
24/08/2024
Yadda Wani Matashi Dan Kabilar Ibò Ya Taimaki Wata Bahaushiya Ta Haifi 'Yan Biyu A Garin Malumfashi
Wannan lamarin ya faru ne da gaske a cikin kasuwar garin Malumfashi dake jihar Katsina.
Wata mata mai juna biyu ta shigo kasuwa da niyyar yin siyayya, sai kwatsam kuma Allah ya kawo mata lalurar haihuwa a cikin kasuwar, inda ta nemi agaji a wurin wani mutum bahaushe ɗan uwanta, amma ya ƙi ya taimaka mata, ya yi banza da ita duk da ganin irin halin neman tamakon gaugawa da take.
Ba ta samu wani taimako daga wajen duk sauran jama'a ba sai shi wannan matashi mai suna CHIJIOKE duk da ya kasance akwai bambamcin ƙabila da addini tsakanin su da wannan mata amman hakan bai hana daya lura cewa matar nan tana bukatar taimako akan haifuwar da zatai ba ya taimaka mata.
Alokacin da Allah Ya sa CHIJIOKE ya lura da alamun cewa cewa wannan mata tana buƙatar taimako haifuwa za ta yi, nan take ya ruɗe ya nufo kanta ya je ya nemi mai baro aka saka ta ya ɗauko ta ya fito da ita bakin kasuwa, sannan kuma ya kara zuwa ya samo mai Keke Napep ya ɗauke ta a ciki s**a hanzarta da ita zuwa asibiti.
Allah Sarki! CHIJIOKE koda s**a je asibitin gwamnati sai s**a tarar a dukka asibitin gaba ɗaya ko ina babu gado, sai ya juya ya nufi asibitin kudi da ita (private), inda suna isa aka ce tana bukatar jini, a nan take ya bada jininsa aka sa mata, yanzu haka maganar da ake matar tana nan ta haihu ta haifi ƴaƴa biyu lafiya.
Wane darasi kuka samu a cikin wannan labari?
Daga It'z Kamalancy