30/04/2025
KATSINAWA MU FITO MU TARBI SHUGABAN KASA _ Gwamnati
DMCV NEWS
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Buƙaci Al'umma Su Fito Yi Ma Shugaba Tinubu Kyakkyawar Tarba Idan Ya Zo Jihar Ranar Juma'a
Gwamnatin Jihar Katsina ta yi kira ga al'ummar jihar da su fito kwansu da kwarkwatansu domin yi wa Mai Girma Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, kyakkyawar tarba a ziyarar aiki da zai kai jihar a ranar Juma'a, 2 ga Mayu, 2025.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Dr. Bala Salisu Zango, ya bayyana wannan kira ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar a ranar Laraba. Ya bayyana cewa ziyarar Shugaban Ƙasa ta kwanaki biyu za ta ba al'ummar jihar damar nuna godiya ga gwamnatin tarayya bisa irin tallafin da take ba wa jihar.
Dr. Zango ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaba da gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda ta aiwatar a cikin shekaru biyu da ta yi tana mulki. Waɗannan ayyuka sun haɗa da babbar hanyar da ta ratsa wajen kauce wa cunkoso (Bypass), wadda ta tashi daga hanyar Dutsin-ma ta haɗe da hanyar Kano, ta zagaya ta ratsa hanyar Daura ta haɗe da hanyar zuwa 'Yandaki da ke kan hanyar zuwa Kaita.
Haka kuma, Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da cibiyar haɗa kayan aikin gona ta zamani (Agric Mechanization Centre), wadda za ta horar da matasan jihar kan yadda ake haɗa kayan aikin gona na zamani.
Kwamishinan ya jaddada cewa waɗannan ayyuka za su inganta rayuwar al'ummar jihar Katsina ta hanyoyi daban-daban, kamar inganta harkokin kasuwanci, samar da ayyukan yi, da kuma haɓaka noma. Ya kuma bayyana cewa ziyarar za ta ba gwamnatin jihar damar tattaunawa da Shugaban Ƙasa kan batutuwan da s**a shafi ci gaban jihar, musamman batun tsaro.
Dr. Zango ya yi kira ga al'ummar jihar da su fito da yawa domin nuna ƙauna da goyon baya ga Shugaban Ƙasa, tare da nuna irin farin cikin da suke da shi na ziyarar da zai kawo jihar.