Soba Online Media

Soba Online Media Soba Online Media is for Broadcasting News, articles and General update not only related to Soba, but the World in general.

ANGUDANAR DA MAULUDIN MANZON ALLAH (S.A.W.W) A GARIN GIMBA.Yan Uwa Musulmai Almajiran sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na gar...
21/09/2025

ANGUDANAR DA MAULUDIN MANZON ALLAH (S.A.W.W) A GARIN GIMBA.

Yan Uwa Musulmai Almajiran sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na garin Gimba, sun gudanar da Muzaharar Mauludin Manzon Allah (s) ayau Lahadi 21/09/2025, Anfara gudanar da Muzaharar ne da misalin 10:30 na safe, inda aka ratsa cikin garin na gimba daga bisani aka dawo Fuddiya inda aka rufe Muzaharar anan.

A kashi na biyu aka buda taro da addu'a da karatun Alkur'ani, aka kira yan Fareti da Ƴan Shotokan karate s**a gudanar da Display, bayan kammalawarsu aka, mika abun magana gamai Jawabi Mal Rabi'u Abdullahi Funtuwa, inda ya gabatar da gwala-gwalan Jawabai akan Mauludin Manzon Allah (S.A.W.W) tareda saita yan uwa akan tsayuwa akan hadafin gwagwarmaya, bayan ya kammala akai addu'a aka sallami yan uwa.

Anyi lafiya Antashi lafiya.

Ibrahim Murtadha Gimba
21/09/2025
28/Rabi'ul Awwal/1447



ZALLAR HOTUNA| Hotuna 20 na wani bangare na Mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) acikin sahun zagayen Mauludin Manzon Allah...
21/09/2025

ZALLAR HOTUNA| Hotuna 20 na wani bangare na Mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) acikin sahun zagayen Mauludin Manzon Allah (SAW), wanda a gabatar Yau a garin Soba, Kaduna.

—Soba Online Media
21/09/2025.




Yadda A Gabatar Da Mauludin Manzon Allah (SWA) a Garin Dinya, Soba – KadunaAl’ummar Musulmi mabiya Jagoran Harkar Musulu...
21/09/2025

Yadda A Gabatar Da Mauludin Manzon Allah (SWA) a Garin Dinya, Soba – Kaduna

Al’ummar Musulmi mabiya Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Yaqub El-Zakzaky (H), na garin Dinya a ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna, sun gudanar da gagarumin taron Mauludi domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SWA).

Taron ya samu halartar daruruwan mabiya tare da jagororin addini da matasa masu kishin Manzon Allah (SWA).

An gudanar da karatun Qur’ani mai girma, wa'azozi da kuma rera kasidun yabo ga Annabi (SWA). Hakazalika, an bayyana muhimmancin rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SWA) a cikin al’umma, musamman kan ƙaunar juna, adalci, da zaman lafiya.

Taron ya gudana cikin tsari da natsuwa, inda fuskar mahalarta ta cika da farin ciki da nuna kauna ga Annabi Muhammad (SWA).

— Soba Online Media
21/09/2025.

Mauludin Manzon Allah (SAW) Ya Kayatar a Garin Dandaura, Kauru- Kaduna.A yau Lahadi, 21 ga Satumba, 2025, al’ummar Musul...
21/09/2025

Mauludin Manzon Allah (SAW) Ya Kayatar a Garin Dandaura, Kauru- Kaduna.

A yau Lahadi, 21 ga Satumba, 2025, al’ummar Musulmi mabiya Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Yaqub Al-Zakzaky (H), na garin Dandaura, karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna, sun gudanar da gagarumin taron Mauludi domin tunawa da fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Taron ya kasance mai jan hankali, inda daruruwan mabiya da masoya Manzon Allah (SAW) daga sassa daban-daban na yankin s**a hallara domin nuna kauna da biyayya ga Annabi (SAW). A yayin taron, an gudanar da jawabai masu cike da hikima, wadanda s**a yi tsokaci kan rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), tare da jaddada muhimmancin yin koyi da halayensa, tausayi da hakuri.

Haka zalika, an gabatar da wakoki da qasidu na yabo ga Manzon Allah (SAW) da s**a sanya taron ya kara armashi. ‘Yan uwa Musulmi maza da mata, dattawa da matasa sun nuna farin ciki da gamsuwa da wannan muhimmin biki na shekara-shekara wanda yake ɗauke da darussa masu zurfi.

An kuma yi addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, kwanciyar hankali, da samun rahamar Allah ga al’umma gaba ɗaya, musamman ma ga al’ummar musulmi da ke fuskantar kalubale a wannan zamani.

Taron Mauludin ya bar tarihi a zuciyar mahalarta, inda aka yi kira da a ci gaba da gudanar da irin wannan taro domin ƙarfafa zumunci, tabbatar da haɗin kai, da kuma yada koyarwar Manzon Allah (SAW).

— Soba Online Media
21/09/2025

LABARI CIKIN HOTUNA.Yadda a gabatar da Maulud na Manzon Allah (SAW) A Garin Soba, Kaduna.Mauludin da ya haɗa al'ummar mu...
21/09/2025

LABARI CIKIN HOTUNA.

