ya kara da cewa, a wani labari da ya fita ranar Litinin, gangar jikin ya cigaba da yawo ta gabas da karin nisan 1,000 zuwa 1,500 mita kafin ya tarwatse.

Dr Wortman ya yi fice a yammacin New York, kuma yana daga daga cikin masu zanga-zanga kan yaki zubar da ciki.

A 2021, ɗiyar daya daga cikin marasa lafiyansa da ta dauki ciki a 1980s ta makashi kotu.

An zargi Dr Wortman da amfani da ruwan maniyyinsa ba bisa ka'ida ba yayin da ya fada wa mara da ke son daukar juna biyu cewa, wanda ya bata kyautar ruwan kwayar halittarsa dalibin likitancin yankin ne.

An gano yadda likitan boye sirrin duk da ɗiyarsa ta cikinsa zama mara lafiyarsa da ke fama da matsalar haihuwa.

Bayan yin kwajin DNA, ɗiyar ta gano yadda take da a kalla 'yan uba tara, k**ar yadda ya nuna a karar da ta shigar.

Karar ta bayyana yadda, bayan fitar sak**akon DNA na ɗiyar Dr Wortman na aurensa na farko, ya tabbatar da alakar halittar.

Bai yi tsokaci ba har zuwa lokacin da aka shigar da karar.

Anyi Garkuwa da Shugabannin APC Mata a Kan Hanyar Dawowa Daga Rantsar da GwamnaAn yi garkuwa da shugabannin mata guda bi...
31/05/2023

Anyi Garkuwa da Shugabannin APC Mata a Kan Hanyar Dawowa Daga Rantsar da Gwamna

An yi garkuwa da shugabannin mata guda biyu na jam'iyyar APC a wajen Manini na karamar hukumar Birnin Gwari kan hanyarsu na dawowa daga rantsar da sabon gwamna, Sanata Uba Sani, ranar Litinin.

Shugaban Cigaban Kungiyar Masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kasai ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna da safiyar Laraba.

Kamar yadda ya bayyana, 'yan bindiga sun toshe titin gami da sake biyu daga cikin shugabannin matan jam'iyyar APC tare da wasu magoya baya masu tarin yawa.

A cewarsa, shugabannin matan APC sune Shugabar matan APC na Birnin Gwari, Hajiya Lami Awarware da Mataimakiyarta, Hajiya Haulatu Aliyu.

An tattaro yadda masu satar mutanen s**ayi aka yi garkuwa dasu ranar Talata gami da tafiya dasu daji.

Shugaban BEPU, ya ce, har yanzu masu garkuwan basu tuntubi iyalan wadanda s**a sace ba, kuma basu bukaci kudin fansa ba.

Gudun Barkewar Rikici ya Hanani Halartar Bikin Ranstar da Abba Gida-Gida  - GandujeGwamnan mai barin Gado na Jihar Kano,...
31/05/2023

Gudun Barkewar Rikici ya Hanani Halartar Bikin Ranstar da Abba Gida-Gida - Ganduje

Gwamnan mai barin Gado na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dalilin da yasa bai je rantsar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

Ya ce, dalilin da yasa bai je rantsarwan ba saboda yana tsoron rikici da ka iya barkewa tsakanin magoya bayansu.

Ganduje ya sanar da hakanne a wata tattaunawa da BBC Hausa ranar Talata.

Kamar yadda ya ce, bai da wata jikakka tsakaninsa da sabuwar gwamnatin jihar.

Tsohon gwamnan Kano ya ce, "Za a iya raba mika mulki gida biyu. Na farko shi ne mika mulki, wanda ya hada da mika takardu da bayanai kan ayyukan gwamnati, duk da kwangilolin da aka kammala, da wadanda ba a kammala ba, gami da shawarwari ga gwamnati mai zuwa.

"Na biyu shi ne rantsarwa. Idan gwamnati mai barin gado da sabuwar gwamnati sun fito daga jam'iyyu mabambanta, ba dole bane sai an talarci rantsarwan, duba da akwai tarkewar rikici tsakanin magoya bayansu."

Kan batun ko ya halarci rantsar da Tinubu don a bashi mukami, Ganduje ya ce, "Banje don a bani wani mukami ba, amma idan aka bani bazan ki amsa ba.

"Ina wa shugabancin Tinubu kyakkyawan zato. Zamu cigaba da masa addua tare da mara masa baya saboda an zabesa ne duba da tarihin jajircewarsa."

