25/03/2025
Jiya a TikTok, ina kallon wani bidiyo na kasuwanci da samun cigaba a rayuwa, sai yake cewa: abu uku zaka yi idan baka samun kuɗi kuma kana so ka rinƙa samu:
1. Ka yi amfani da lokacin ka (time⏳) ka koyi wata sana'a (skill🎯)
2. Sai ka yi amfani da wannan sana'ar ka nema kuɗi (money💵)
3. Sai ka yi amfani da wannan kuɗin ka sama kuɗaɗe (more money💰).
Koyon sana'ar zata iya ɗaukan ka watanni ko shekara, idan ka bada lokacin ka sosai zaka iya wannan sana'ar da kyau, kana yi a hankali har ka ƙware. Yanzu, duniyar tana karkata ne zuwa ga digital era, abubuwa suna komawa online 🌍💻, akwai sana'o'in zamani da dama da zaka iya koya, kamar su:
• Tallata kaya ta internet (digital marketing 📢)
• Shirya bidiyo ko hoto (video/photo editing 🎥)
• Koyon zane-zane (graphic design 🎨)
• Haɗa website (web design & development 🌐)
• Haɗa application (app development/UI/UX design 📱)
• Blockchain & cryptocurrency ₿
• Shigarwa da fitar da bayanai (data analysis 📊)
Da sauran sana'o'in zamani, ɗaya ko biyu sun isa.
Sai ka rinƙa faɗawa mutane (a online da offline) cewa kanada skills kaza, kuma zaka iya yin kaza da kaza, kana faɗan abubuwan da zaka iya yi ko kake yi, kana posting samples ɗin su. Mutane (masu kasuwanci, kamfanoni, makarantu, da sauransu) waɗanda suke neman masu irin wannan sana'ar da ka koya zasu nemeka su baka aiki ka yi musu, su biya ka. In ma basu nemeka ba, kai ka nemesu.
A haka zaka rinƙa amfani da wannan sana'ar, kana samun kuɗin ka a hankali a hankali, har ka kai lokacin da zaka yi amfani da wannan kuɗin ka fara wani abu da zai kawo maka kuɗaɗe (investment), kamar su:
• Gina gidajen haya (real estate 🏠)
• Kiwon dabbobi (animal rearing🐄)
• Noma (farming 🌾)
• Shigo da kaya daga waje ko fitar da su (import/export business 🚢)
• Bada hayan mota, kekenap, babur (Transport business 🚗)
• Kasuwancin stock da cryptocurrency 💹🪙
• Sanya jari a sababbin kamfanoni (startups 🚀)
Da sauran su.
Duk kuɗin da ka samu ko ka kashe, ka rinƙa rubuta su, kana sanin shiga da fitar su. Kuma ka nema masana wannan ɓangaren kaji ta bakin su yadda zaka haɓaka wannan kasuwancin daga wannan matakin da kake zuwa mataki na gaba.
Sannan, tunaninka (mindset 💭) yana da matuƙar muhimmanci wajen samun cigabanka. Dole ne ka kawar da gurɓataccen tunani (negative mindset), kuma hanya mafi sauƙi da zaka bi domin yin hakan ita ce ka yi abota da mutane masu tunani mai kyau—masu son cigaba, ba waɗanda zasu rinƙa maidaka baya ba. Kuma sai ka dage, sai ka jajirce, sai ka yarda cewa zaka iya.
📌 A YouTube channel ɗina (zansa link ɗin a comment), zaku sama wasu daga cikin skills ɗin da na lissafo, na abinda ya shafi computer da kuma wasu na daban masu zuwa nan gaba.
Duniya tana ta cigaba, kada ka tsaya a barka a baya!