20/10/2023
Inna Lillahi...
Tsananin bulala har sai da s**a kashe...
Yau Juma'a 20 October, 2023 na samu labarin wani mummunar hukunci da hukumar makarantar Al-Azhar Academy dake bayan Kofar Gayan Zariya s**a yi wa wani dalibinsu mai suna Marwanu Nuhu Sambo, dan JS3 (Basic 9), wanda a yayin wannan hukuncin sai da s**a aika shi har lahira, saboda tsananin hukunci.
Bayan kisan wannan yaro da s**a yi, ba su sanar da iyayensa ba har sai da iyayen yaron s**a rika jin rade-radin cewa an kai yaron asibitin Al-Ridha Clinic, inda s**a garzaya can domin tabbatar da labarin da suke samu game da dan nasu, amma bayan sun samu likitan, sai ya fada masu cewa, shi ba mara lafiya aka kawo masa ba; gawa ce aka kawo masa.
Na tafi da kafafuwana har wannan makaranta domin tabbatar da wannan labarin, a inda na zanta da wasu dalibai 2 da kuma wani yaro mai sayar da abinci a makarantar, tare da wata mata aure duka s**a tabbatar man da faruwar wannan al'amari.
Daga nan, na garzaya zuwa gidan da dalibin da aka kashe yake, na tattauna da wasu iyayensa guda biyu, duka s**a tabbatar man da faruwar abin, har s**a kai ni inda ake yi wa gawar yaron wanka.
Bayan nan, na sake zuwa wurin wasu daliban makarantar, inda na zanta da su, daya daga cikin yaran ajinsu daya da dalibin da aka kashe. Sannan ya labarta man yadda malaman s**a aikata wannan hukunci. Yaron ya ce, mataimakin shugaban makarantar (vice principal) shi ya zo da yaron gaban assembly, inda s**a rika yi masa bulala babu kakkautawa tare da shugaban makarantar (Principal), tun suna iya kirga bulalar har s**a bata lissafi, inda yaron ya tabbatar man da kansa ya kirga bulala akalla 105 wanda aka yi wa yaron a gaban assembly, daga nan kuma s**a wuce da shi office, s**a cire masa riga, s**a bar shi da gajeren wando kawai s**a ci gaba da dukan sa har yaron ya yi yunkurin gudu, amma aka sa zabaniyawa (prefects) na makarantar s**a rike shi s**a koma da shi, s**a ci gaba da dukan sa har sai da s**a cire masa hakora, s**a kashe shi. Inji JAMILU S. BIZARA.