Yadda 'Yan Najeriya S**a Tafka Asarar N1.5 triliyan Cikin Shekaru ShidaKamar yadda bayanan Hukumar Inshora ta Najeriya (...
30/05/2023

Yadda 'Yan Najeriya S**a Tafka Asarar N1.5 triliyan Cikin Shekaru Shida

Kamar yadda bayanan Hukumar Inshora ta Najeriya (NAICOM) ya bayyana, 'yan Najeriya sun tafka asarar sama da N1.5 triliyan a shekaru shida da s**a shude.

Tarihi ya nuna yadda s**a tafka asarar daga 2017 zuwa 2022, sak**akon gabara, hatsari, sata, lalacewar kadara, annoba da cutar da ta jawo kashe kudi, bas**a da mutuwa.

Kididdigar shekaru da aka tafka asarar su ne: A 2017, wanda aka yi asarar N186 biliyan; a 2018, N252 biliyan; da 2019, N225 biliyan.

Yayin makura barkewar annobar Korona a 2020 da 2021, asarar ta ta'azzara zuwa 247 biliyan da N337 biliyan. A 2022, asarar dukiyar ta sauka zuwa N318 biliyan.

Sai dai, k**ar yadda 'yan Najeriya ke cewa, yayin da lamari ya musu k**ari, "Ubangiji baya gajiya da abubuwan al'ajabi" - Ma'ana ni'imar Ubangiji ta yalwaci kowa.

Tabbas, miliyoyin 'yan Najeriya da kamfanonin da s**a tafka wadannan asarorin sun samu damar maida asararsu, madalla abun al'ajabi na Inshora.

Kamar yadda NAICOM ya bayyana, Kamfanonin Inshora sun biya wadanda lamarin ya faru dasu N1.5 triliyan na Inshora, wanda hakan ya zama kariya daga barazanar karayar arziki.

Wadanda s**a fi amfana da tsarin inshora su ne masu tari da Leadway Assurance, daya daga cikin kamfanonin inshora kuma wanda yafi kowanne biyan masu tsarin inshora cikin shekaru shida da s**a shude.

Leadway, a shekaru bakwai da s**a shude ya biya kwastomominshi N271 biliyan, yayin da ya nuna amfanin inshora a matsayin hanya mafi sauki da ke kariya daga karayar arziki. Kamfanin ya biya kwastomominshi
A shekarar 2017; N23 biliyan; a 2018 ya biya N34 biliyan; a 2019 ya biya N38 biliyan; a 2020 ya biya N44 biliyan; a 2021 ya biya N48 biliyan, sannan a 2022 ya biya N57 biliyan.

Daga Hawa Mulki, Abba Gida-Gida ya Fatattaki Ma'aikatan Ganduje Gami da Kwace Wasu KadaroriGwamna Abba Kabir Yusuf na Ji...
30/05/2023

Daga Hawa Mulki, Abba Gida-Gida ya Fatattaki Ma'aikatan Ganduje Gami da Kwace Wasu Kadarori

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ( wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida) ya kori wasu ma'aikatan gwamnati da tsohon Abdullahi Ganduje ya dauka.

A wani umarnin da ya rattaba hannu, sabon gwamnan yayi umarni cewa "Ta sallami dukkan wadanda gwamnati ta ba muk**ai a ma'aikatu, bangarori da hukumomi ko kamfanoni da gaggawa."

Haka zalika, ya sauke dukkan shugabanni ma'aikatu, bangarori da hukumomi, kamfanoni da madaba'oin gaba da sakandiri da gaggawa.

Gwamna ya umarci hukumomin tsaro na jihar su kwace dukkan kadarorin da tsohuwar gwamnati ta siyar.

"A yau nake sanar da cewa, hukumomin tsaro su kwace dukkan gurare da kadarorin da gwamnatin Ganduje ta siyar ba bisa ka'ida ba, karkashin jagorancin 'Yan Sanda, DSS, Jami'an Tsaron Farar Hula da Hisba, har zuwa lokacin da gwamnati zata yanke hukunci," cewarsa.

"A kwanaki kalilan masu zuwa, zamu tsara yadda zamu dawo da jihar bisa tsari gami da dawo da martaba da kimarta, tare da cigaba.

Yayin tabbatar da an tsaftace Kano, ya sanar da yadda daga 1 ga watan Yuni, dukkan ababen hawa zasu rika yawo da abun zaba shara a cikinsu da dukkan 'yan kasuwanni - duk da kantina da shaguna - suma zasu mallaki abun zuba shara tare da zubarwa yadda ya dace.

