22/10/2025
Gwarzo:
Sallamawa Jagora irin na su Shahid Muhammad Turi, abu ne da tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, kuma zai tabbata a matsayin ramzi na sadaukarwa ga dukkan 'yan gwagwarmaya har ƙarshen duniya.
Mun ji abubuwa da yawa a wajen su Jagora (H) dangane da Shaikh Turi (RH), da irin shauƙinsa ga Shahada, wanda duk sadda Jagora s**a yi bayani akan falalar Shahidi, s**a ce, Shaikh kan yi iyakan kokarin sai ya nemo Hadisin don ya kiyaye shi. Kila a kokarinsa na samun ƙwarin guiwan dakewa a yayin jarabawa.
Shahid ya taba rokon ai masa addu'ar ya samu Shahada a wajen wani bawan Allah, a gaban su Jagora (H), wanda har sai da su Jagora s**a ji ina ma bai roki wannan addu'ar a irin wannan wajen ba.
Lokaci na ƙarshe shi ne Waki'ar Buhari ta 2015, wanda tare da Shaikh sun yi waya da Jagora (H) ya tuntubi me ya k**ata a yi, an ba da Irshadin ko da Muzaharori aka yi a garuruwa ya wadatar. A babin biyayya ga su Jagora (H), Shaikh (RH) ya fita Muzaharar a garin Kano, har an hasko shi a hoto a sahun Muzaharar tare da ba'adin 'yan uwa, karfe 12:00 da wani abu na dare ana kan yi, ya zabi lallai ya k**a hanyar Zaria don ya je ya sauke wazifarsa.
Su Jagora (H) kansu sun yi mamaki a sadda Malam Qasim ya kira su yace musu, ga Malam Turi nan ya zo Gyallesu, kuma ya nufi inda sojoji ke harbi a wajejen karfe 2:30 na dare. Su Jagora s**a ce, ace masa ya dawo.
Ina daga wadanda s**a tare Shaikh, akan lallai ya yi hakuri ya koma, tun kafin zuwan Shahid Qasim don isar da wannan sakon. Amma Shaikh yace, ku kyale ni, zan je ne in gaisa da 'yan uwa da ke can gaba suna ta kokarin a madadinmu, gashi suna ta yin Shahada, za mu je mu nemi albarkarsu. Wani dan uwa (ana kiransa da Tall Man) yana ce masa, Akramakallah yanzu dare ne, da ace da rana ne da za mu bari ka yi hakan, sai ga Shaikh Qasim ya zo, ya ce masa, su Malam sun ce a dawo....
Da Asubah, Jagora (H) ya fito an yi Sallah tare da ba'adin 'yan uwa a cikin gida. Bayan an idar, a yayin da sojoji na kan harbe-harbe a unguwar a kokarinsu na kutsowa gidan Jagora, kafin shigan Jagora cikin gida daga wajen da s**a bayar da sallah, sai da ya ce wa Shaikh; Malam Turi, na ji an ce ka nufi inda sojoji suke harbi dazu, na san kana son Shahada ne, in lokacinta ya zo, za a yi. Amsar da Shahid (RH) ya baiwa Jagora ta sa Jagora ya dauki darduma ya shiga gida ba tare da ya kara cewa komai ba. Yace masa: "Nafsi bi nafsikumul fidha" Wato: “Rayuwata ta zama fansa ga rayuwarku.”
Lahaula wala quwwata illa billah. 😢
Daga sallar nan ne Shaikh ya fito daga gidan Jagora (H) ya kasance mai ƙarfafawa ga 'yan uwan da suke kokarin bayar da kariya, har ma in ya ga wani zai sare, sai ya masa nasiha akan cewa, dan uwa, yau ba ranar kuka ba ne, ranar cikawa Allah alkawari ne. "Ba mun ce da jini da ruhi za mu fanshi ran su Malam (H) ba? To yau ranar wannan ne. In kuma jarabawa ta yi nauyin da ba za a jure ba, har yanzu akwai hanyar fita ta bayan makabartan nan, don kar a raunata wadanda suke kokari" Haka Shaikh ya fada wa wani dan uwa da yaga ya fashe da kuka saboda yadda ya ga ana fasa kwakwalen 'yan uwa da jikkunansu da harsasan soji. Sai kuwa wannan dan uwan ya share hawaye, take ya hakura, ya koma yana farfasa duwatsu. Allah masani, ba mamaki shi ma ya yi Shahada.
Har soji ya zo bakin gidan Jagora ta wajen kofar gida, Shaikh Turi na tsaye kyam a gaban gidan, zuwa lokacin da s**a seta shi s**a harbe shi ya fadi a ƙasa.... Aka dauke shi aka shigar da shi cikin gidan Jagora cikin jini, yana abin zalunta, mai sadaukarwa, Shahidi, ma'abocin cika alkawari ga Allah Ta'ala.
Ba za ka san wane ne Shaikh Turi ba, sai ka tambayi matarsa Malama Maimuna akan karamcinsa ga iyalansa a babin zamantakewa. Ko ka tambayi 'ya'yansa mata shida masu albarka, da Allah Ta'ala Ya azurta shi da su, wanda ya ba su tarbiyar addini, da ilimi, ya tafi ya bar su a cikin albarkar. Ko ka tambayi makwaftansa, ba kawai wadanda s**a hada katanga guda ba, har mutanen garin Kano bakidaya, wane ne Shaikh Turi? Ciki kuwa har da mahukunta, da s**a masa shaidar cewa ba su taba masa tayin abin hannu ko da wane irin salo ya amsa ba. Baka batun gidajen Malaman Kano, ko ma'abota Allah, Shurafa, karamcinsa gare su baya ƙafewa har yau.
Shaikh karimi ne da dukkan ma'anar karamci, ma'abocin haiba da kwarjini ne kwarai, jarumi ne, sadauki, muklisi. Wajen koyi, yana kokarin sanya kafarsa a inda Jagora (H) s**a daga ne. Shi yasa Sisters din Kano s**a zama 'yan gatan Shaikh, saboda koyi da yadda Jagora (H) ke kokarin sauke hakkoki da bayyana 'yancin mata a aikace.
Yana wahala in yi hira da wani mutum, musamman 'yan uwa na Kano akan Shaikh Turi a yanzu, har mu kammala hirar ba tare da mai maganar ya fara hawaye ko ya fashe da kuka ba. Abin mamaki, ina rubutun nan kwalla na fitowa daga idanuna, zuciya na bugawa da sauri fiye da sadda na fara yi.
Allah Ta'ala Ya girmama ladan Shaikh (RH), Ya girmama matsayinsu. Ya tsinewa makasansu albarka. Ya kuma bamu itasu, albarkacin Annabi da Ahlulbaiti (AS).
— Saifullahi M. Kabir
27 ga Rabi'ul Thani 1447 (20/10/2025)