29/06/2025
Ba Don Na Hana Maryam Bin Rakiyar Yayarta Ba Da Tare Za Su Yi Hatsari Da Balaraba - Cewar Mahaifin su, Malam Muhammad
Daga Ahmad Nagudu
Mahaifin Maryam Malika da kuma tsohuwar Jarumar Kannywood wato marigayiya Balaraba Muhammad, ya bayyana yadda Allah Ya tsallakar da Maryam daga hatsarin da ya faru da yayar ta wadda ya yi sanadin rasuwar ta a ranar auren ta. Domin a yadda bayanin sa ya nuna a yayin tattaunawar sa da kafar AGG Multimedia Kaduna, ba don ya hana Maryam shiga motar kai amarya Balaraba (yayar ta ba) da watakila yanzu ita ma (Maryam) din, babu ita.
Kamar yadda wakilin Nagudu TV ya ruwaito, a cewar Malam Muhammad din, "Ka ga Maryam din nan, sai da ta shiga motar (kai amarya Balaraba) za ta tashi - ta ce tare za su tafi, da ita za ta je, ni na saukar da Maryam ta na kuka, na ce ba za ta je ba. Allah dai da ya ke Ya sa kwanan ta na gaba, ga ta nan."
Malam Muhammad, ya na furta wadannan kalaman ne jim kadan bayan kammala daurin auren 'yarsa Maryam Malika da Abdul M. Sheriff a cikin gidan sa da ke unguwar Kaji a garin Kaduna.
Daga Ahmad Nagudu - NAGUDU TV