Gidajen Mai Sun Cika Makil Bayan Tinubu ya Sanar da Cire TallafiGidajen a Legas na fuskantar dogayen layika awanni kadan...
30/05/2023

Gidajen Mai Sun Cika Makil Bayan Tinubu ya Sanar da Cire Tallafi

Gidajen a Legas na fuskantar dogayen layika awanni kadan bayan Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da "cire tallafin man fetur."

Daily Trust ya gano yadda gidajen man NNPC a Ikeja, Alausa s**a cika makil da direbobin da s**a garzaya siyan man fetur.

Sai dai, gidajen man da ba na gwamnati ba, sun dakata da siyar da mai har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.

Haka zalika, a Abuja, layin siyan man fetur ya cika gidajen man babban birnin.

A jawabin rantsarwansa, Tinubu ya ce, tallafin yafi amfanar masu hannu da shuni kan talakawa.

"Mun jinjinawa matakin da gwamnati mai barin gado ta yanke man cire tallafin man fetur, wanda ke cigaba da amfanar masu hannu da shuni fiye da talakawa.

Cigaba da narka tattalin arziki a bangaren ba abu bane mai dorewa. Don haka, zamu yi amfani da kudin wajen narka wa a bangarorin ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da ayyuka da zasu amfanar da miliyoyin rayuka." cewarsa.

Yar ila yau, ya ce zai sake duba batun korafe-korafe kan haraji don bunkasa tattalin arziki tare da jawo hankalin masu zuba hannayen jari.

Shanu da Raguna na Sunfi Min Saukin Jagoranta Fiye da 'Yan Najeriya - BuhariShugaban Kasa Mai Murabus, Muhammadu Buhari ...
29/05/2023

Shanu da Raguna na Sunfi Min Saukin Jagoranta Fiye da 'Yan Najeriya - Buhari

Shugaban Kasa Mai Murabus, Muhammadu Buhari ya ce shanunsa da raguna sun fi masa saukin jagoranta fiye da 'yan Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a taron kafin ranstarwa da ya gudana a Abuja da daren Lahadi, yayin jinjinawa sak**akon zaben da ya samar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.

Buhari ya taya 'yan Najeriya murna bisa yadda s**a fahimci su na da karfin kada kuri'u kuma kuri'unsu sun yi amfani.

Ya ce: "Ina tunanin yadda gobe (Litinin zan shilla zuwa mahaifana gami da komawa kiwon shanu da raguna na, wadanda s**a fi min saukin jagoranta fiye da 'yan Najeriya.

"Masu rike da muk**ai, Shugabannin Jihohi da Kananan Hukumomi, da Wakilansu, Ina matukar godiya gareku tare da muku fatan alheri," Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta yanko inda ya ke cewa.

Ganduje Yayi Mursisi Yaki Zuwa Taron Rantsar da Sabon Gwamna, Bayan Barin Bashin N241.5bGwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ga...
29/05/2023

Ganduje Yayi Mursisi Yaki Zuwa Taron Rantsar da Sabon Gwamna, Bayan Barin Bashin N241.5b

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya mika mulki ga zaɓaɓɓen gwamna, Abba Kabir Yusuf tare da barin bashin N241.5 biliyan.

Sakataren gidan gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji ne ya wakilci gwamnan mai barin madafun iko, wanda ya ki halartar bikin rantsuwa, inda ya mika mulki ga gwamna mai jiran gado da safiyar Litinin a gidan gwamnatin Kano.

Ya bada takaitaccen rahoton abubuwan da aka kashe da ya kunsa ayyukan gwamnatin jihar daga 2015 zuwa 2023, inda ya zayyana yadda aka bar bashin N241.5 biliyan ga jihar.

Kamar yadda Ganduje ya ce " Abubuwan da aka yi amfani dasu daga watan Yunin 2015 zuwa Mayun 2023 ya nuna yadda aka kashe jimillar N660.3 biliyan da jimillar N540.6b a matsayin kudin da ake juyawa, sannan an tara N1.2tiriliyan.

"Saura sun hada da Wutar Lantarkin Kano da Ruwa, wanda ke da N740m, haka zalika Wutar Lantarkin Kano da Ruwa na da N703m, kuma ana saran samun N4b Talata mai zuwa.

"Sannan akwai Hukumar Lafiya na Jihar Kano da ke da N4.3biliyan, kazalika, Kamfanin Noma na Jihar (KASCO) na da N837.7m.

