Garin malam mudi media

Garin malam mudi  media Wannan kafar an samar da ita ne domin isar da sakon harka Islamiyya dama duniya baki daya.

Taron Idil Ghadeer a garin kidandanDa Yammacin wannan Rana Ta Lahadi, 22 ga Watan Yuli, 2025 Yan'uwa Almajiran sayyid ib...
22/06/2025

Taron Idil Ghadeer a garin kidandan

Da Yammacin wannan Rana Ta Lahadi, 22 ga Watan Yuli, 2025 Yan'uwa Almajiran sayyid ibrahim zakzaky (H) Na Da'irar kidandan Sun Gudanar da Taron Idil Ghadeer Labari Cikin Hotuna .

support palastine
are all Palestine
Protect Iran

Malam Mudi Media Forum
02262025

An gudanar da Walimar dawowar dan uwa da ya fito daga gidan yarin Kuje a garin Galadima.🙏🙏Da yammacin  Yau Lahadi ne 8/6...
08/06/2025

An gudanar da Walimar dawowar dan uwa da ya fito daga gidan yarin Kuje a garin Galadima.🙏🙏

Da yammacin Yau Lahadi ne 8/6/2025 yan uwa matasa Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)na garin Galadima da kewaye s**a gudanar da Walimar murnar dawowar dan uwa Yahaya Abdullahi Galadima daya fito daga gidan yarin kuje, waɗanda aka kai tsawon shekaru shida ana tsare dasu bisa zalunci.

Bayan buda taron da addu'a da karatun Alqur'ani an saurari jawabi daka bakin shi ɗan uwan inda yayi takaitaccen jawabi akan yadda s**a tsinci kansu lokacin tsarewar, da kuma darussan da s**a samu acan gidan yarin ,tare da kuma karfafa yan uwa akan gwagwarmaya.

Rahota a takaice.

_sani Sa'adu Ringim
Garin m Mudi media
08/06/2025

Angudanar da Zikiran tunawa da waqi'ar Buhari ta 2015 a Garin Kidandan.( Majalisul Azah)Yau juma'a 30/5/2025 Yan uwa Alm...
30/05/2025

Angudanar da Zikiran tunawa da waqi'ar Buhari ta 2015 a Garin Kidandan.( Majalisul Azah)

Yau juma'a 30/5/2025 Yan uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky Hafizahullah sun gudanar da taron Zikiran tunawa da Waqi'ar Buhari ta 2015. Bayan kammala addu'an bakwai na wakilan yan uwa na Kidandan m Hamza hudu Kidandan.

Taro ya gudana ne da misalin karfe 10:30am na ranar yau juma'a 30/05/2025 inda aka fara bude taron da addu'a , sannan sai aka gabatar da wakokin juyayi a wajan Wanda mawaka s**a gabatar duk a wajan bayan sun kammaala waƙoƙin sai aka gabatar da Mai Jawabi mlm Aliyu Timizy wakilin yan uwa na Kaduna.

Inda m Aliyu Timizy yai magana akan sadaukar wa da kuma riko da jagora,inda yace shifa jagora ana bin shine ido a rufe ba ido budeba ,duk abinda yace ayi babu tambaya kawai kai mabiyi aikatawa zakayi.

Daga karshe akayi addu'a aka sallame yan uwa ga wasu hotuna daga wajen taron.

@ Garin m Mudi media@
30/5/2025
Sani Sa'adu
We support palastine
SHAHIDAMMU GWARAZWMMU

AN GABATAR DA MURNAR AUREN SAYYIDA ZAHARA AS. DA IMAM ALI AS. A GARIN SHADODa yammacin jiya alhamis aka gabatarda murnar...
30/05/2025

AN GABATAR DA MURNAR AUREN SAYYIDA ZAHARA AS. DA IMAM ALI AS. A GARIN SHADO

Da yammacin jiya alhamis aka gabatarda murnar auren sayyida zahara as da imam ali as a garin shado.

an gabatarda taronne a cikin makarantar fudiyya islamiyya shado.

malam mudi press.
09057300664

DA ƊUMI-ƊUMI: Jaruman Kannywood sun ziyarci Jagora  Sayyid Ibrahim Zakzaky H  a gidansa Dake  Abuja.Wasu gungun jaruman ...
29/05/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Jaruman Kannywood sun ziyarci Jagora Sayyid Ibrahim Zakzaky H a gidansa Dake Abuja.

