Three Stars Multimedia

Three Stars Multimedia Three Stars Multimedia

15/07/2025
Yan majalisar dokokin Najeriya sun yi karatu na biyu ga ƙudurin dokar da ke neman yin gyaran fuska ga dokar zaɓe ta shek...
17/05/2025

Yan majalisar dokokin Najeriya sun yi karatu na biyu ga ƙudurin dokar da ke neman yin gyaran fuska ga dokar zaɓe ta shekarar 2022 da za ta tilasta yan ƙasar jefa ƙuri’a a lokacin manya da ƙananan zaɓuka masu zuwa.

Wannan sabon ƙudurin doka dai ya janyo rarrabuwar kai a majalisar dokokin kasar nan.

Yayin da wasu ƴan majalisar ke ganin zai zama tamkar take yancin yan ƙasar ne, wasu kuwa na bayyana shi a matsayin mataki mai kyau, wanda idan ya zama doka za a iya cin tara ko kuma yanke wa duk wanda yaki yin zaben hukuncin zaman gidan kaso.

Yan majalisar sun bayyana cewa akwai bukatar cin tarar naira dubu 100 ga duk wanda ya ki jefa kuri’a ko kuma dauri a gidan yari na tsawon watanni shidda ko ma duka biyu.

Ƴan majalisar dai sun kai ga yi wa kudurin karatu na farko da na biyu, da kakakin majalisar wakilan kasar Tajudeen Abbas ya jagoranci zaman.

Wutar NEPA ta lantarke wani saurayi har lahira a Jihar Jigawa a lokacin da yake kokarin satar wayar wuta daga na'urar sa...
17/05/2025

Wutar NEPA ta lantarke wani saurayi har lahira a Jihar Jigawa a lokacin da yake kokarin satar wayar wuta daga na'urar samar da wuta ta karkashin kasa, a sabon ginin Sakatariyar Jihar Jigawa da ke Dutse.

A cewar rundunar yan sandan Jihar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na safe, kuma jami’an ma’aikatar ayyuka ne s**a sanar da hakan.

Isar su wurin da abin ya faru keda wuya, jami'an sun gano gawar saurayin da ba a san ko wanene ba a karkashin wani murfi na siminti dake lullube da wayoyin wutar.

Binciken farko ya nuna cewa wutar lantarki ce ta k**a mutumin a lokacin da yake kokarin lalata wutar lantarki mai karfin gaske.

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa rundunar soji ta dukufa wajen ma...
17/05/2025

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa rundunar soji ta dukufa wajen magance matsalar rashin tsaro dake neman dawowa a yan kwanakin nan.

Ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sayo karin jiragen sama domin karfafa yaki da masu tayar da kayar baya.

Janar Musa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa Jim kadan bayan wata ganawar sirri da s**a yi da shugaba Tinubu da hafsoshin tsaro a fadar A*o Rock.

Ya bayyana cewa, an riga an sayo karin kayan aiki domin karfafa yaki da ‘yan ta’adda, wadanda s**a zafafa kai hare-hare a ‘yan watannin nan, musamman a yankin arewacin kasar.

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya bukaci maniyyatan Jihar da su kasance jakadun kasar na kwarai  a tsawon zam...
17/05/2025

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya bukaci maniyyatan Jihar da su kasance jakadun kasar na kwarai a tsawon zamansu a kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajji.

Gwamna Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin da yake bankwana da rukunin farko na alhazan jihar dari hudu da ashirin da takwas a filin jirgin saman Sultan Abubakar dake jihar Sokoto.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Sokoto ta hanyar kwamitocin da aka kafa za ta rika sanya ido a kan maniyyatan yayin da suke kasa mai tsarki da nufin tabbatar da jin dadinsu da gudanar da aikin hajjin cikin nasara.

Gwamna Aliyu wanda ya sami wakilcin mataimakin sa Idris Mohammed Gobir, ya bukaci maniyyatan da su yi addu’ar Allah ya kara wa Jihar Sokoto da kasa zaman lafiya mai dorewa.