"A halin yanzu, bashin da ake bin Kano na Kungiyar Amintattun Jihar ya kai N75.6b, da kuma N9.2b na jihar, tare da N66.3b na karamar hukuma, wanda hakan ya bada jimillar N75.6b.

Har ila yau, akwai kudin haraji, na Kamfanin Fansho na N4.5b. Daga nan ne jimillar bashin ciki da waje ya k**a N123.3b.

"Saboda haka, jimillar bashin da ake bin jihar daga 31 ga watan Disamba 2022, wanda ya k**a N241.5 b."

Yayin jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan rahoton, sabon gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana alhininsa kan yadda gwamna Ganduje ya ciwo tarin bashi ga mutanen jihar.

"Ina ake so mu nema wa jihar kudi?

" Ɗan kudin da jihar ta bari ba wani na azo a gani bane.

"Ina bada hakuri, amma dole tasa zan bayyana hakan don mutanen kwaran jihar su fahimci inda muka dosa.

"Don me ake fakewa da masu tuntuba, masu tuntuba da yawa don kawai a kwashe arzikin jihar.

"Zamu bi diddigi kan lamarin. Ban yaba ba.

"Sai dai, muna godiya ga tsohon gwamnan kan yadda ya hidimtamawa mutanen kwaran jihar k**ar yadda yake tsammani " cewarsa.

Da Duminsa: An Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban KasaAn rantsar da zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu da ...
29/05/2023

Da Duminsa: An Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Kasa

An rantsar da zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Babban Alkalin Shari'ar Najeriya, Kayode Ariwoola ne ya rantsar dasu ranar Litinin.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta ayyana Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas kuma tsohon Sanata a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a watan Fabrairu 2023.

Ɗan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC ya tashi da kuri'u 8,794,726 tare da dankara abokin hamayyarsa mafi kusa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubukar, wanda ya samu kuri'u 6,984,520 a zaben, yayin da Peter Obi na jam'iyyar LP ya zo na uku da kuri'u 6,101,533 da kuma Rabiu Kwankwaso na NNPP a na hudu da kuri'u 1,496,687.

Yana Gab da Sauka Madafun Iko, El-Rufai ya Rushe Wata Kungiya a Kudancin KadunaAna saura awanni kalilan ya sauka daga mu...
28/05/2023

Yana Gab da Sauka Madafun Iko, El-Rufai ya Rushe Wata Kungiya a Kudancin Kaduna

Ana saura awanni kalilan ya sauka daga mulki, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya bayyana Kungiyar Cigaban Al'ummar Atyap a matsayin haramtacciyar kungiya.

Hakan yazo ne a wata takarda da Muyiwa Adekeye, Mai Bada Shawara ta Musamman ga Gwamnan a Lamurran Sadarwa, da ta fita ranar Lahadi.

Adekeye, wanda ya bayyana yadda gwamnatin jihar, a wani umarnin rushewa, ya ayyana Kungiyar Cigaban Al'ummar Atyap a jefa kanta cikin Al'ummar da ke barazana ga zaman lafiyan jihar, kuma ta jefa kanta cikin munana dabi'un da ke da matukar hatsari ga zaman lafiya, kwanciyar hankali, da lumana ga mulkin jihar Kaduna.

Ya bayyana yadda gwamnan ya rattaba hannu kan umarnin rushe kungiyar, duba da yadda Sashi na 60 a Kundin Jerin Laifukan Jihar Kaduna mai Lamba. 5 na 2017, da kuma Sashi na 5 sakin layi na 2 a Kundin Tsarin Mulkin shekarar 1999 na Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ta bashi dama.

Gwamnan ya bayyana yadda umarnin rushe kungiyar ya fara aiki ranar 24 ga watan Mayu, 2023.

Adekeye ya kara da cewa: "Umarnin rushe kungiyar ya lura da Sashi na 38 da na 40 a Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya da ya bada damar bayyana ra'ayi, damuwa da addini da kuma damar 'yancin kafa kungiya da tabbatar da zaman lafiya ga dukkan 'yan kasa.

"Haka zalika, Sashi na 45 sakin layi na 1, na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ba nuna yadda Gwamna ke da ikon daukan irin wadannan matakan da hukunci idan da bukatar hakan don tabbatar da cigaba da tsaron al'umma, doka, da tarbiyya ko lafiyar al'umma, ko dama da 'yanci ga dukkan 'yan Jihar Kaduna."

A makon da ya gabata, gwamnan ya lashi takobin daukan tsauraran matakai har zuwa awa ta 11 kafin saukarsa daga mulki.

Address

Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Vidia.ng Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share