07/07/2024
AYYAMUL HUSAIN (A.S)
Batun farkon shekara muna iya cewa lokaci ne har wala yau na murnar shiga sabuwar shekara. Ko ba komai da ni’imar Allah yasa an ga farkon shekarar an kuma ga ƙarewarta.
Ainihin ni’ima ce ganin farkon shekara da ƙarewarta lafiya. Sannan kuma ni’ima ce ganin shigar sabuwar shekara. Don haka mukan fara da taya mutane murna, murnar shiga sabuwar shekara. Don duk lokacin da ka wayi gari, wata ni’ima ce Allah Ta'ala ya yi maka da baka dama."
Sheƙar da jinainan tsarkakan bayi na gidan Manzan Allah (S.A.W.W). Wannan kuma sai ya maida wannan lokaci namu na murna sai ya koma baƙin ciki, sai ya zama lokaci ne da aka sheƙar da jinin Manzan Allah (S.A.W.W) a falalin Karbala.
Duk iyalan gidansa gaba ɗaya aka rutsa da su, aka yanyanka su, aka karkashe, aka gutsittsira kawukansu, aka sossoke su a masu, aka tattara matansu a matsayin ainihin ribar yaƙi. Aka kora su korawar bayi, aka bi gari-gari da su, ana bikin tariya, har aka kai su ga ainihin wani ja’iri, wanda ke rayawar yana mulki da sunan addini (addinin Musulunci). To, wannan sai ya zama wata ne na baƙin ciki."
SHEIKH IBRAHEEM ZAKZAKY(H) Muharram 1434H