28/06/2022
Zamu Kawo Karshen Cin Mutuncin Juna, a Kafofin Sadarwan Zamani(Social Media). Ga Al'ummar kasata..
Daga. Shafin Mallam Yusuf Yahaya Bamalli.
Siyasa Ra'ayi. Siyasa Mutuncinka. Siyasa, akidarka. Siyasa. Mafitanka ce. Siyasa addininka ne.
Amma cin mutunci, a siyasa jahilcine Cin mutunci a Siyasa rashin Ilimi ne, Dama ita Haka ake Gudanar da soyayya ga dan'siyasa. Ka fifita Mutuncinshi akan mutuncinka, Takan Siyasa, ka Kare martaban wani fiye da Martaban kanka Dana iyalinka, ko iyayeka. Wannan kuskure ne.
Siyasa ana yinta ne Domin Samar da yan'ci, tare da Samoma Al'umma saukin rayuwa, bakamar yadda ake gudanar mulkin Soja ba. Amma abin takaici, da ban tausayi, Al'ummarmu sun dauki Wannan Haka ta siyasa fagen cin mutunci, da zubarma da Juna mutunci, sabo da wani, ko banbancin Jam'iyya, ko manufa. Masu aukata Wannan aika-aika Musamman Matasanmu, kusani Kuna bata gobenku ne. Domin kaima Mahaifin wasu ne, Kuma kana da Iyaye, da Malamai da s**a karantar dakai Tarbiyya. Wani irin riba zaka samu akan abin Duniya, kana zubar da mutuncin gidanku, da mutuncinka Domin Kare Mutuncin wani.
Amma Kullun ana samun wasu Mutane marasa daraja da mutunci. Wanda Suke aibata fiyayyen halitta. Annabin muhammad (s.a.w) wani irin mataki ka dauka, Bayan shine akayi Duniya da abin dake ciki damu, Domin shi. ( S.a.w). Amma sabo da asaran lokaci. Kaje kana Bata ranka, Akan aikin wani. Wallahi tallahi. Muji tsoron Allah. A Kowani irin Lokaci, Kowani irin Hali. Bawa zai iya Amsa Kiran mahaliccinsa.
Kafar Sadarwa Zamani, ( social media) Kar ka dauketa hangar da Zara rabaka da mutuncika, da mutuncin iyayenka. Ayi siyasa na ilimi da wajewa. Kowa ya tsaya a Matsayinsa. Mu zauna lafiya da juna.
Allah ya zaunar da mu lafiya.