01/12/2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Ministan Tsaro Badaru Ya Ajiye Muƙami
Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus ba zato ba tsammani, yana mai danganta hakan da dalilan lafiyar sa.
Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa Badaru ya miƙa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wasikar murabus dinsa mai kwanan watan 1 ga Disamba. Shugaban kasar ya karɓa tare da gode masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa, inda ya bayyana cewa za a mika sunan sabon minista ga Majalisar Dattawa cikin mako.
A gefe guda kuma, tsohon Shugaban Sojoji, Janar Christopher Musa, ya gana da Shugaba Tinubu a fadar Villa da yammacin Litinin. Ba a bayyana cikakken bayanin tattaunawar ba, amma majiyoyi sun ce ganawar na iya zama tana da alaƙa da sabuwar kujerar Ministan Tsaro, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fama da ƙarin kalubalen tsaro.