01/10/2023
Babu Abinda da al'ummar Nigeria s**a amfana a tsawon Shekaru sittin da uku 63" na samun 'Yancin Kai a Nigeria.
Daga Muhammad Auwal Husainiyya
Dukkan abinda zai amfani talakawan Nigeria ya zama masifa da bala'i idan ka shiga kasuwa anan ne zaka gane cewa akwai masifa da Bala'i a kasar Nigeria, shinkafa mai tsakuwa ta Zama Zinare, Gero da dawa sun Zama sai wane da wane, masara kam ba'a Magana, garin rogo da dafaffen rogo sun Zama abin alfahari da ado a matsayin abinci.
Hanyoyin mota sun Zama tarkon mutuwa, saboda rashi kyawunsu, "Check-points" na jami'an tsaron Nigeria sun Zama "Business center" jami'an tsaron Nigeria sun zamanto k**ar dodanni a idon talakawa.
Asibitoci sun Zama Sansanonin Kare kukanka, akan Naira dubu biyu na magani sai uwa ko 'ya'yanta su mutu.
Babu tsaro a Nigeria Gidajen Jama'a da gonaki sun Zama dandalin Kidnappers, gida babu aminci a gona babu aminci, Kai hatta a makaranta Kidnappers suna Kai samame,
Menene abu kwaya daya Wanda yan Nigeria suke Mora?? Amsa shine babu, kai hatta Iskarda muke shaka da ace Gwamnati ce samar dashi to tuni mundade a Lahira. Yak**a Yan Nigeria sudawo hayyacinsu babu mafita a APC KO PDP Mafida dayace dole azo abi Allah a watsarda tsarin kafuruci "Construction" a rungumi littafin Allah ta hanyar Mai Kira zuwa shari'an Allah (T) Shine Mallam Zakzaky (H). domin da'awarsa ce kadai zata samarwa duk wani dan Nigeria 'yanci, domin yana kirane azo ayi adalci akuma yaqi zalumci bawai azo ayi shi'anci ba.
Shiyasa Azzaluman Gwamnatocin Nigeria suke zalumtarsu tsawon Shekaru domin sunsan shine da'awarsa take fada da zalumci.
-Muhammad Auwal Husainiyya
-01/10/2023.