12/07/2026
🎠Labarin Mai Shago Da Uwar marayu
​Wata rana a wani babban kanti na kayan gwari da ’ya’yan itatuwa, wani mutumi ya shigo domin sayayya. Sai ya tambayi mai shagon:
​"Nawa ne kilon ayaba?"
Mai shagon ya amsa da cewa: "Kilo É—aya 500 ne."
Ya sake tambaya: "Nawa ne kilon tuffa (apple)?"
Mai shagon ya ce: "Kilo É—aya 600 ne."
​Yayin da mutumin yake tsaye yana tunanin tsada da hauhawar farashin kayayyaki, sai wata mata (bazawara) ta ƙaraso da kwandonta a hannu. Ta kalli mai shagon, sannan cikin muryar tsoro da fargaba ta tambaya:
​"Nawa ne kilon ayaba da na tuffa?"
​Mutumin da ke tsaye ya so ya yi saurin amsa mata farashin da aka faɗa masa yanzu-yanzu, amma sai mai shagon ya dakatar da shi da hannu, sannan ya juya ga matar da murmushi cike da fuskarsa, ya ce:
​"Ayaba da tuffa duka kilonsu 100 kacal ne!"
​Matar ta ji daɗi ƙwarai, ta saki ajiyar zuciya sannan ta ce: "Godiya ta tabbata ga Allah da ya yalwata mana!" Ta sayi kilon kowane ɗaya, ta biya sannan ta tafi tana godiya.
​
​ Ganin haka, sai mutumin ya cika da bacin rai, ya kalli mai shagon cikin fushi ya ce:
​"Yallabai, shin wannan ba zamba ba ce? Ni ka ce mini ayaba 500, tuffa 600, amma ita ka siyar mata a kan 100? Me yasa kake siyarwa maza da farashi daban, mata kuma da farashi daban?"
​ Mai shagon ya dafa kafaɗarsa, ya yi murmushi mai cike da sanyaya zuciya, sannan ya ce masa:
​"Ka yi haƙuri ɗan'uwana. Wallahi ban cuce ka ba, kuma ban zalunce ka ba. Wannan matar da ka gani, uwa ce ga marayu huɗu. Tsawon shekaru take gwagwarmayar rayuwa ita kaɗai, kuma ta ƙi jinin wani ya ba ta sadaka ko ya miƙa mata hannun taimako saboda kiyaye mutuncinta."
​ "Na yi tunanin hanyar da zan taimake ta ba tare da na karya mata zuciya ko na zubar da mutuncinta ba. Ban sami wata hanya ba face rage mata farashi duk lokacin da ta zo. Ita a zatonta cewa farashin abubuwan ne s**a yi sauƙi, ni kuma na san na taimake ta ba tare da na kunyata ta ba."
​"Kuma babu wanda ya san wannan sirrin sai Allah na sama. Don haka, kada ka zargi lamarina."
​Jin haka, sai mutumin ya yi shiru, idanunsa s**a cika da ƙwalla. Ya fito da hannunsa ya rike kan mai shagon ya sumbaci goshinsa domin girmamawa, sannan ya ce:
​"A’a, kai ne ya kamata ka yafe mini a bisa zargin da na yi maka."
​📜 Darasi:
​"Kula da raunin zuciyar mutane da biya musu buƙatunsu na rayuwa, wani daɗi ne da armashi wanda babu wanda ya san zanɗonsa, face wanda ya ɗanɗana shi."