Wasu gungun jaruman finafinai Hausa na Kannywood sun ziyarci Jagoran Mabiya Shi'a Sheikh Ibraheem Zakzaky a ranar Laraba, a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Jaruman sun ce sun kai ziyarar ne domin neman shawarwari don inganta sana'arsu.

Sheikh El-zakzaky ya h**e su da su zama jakadu na gari wajen isar da saƙo, da wayar da kan al'umma, ilimi da fadakarwa, ya ƙara da cewa ba komai ne ya zama aikin assha ba a ayyukan ku sai dai ya na da kyau ku zama mutane masu isar da sako ingantacce ga Al'umma.

Alhamdulillah Sauran Yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky 33 da kotu ke tsare dasu yau Suma sun shaki iskar yanci al...
28/05/2025

Alhamdulillah Sauran Yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky 33 da kotu ke tsare dasu yau Suma sun shaki iskar yanci alhamdulillah Masha allah.

Garin Malam Mudi Media Forum
28052025

Sheikh  Rabi'u Abdullahi Funtua tare da wasu wakilan 'yan'uwa na Yankin Funtuwa sun kai  ziyara Garin Kidandan.Sunje ta'...
28/05/2025

Sheikh Rabi'u Abdullahi Funtua tare da wasu wakilan 'yan'uwa na Yankin Funtuwa sun kai ziyara Garin Kidandan.

Sunje ta'aziyya wakilin 'yan'uwa na Garin Malam Hamza Kidandan wanda ya rasu sakamakon hadarin mota.

Garin Malam Mudi Media Forum
28052025

An gudanar da addu'ar cika kwana uku ta rasuwar  wakilin yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky (H) na garin kidandan ...
26/05/2025

An gudanar da addu'ar cika kwana uku ta rasuwar wakilin yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky (H) na garin kidandan marhum malam hamza hudu kidandan yau litinin 26/5/2025.

Malam Mudi Media Forum
26052025

Inna lillahi wa'inna ilahin raji'un  motar dasu wakilin yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky (H) na garin kidandan m...
25/05/2025

Inna lillahi wa'inna ilahin raji'un

motar dasu wakilin yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky (H) na garin kidandan marhum malam hamza hudu kidandan ke ciki bayan sunyi accident a ranar juma'ar data gabata.

Malam Mudi Media Forum
25/5/2025

Daga wajen Saukar mahaddata karatun Alkur'ani mai girma dake gudana yanzu haka yau Lahadi 25/5/2025 a garin Kano. Garin ...
25/05/2025

Daga wajen Saukar mahaddata karatun Alkur'ani mai girma dake gudana yanzu haka yau Lahadi 25/5/2025 a garin Kano.

Garin malam mudi media
25/5/2025

Anyi jana'izar wakilin yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky (H) na garin kidandan marhum malam hamza hudu.Da safiyar...
24/05/2025

Anyi jana'izar wakilin yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky (H) na garin kidandan marhum malam hamza hudu.

Da safiyar wannan ranar asabar 24/may/2025 aka gabatar da jana'izar wakilin yan'uwa almajiran sayyid ibrahim zakzaky H na garin kidandan marhum malam hamza hudu wanda ya hadu da hatsarin mota jiya juma'a 23/may/2025 tsakanin iyatawa da kidandan marhum malam hamza hudu dan uwa ne jajirtatce ya rasu yabar mata uku da 'ya'ya muna rokon allah madaukakin sarki ya hadashi da ceton manzon allah (s.a.a.w).

Mudi Media Forum
24/may/2025.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN!!! Munyi bannan rashi a hanyar Garin malam Mudi !!!. da yamma cin yau juma'a Allah y...
23/05/2025

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN!!!

Munyi bannan rashi a hanyar Garin malam Mudi !!!.

da yamma cin yau juma'a Allah yayiwa Malam Hamza kidandan rasuwa sakamakon accedent daya samu a hanyar Zaria.

malam Hamza shine wakilin yan uwa na garin kidandan ,kuma babban jarumi akan harka muslinci.
Hakika malam ka cika alkawarinka ka tafi ka barmu. Muna rokon Allah ya bamu guzurin iskeku.

Allah ya gafarta maka yayi maka rahama.

malam mudi press.
09057300664

Address

Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Garin malam mudi media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share