Ni da Tijjani Babangida a shekarun baya
16/05/2025

Ni da Tijjani Babangida a shekarun baya

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta bukaci maniyyatan kasar da su guji daukar kudi sama da Riyal dubu sittin ko kw...
16/05/2025

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta bukaci maniyyatan kasar da su guji daukar kudi sama da Riyal dubu sittin ko kwatankwacin sa na kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.

NAHCON ta bayar da wannan shawarar ce a wata sanarwa da babban jami’in yada labaranta Malam Shafil Mohammed ya fitar a Abuja.

Mallam Mohammed ya gargadi maniyyatan da su guji daukar makudan kudade.

Bayanin ya ce duk wani kudi da ya zarce Riyal na Saudiyya dubu sittin ko mak**ancin sa na karafa, duwatsu, ko zinare, dole ne a bayyana shi ga hukumar kwastam yayin sauka da tashi.

Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya bayyana takaicin sa da cewa, duk da dumbin ma’adanai masu daraja da Jihar k...
16/05/2025

Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya bayyana takaicin sa da cewa, duk da dumbin ma’adanai masu daraja da Jihar ke samu, a halin yanzu ba ta samun kudaden shiga daga gare su.

Sai dai Gwamnan ya bayyana cewa dage haramcin da Gwamnatin Tarayya ta yi na hana hakar ma’adanai masu karfi ya ba shi damar yin cudanya da masu zuba jari da za su taimaka wajen bunkasa fannin da kuma bunkasa kudaden shiga na jihar.

Gwamnan yana da yakinin cewa da zarar an fara zuba jari a kan ma’adinan, to ba shakka Jihar Zamfara za ta daina dogaro da kudin shiga daga Gwamnatin Tarayya.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin yankin Arewacin Najeriya da aka kwashe shekaru ana fama da matsalar rashin tsaro, sai dai gwamna Lawal a lokacin da yake magana a wani shirin gidan talabijin a Abuja, ya ce ya samu nasarar inganta harkokin tsaro a jihar cikin shekaru biyu da s**a gabata.

16/05/2025
A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da jigilar maniyyata aikin hajjin bana na shekarar 2025 zuwa kasa mai...
16/05/2025

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da jigilar maniyyata aikin hajjin bana na shekarar 2025 zuwa kasa mai tsarki, tare da bada tabbacin samun cikakken tallafin kayan aiki da walwala a tsawon wannan tafiya ta ibada.

Taron kaddamarwar wanda ya gudana a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, ya sami jagorancin mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf.

Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da aminci ga dukkan maniyyatan da s**a fito daga Kano.

Ya bukaci maniyyatan Jihar da su kasance masu ladabi da hakuri da mutuntawa a cikin wannan tafiya mai alfarma.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kauran Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara, Alhaji Aminu Sani Jaji ya ce wasu yan bi...
16/05/2025

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kauran Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara, Alhaji Aminu Sani Jaji ya ce wasu yan bindiga da ke addabar mazauna yankin Arewa maso Yamma, cikin tsabar rashin tausayi s**a mikawa karnuka jarirai tagwaye.

A zantawar sa da manema labarai, Alhaji Jaji ya ce an yi garkuwa da mahaifiyar jariran a wani kauyen Zamfara lokacin tana dauke da juna biyu.

Ya bayyana cewa yayin da ta haifi jariran tagwaye, barayin s**a jefa jariran ga karnuka s**a cinye su.

Dan majalisar tarayyar cikin takaici ya kuma bada wani labari mai ratsa jiki na wani yaro mai lalurar farfadiya da aka kashe saboda ya fadi a lokacin da aka k**a shi.

Tawagar hantsi sun ziyarci 3 stars multimedia
14/05/2025

Tawagar hantsi sun ziyarci 3 stars multimedia

Address

Kaduna State

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Three Stars Multimedia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Three Stars Multimedia:

Share