29/07/2025
✿─═ ALAMOMIN DA ZAKI GANE JININ AL’ADA YA KUSA ZUWA (HAILA) ═─✿
Jinin al’ada (haila) yana zuwa ne a kowane wata ga mace mai ƙoshin lafiya. Amma kafin ya zo, jiki kan nuna wasu canje-canje da ke nuna cewa lokacin al’ada ya kusa. Ga wasu daga cikin alamomin da yawancin mata ke gani:
1. Ciwon Mara (Lower Abdominal Pain)
Kamar yana jan ciki ko nauyi, musamman a mara. Wannan alamace da jikin ki na shirye-shiryen sakin jini.
2. Jin nauyi a Nono ko Ciwon Nono
Nonon ki zai iya kumbura, ya yi zafi ko ya matse kamar yana cika.
3. Jin Kasala da Gajiya:
Zaki riƙa jin jiki yayi nauyi, kina jin kaman bacci ko rashin kuzari.
4. Jin Zafi a Ƙugu ko Bayan Mara
Wasu mata na jin kamar raɗaɗin baya ko nauyi a ƙugu kafin jini ya zo.
5. Canjin Halayyar Zuciya (Mood Swings)
Zaki riƙa jin saurin fushi, kuka, damuwa ko rashin natsuwa – wannan yana da alaƙa da hormone.
6. Ƙaiƙayi ko Ƙasa Jin Daɗi a Gaba (Vaginal Discomfort)
Zaki iya jin ɗan danshi ko wani ruwa mai laushi wanda ke nuna jiki na tsabtace kansa kafin haila.
7. Jin Yunwa Ko Son Abinci da Ba Kasafai K**e Ci Ba
Wasu mata na jin kwaɗayin abubuwan da ba su fiye ci ba, kamar sweet, nama, lemu, da sauransu.
8. Yawan Fitsari Ko Jin Ciwon Ciki Mai Laushi
Zaki iya riƙa zuwa bayan gida da yawa ko jin kamar ciki na juya.
9. Fitar Ruwa Mai Launin Ruwan Ƙasa (Brownish Discharge)
Kafin haila, wani ruwa mai ɗan ruwan ƙasa yakan fito – wannan alama ce cewa jini na dab da fita.
SHAWARA:
Ki riƙa lissafa kwanakin ki don sanin lokacin haila.
Ki kula da tsafta sosai kafin lokacin da bayan haila.
Idan kin fuskanci matsaloli irin su yawan zubar jini, rashin haila na dogon lokaci, ko zafi fiye da kima – ki tuntuɓi likita.
Wallahu a'alam.
WHATSAPP 07073359324
CALL 07068776855
Domin shiga WhatsApp channel namu ga link
https://whatsapp.com/channel/0029VbAeN1X2P59sFgPoIF3r
Abin sadaqa ayiwa annabi sallallahu Alaihi wasallam salati