24/12/2025
Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin warware rikice-rikice da dabarun tunkarar zaɓen 2027 a APC
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da wani kwamiti na Dabaru, Warware Rikice-rikice da Wayar da Kai domin magance sabani a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar babban zaɓen 2027.
An ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Laraba a birnin Lagos, inda ya ƙunshi gwamnoni na jam’iyyar, mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya da sauran manyan masu ruwa da tsaki. Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, shi ne Shugaban kwamitin, yayin da tsohon Mai Ba da Shawara kan Shari’a na APC, Muiz Banire, ke matsayin Mamba/Sakatare.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Sanata Adamu Aliero, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, da gwamnoni Hyacinth Alia (Benue), Umar Namadi (Jigawa), Bassey Otu (Cross River), Abiodun Oyebanji (Ekiti) da Sheriff Oborevwori (Delta).
Haka kuma, gwamna Uba Sani (Kaduna) da Siminalayi Fubara (Rivers), Ministan Harkokin Teku da Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, na cikin mambobin kwamitin.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Mai Mala Buni ya gode wa jam’iyya bisa amincewa da shi da sauran mambobi, yana mai cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa da jajircewa. Ya ce za su yi shawarwari da tattaunawa domin samar da dabaru masu faɗi, nagarta da ɗorewa, tare da samar da tsarin da zai bai wa kowa, musamman masu ƙorafi damar jin ana damawa da su.
Buni ya ƙara da cewa kwamitin zai yi la’akari da matakan kariya da hanyoyin magance barazana tun kafin ta taso, yana mai kira ga mambobi da su guji fifita son rai ko ra’ayin kashin kai a kan muradun jam’iyya.
Tun a ranar Juma’a, 19 ga Disamba, a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na APC da aka gudanar a Abuja, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin haɗin kai a jam’iyya. Ya bayyana wa shugabannin jam’iyyar cewa APC ta ginu ne a kan akidar siyasar ci gaba, faɗaɗa shigar kowa da girmama bambancin ra’ayi.
A cewarsa, dole ne dimokuraɗiyyar Najeriya ta dore, kuma hakan zai samu ne kawai ta hanyar juriya, haƙuri da bai wa kowa wuri a cikin tafiyar siyasa.