
27/08/2025
Professor Isa Ali Pantami, CON (Majidadin Daular Usmaniyya), ya yi wa jami’an tsaro biyu da ke taimaka masa decoration, waɗanda aka ɗaga matsayinsu zuwa sabon muƙami na Inspector.
Taron, wanda aka gudanar a ofishinsa, ya kasance taro ne cike da farin ciki, godiya, da kuma ƙarfafawa, yayin da Farfesa Pantami da kansa ya saka wa jami’an sabbin muƙaman, yana mai jinjina wa shekarun sadaukarwar su da horon da s**a samu, da kuma jajircewarsu wajen gudanar da aiki.
Yayin da yake jawabi ga sabbin jami’an da aka ɗaga matsayin su zuwa Inspectors, Farfesa Pantami ya yaba wa himma da juriya da s**a nuna wajen gudanar da ayyukansu. Ya lura da cewa ɗaga matsayinsu zuwa Sifeto ba wai kawai wata nasara ce ta kashin kansu ba, har ma wata alama ce ta amincewa dasu da kuma sadaukarwa irin nasu, da kuma ƙwarewarsu da suke nunawa a yayin aikinsu.
A saƙon fatan alheri, ya kuma bayyana fatan alheri ga jami’an a cikin ayyukansu na gaba, yana mai yi musu addu’ar samun ci gaba mai ɗorewa a cikin aikinsu, tare da tunatar da su cewa nasarar da s**a samu ya k**ata ta zama abin ƙarfafawa ga wasu su ma su yi aiki tuƙuru da ingantacciyar manufa.
Signed:
Management