
11/08/2025
CIN AMANAR DA AKAYI WA FARIDA
Daga Datti Assalafiy
Akwai wani bawan Allah matashi da s**a kulla soyayya da marigayiya Farida Dee Suleiman, dan garinsu ne wato Mubi jihar Adamawa, kusan tare ma s**a taso tun yarinta
Farida ta so shi so na hakika, ita ta dauki nauyinsa har ya kammala jami'ah, sannan tayi kokarin nema masa aiki a Abuja
Da ya tashi saka mata sai labarin aurenta da wata ta gani ana yadawa a Media, ku duba screenshot na sakon da ta tura min ta inbox tana fada min cewa saurayinta zai yi aure, tana ji kamar zata mutu saboda bakin ciki
Ban yi kasa a gwiwa ba na kirata na yi ta kokarin kwantar mata da hankali, Farida ta killace kanta a daki, taki cin abinci, ta gagara fita ko'ina, na kai kusan wata guda kullun sai na kirata kamar sau biyar ina kokarin kwantar mata da hankali
Amma a karshe sai da ta samu babbar matsala a cikin zuciyarta, bakin ciki da damuwa ya haddasa mata ciwon zuciya akan saurayi mayaudari maciyin amana
Kar ku manta, itace ta dauki nauyin karatunsa na jami'ah, idan ta samu kudi ta kan ware masa wani kaso saboda tsananin soyayya, hatta kayan jikinsa ita take saya masa, amma a karshe yaci amanarta ya auri wata
Wannan ya zama darasi, ba'a kwallafa rai a kan mutum, domin mutum yana canzawa kamar yadda hawainiya take canza kalarta
Allah Ka jikan Farida, Ka sa jinyar da tayi ya zama kaffara a gareta