22/08/2022
'YAN BINDIGA SUN HARBE MUTUM 2 A'KANO
'Yan ta adda sun kai hari kauyan gomo dake karamar hukumar sumaila, Inda s**a harbe mutane 2 har lahira, Sudai 'yan ta addan sun kai sumame ne gidan wani babban attajiri A'kauyan, Inda bayan sun shiga gidan nasa basu sameshi ba, Sun tarar gidan ba kowa hakan ne yasa s**a fito domin komawa Inda s**a fito , Kwatsam dake garin akwai maharba sai s**ai karo da wadannan maharba sun tare hanya, Ganin hakanne yasa 'yan ta addan s**a bude musu wuta nan take s**a kashe mutane 2 acikin su har lahira
Wakilin L D HAUSA ya samu damar zan tawa da wani Wanda Abun ya faru A'idon sa, Inda yake tabbatar wa da wakilin namu cewar dama irin wannan hara-haren suna yawan fama dashi a'kauyan tun ba yanzu ba, Domin kuwa garin ya kasance A'kar kashin wani jeji ne Wanda ake Kira da jajin Burra, Kuma jejin yana da mugun girma Wanda ya hade da jihohi 3 duk tsabar girman sa, jihohin sun kasance BAUCHI, JOS, KANO
Shi Wannan dajin Ya kasance wani babban dajine a'yankunan, Wanda A'shekarar 2014 ma 'Yan Boko Haram sun taba shiga jejin Dan samun mafaka agun bayan kuma rahotan sirri ya isowa gwamnati nanne gwamnati ta girka bataliyar jami'an tsaro a dajin,Inda Acikin shekarar 2016 Sojojin s**a samu damar fatattakar jami'an tsaron, Sai dai a yanzu haka Ana zargin wajan ya koma matattarar 'yan ta adda da kuma masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa
.