Yadda a gabatar da Maulud na Manzon Allah (SAW) A Garin Soba, Kaduna.

Mauludin da ya haɗa al'ummar musulmi na garin Soba dakewa. Mahalartan sun Kungiyoyi, Islamiyyu, ƴan Darika, ƴan Shi'a, ƴan Qadiriyya da sauran su.

—Soba Online Media
21/09/2025.

21/09/2025

KAITSAYE(2)| Kuna iya Kallon Maulud na Manzon Allah(SAW) Na Zagaye wanda ake Gabatarwa Yanzu A Karamar Hukumar Soba, Jihar Kaduna.

Mauludin duk gari wanda ya haɗa ƴan uwa Musulmi daga dukkan bangaror

21/09/2025

KAITSAYE| Kuna iya Kallon Maulud na Manzon Allah(SAW) Na Zagaye wanda ake Gabatarwa Yanzu A Karamar Hukumar Soba, Jihar Kaduna.

Mauludin duk gari wanda ya haɗa ƴan uwa Musulmi daga dukkan bangarori da mazhabobi.

—Soba Online Media

21/09/2025

Ku kasance da shafin Soba Online Media nan da mintuna kadan domin kallon yadda Maulud duk gari zai gudana kaitsaye a Garin Soba.

20/09/2025

KAITSAYE Muzahara Tazo Gurin Rufewa

20/09/2025

KAITSAYE| Kuna iya Kallon Muzaharar Maulud na Manzon Allah(SAW) Wanda ake gabatarwa yanzu haka a garin Dutsen Wai, Kubau ta jahar Kaduna.

—Soba Online Media

An gudanar da Muzaharar Mauludin Manzon Allah (s) a garin Richifa Da Yammacin yau Juma'a wanda tayi daidai 19/09/2025, Y...
19/09/2025

An gudanar da Muzaharar Mauludin Manzon Allah (s) a garin Richifa

Da Yammacin yau Juma'a wanda tayi daidai 19/09/2025, Yan Uwa Musulmai mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na garin Richifa, sun gudanar da Muzaharar Mauludin Manzon Allah (S.A.W.W), sun fara Muzaharar ne da Misalin 4:30 na yamma, inda s**a dauki tsawon awa Ɗaya ana gudanarwa.
Anyi lafiya antashi lafiya.

Ga wasu daga hotunan da muka ɗauko muku.

Rahoto: Ibrahim Murtadha Gimba

Soba Media Forum
19/09/2025
26/Rabi'ul Awwal/1447

An Gudanar da Mauludin Manzon Allah (SAW) Na Yankin Kudancin Zaria A Garin Dutsen Wai.Daga Ahmad Harouna Imam18 ga Satum...
18/09/2025

An Gudanar da Mauludin Manzon Allah (SAW) Na Yankin Kudancin Zaria A Garin Dutsen Wai.

Daga Ahmad Harouna Imam
18 ga Satumba, 2025

A yau Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025, al’ummar Musulmi mabiya Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Yaqub El-Zakzaky (H), na Halqar Azzahra (A.S) daga yankin Kudancin Zaria (Soba dakewa), sun gudanar da Mauludin Manzon Allah (SAW) a garin Dutsen Wai, karamar hukumar Kubau, Jihar Kaduna. Wannan biki na Mauludi ya kasance daya daga cikin manyan al’amuran addini da al’ummar yankin ke gudanarwa a duk shekara domin nuna kauna da farin ciki ga haihuwar Shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Taron Mauludin ya fara ne da bude taro da addu’o’in neman albarka, sannan aka gabatar da karatun Alkur’ani mai girma wanda ya nishadantar da mahalarta tare da tunatar da su kan muhimmancin daukar darasi daga kalmomin Allah Madaukaki.

Bayan haka aka gudanar da Ziyarar Manzon Allah (SAW) da waƙoƙin yabo na Annabi (SAW).

An gabatar da babban bako na musamman, Shaikh Abdulhamid Bello Zaria. Shaikh gabatar da jawabi mai zurfi wanda ya tabo fannoni da dama, ciki har da muhimmancin rayuwa bisa koyarwar Manzon Allah (SAW), darasin hadin kai tsakanin al’ummar Musulmi, da kuma gargaɗin nisantar abubuwan da ka iya kawo rarrabuwar kai a cikin Musulunci.

A cikin jawabin nasa, ya kuma jaddada cewa bukukuwan Mauludi suna da muhimmanci wajen tunatar da Musulmi tarihin Annabi (SAW), halayensa da kuma irin jajircewarsa wajen yada addinin Musulunci.

Haka kuma, an gabatar da fareti na musamman daga ɗalibai ta makarantun Fudiyoyi dake yankin, wanda ya kara wa taron armashi da ɗaukaka.

Wannan Mauludi ya sake tabbatar da yadda mabiya Harkar Musulunci a Kudancin Zaria (Yankin Soba dakewa) ke ci gaba da kasancewa cikin himma wajen gudanar da bukukuwan addini da nuni da kaunar su ga Annabi Muhammad (SAW).

—Soba Online Media

Address

Soba
Kaduna

Telephone

+2347019265726

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Soba Online Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share