
22/06/2025
BAYAN HARIN DA KASAR AMERIKA TA KAI KAN TASHOSHIN NUKILIYAR IRAN - GA HANYOYI HUDU DA IRAN ZATA IYA MAYAR DA MARTANI.
1. RUFE MASHIGAR RUWAN HORMUZ (Strait of Hormuz)
Strait of Hormuz wata siririyar hanya ce da ake amfani da ita wajen shige da fice a Tekun Pasha (Persian Gulf). Kaso 20% na kasuwanci da hada-hadar man petur na duniya ta wannan mashigar ruwa ake aiwatar da shi. Hakan yasa duk wani abu da zai kawo cikas a wannan mashiga ta Hormuz koda kuwa na yan kawanaki ne zai shafi farashin mai da tattalin arzikin duniya musamman kasar Amurka wadda ta dogara kacokam da man fetur wajen gudanar da alโamuran yau da kullum. Iran tana da adadi masu yawa na kananu da manyan jiragen ruwa, tare da boma-boman karkashin ruwa (naval mines) da zata iya amfani dasu wajen datse hanyar. Ko Iran batayi amfani da jiragen ruwa ba, zata iya sanya dokar hana bi ta wajen tare da amfani da makami mai linzami akan duk wani jirgi da ya karya dokar, kamar dai yadda yan Houthi sukeyi ga jiragen ruwan Israโila a Tekun Maliya (Red Sea).
2. KADDAMAR DA MUNANAN HARE HARE KAN SANSANONIN SOJIN AMURKA DAKE KASASHEN LARABAWA MAKWABTAN TA.
Akwai kimanin sojojin Amurka 50,000 a yankin gabas ta tsakiya, tare da sansanonin su dake cikin kasashe irin su Saudi Arabia, Bahrain, Kuwait, Jordan da sauran su. Iran ta sha nanata cewa duk kasar da ta yarda akayi amfani da kasarta wajen kai mata hari tofa itama ta zama abar farmaka. Kaddamar da hare hare a kan wadannan sansanoni shine abu mafi sauki wajen iran fiye da kai hari Isra'ila. Saidai hakn ba shakka zai shafi alakar ta da makwabtan nata, tunda ba tanan aka kawo mata hari ba.
3. AMFANI DA KUNGIYOYIN GWAGWARMAYA NA SOJOJIN SA KAI (Axis Of Resistance)
Duk da a yan kwanakin nan tasirin kungiyoyin ya lafa, sanadin yakin Isra'ila da Gaza, hakan baya nufin yanzu basuda katabus a yankin. Iran zata iya amfani da wadannan kungiyoyi wajen dagulawa Amurka lissafi, ta inda batayi zato ba. Ita kuma ta ci gaba da yakinta da Isra'ila.
4. FICEWA DAGA YARJEJENIYAR HANA YADUWAR MAKAMIN NUKILIYA (Non Proliferation Treaty), TARE DA KIRKIRAR MAKAMIN NUKILIYAR.
Masana da yawa sun tabbar da cewa hare-haren Isra'ila da Amurka ba zai taba lalata shirin nukiliyar Iran ba, domin yawancin tashoshin an binne su a can karkashin kasa, hana rantsuwa, zai dai iya bata mata lokaci kafin cimma nasarar hada makamin. Rahotanni masu inganci sun tabbatar da cewa Iran ta kwashe duka makamashin da ke cikin cibiyoyin Nukiliyar ta, da dadewa kafin Amurka da Isra'ila su fara kai mata hari. Don haka Iran zata iya kin amfani da karfin soji wajen aiwatar da ramuwar gayya akan amurka, tayi amfani da wannan dama ta fice daga Non proliferation treaty tare da kirkirar makamin kare dangi, kamar yadda North Korea tayi, in ba'a manta ba ashe karar 2003 North Korea ta fice daga wannan YARJEJENIYAR, shekaru uku bayan ficewar ta saita bawa duniya mamaki da gwajin makamin Nukiliya.