Radio Nigeria Karama FM

Radio Nigeria Karama FM KARAMA FM IS THE FIRST 100% HAUSA FM STATION IN NIGERIA ESTABLISHED IN 2009 IN KADUNA STATE .

28/08/2025

Dawo war Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu daga ziyarar aikin da ya kai Kasashen Brazil da Japan. Jirgin Shugaban Kasa ya sauka ne a filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe daya na daren Laraba.

26/08/2025

Yau ce Ranar Hausa ta Duniya .

Shin wani Karin magana ne da harshen Hausa yafi bada ma ana a wurinka.

Rubuta mana a comment section.

25/08/2025

25/08/2025. 6pm. ADVICE

An shawarci iyaye da su karfafa wa ‘ya’yansu gwiwa wajen cin gajiyar Cibiyoyin horon Sana'o'i da gwamnatin Jihar Kaduna ta samar da zasu fara aiki nan bada jumawa ba.

Babban Sakatare a Ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu na jihar Kaduna Dakta Mahmud Lawal ya bayar da shawarar a lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar cigaban Anguwan Fada dake gundumar Rigachikun yayin ziyarar da s**a Kai masa.

Dakta Mahmud yace Gwamnatin Mallam Uba Sani ta samar da Manyan Cibiyoyin horon Sana'o'in ne a kokarin da take yi na rage zaman kashe wando tsakanin Matasa da basu damar zama abin alfahari a cikin al'umma.

Yace tuni aka kaddamar da daukan Malaman da zasu bada horo a Cibiyoyin Horas da Sana'o'in na zamani da aka samar a yankunan Rigachikun, Soba da Samarun Katab,

Babban Sakatare a Ma'aikatar Kananan Hukumomi da Masarautun ya kuma nemi Iyaye dasu taimaka da shawarwari ga 'ya'yansu dake shirin shiga Manyan makarantu wajen zabar Kwasa-kwasan da s**a dace da zamani domin ganin ba a barsu a baya ba.

COV/IBY

25/08/2025

Masu hannu da shuni su ne masu cin gajiyar Shari'a a Nijeriya

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi gargadin cewa shari’a a Najeriya na ƙara zama “kayan sayarwa,” inda talakawa ke fuskantar rashin adalci, yayin da masu kuɗi ke kauce wa hukunci.

Sultan ya bayyana haka ne a matsayin babban bako a taron shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) da aka gudanar a Enugu a ranar Lahadi, inda ya yi kashedi cewa rashawa da rashin adalci suna lalata sahihancin tsarin shari’a.

“Yau, shari’a tana ƙara zama kayan sayarwa, kuma talakawa ke zama waɗanda ake zalunta a wannan irin shari’a, yayin da masu kuɗi ke aikata laifuka iri-iri suna kuma yawo a kan tituna ba tare da hukunci ba,” in ji shi.

Sai dai ya yaba wa NBA bisa zaben taken taro “Stand Out and Stand Tall”, yana mai cewa ya dace da bukatar gaggawa da ke gaban lauyoyi na cika alkawarin aikinsu na sana’a.

Ya ce dole ne masana shari’a su ci gaba da zama masu jajircewa wajen tabbatar da mulkin doka domin adalci, ɗaukar nauyi da daidaito a gaban doka.

“Kuna ƙuduri ne na tabbatar da mafi girman ƙa’idojin mulkin doka domin tabbatar da cewa kowa, har ma da waɗanda ke riƙe da iko, ya kasance ƙarƙashin doka kuma ya ɗauki nauyi a kanta. Idan muka iya yin haka, za mu shawo kan ainihin matsalar mulki a ƙasar nan,” in ji shi.

Sultan ya jaddada cewa adalci shi ne ginshiƙin kowace al’umma mai kwanciyar hankali, kuma doka dole ta kasance mai nufin cimma adalci a matsayin babban manufarta.

Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da shi wajen tattauna manyan batutuwa da za su tsara makomar Najeriya.

25/08/2025

25-08. Voters registration

Kwamitin Hizba karkashin Majalisar koli dake kula da harkokin shari ar musulunci ta kasa, reshen jihar Kaduna, tayi kira da Al umma da su gagauta zuwa Hukumar Zabe ta kasa wajen sabon rijista ga marasa shi ,don karfafa mulki da tabbatar da kyakkyawan Shugabanci a kasarnan.

Kwamitin Hisban ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, ta hannun kwamqndan kwamitin hisba na majalisar, reshen jihar Kaduna Malam Abdullahi Bayero a Kaduna.

Majalisar ta bukaci matasa da s**a cika shekaru 18 dasu ribaci wannan dama da hukumar Zabe ta bayar don zuwa su mallaki Katin zabe .

kwamitin Hisban ya kuma bukaci kungiyoyi na addini da sauran masu ruwa da tsaki, da su rungumi jagoranci wayar da kan Al umma don zuwa yin rijistan Katin zabe duba da muhimmancin sa wajen tabbatar da shugabanci na gari a kasarnan.

Harwayau majalisar karkashin kwamitin Hizban reshen jihar Kaduna, tace zata cigaba da aiki da duk wasu kungiyoyi ,wajen ganin duk wani da ya dace ya sabunta rajistan zabensa ,ko gyara wani kuskure ya je Hukumar Zaben don sabunta Katin zabensa

Press release .

06/04/2025

Shirin Inda Ba Kasa.... Na wannan mako zai yi magana akan samo hanyoyin bunkasa tattalin arziki da ba sashen man fetur ba ne

06/04/2025

In today's in da ba kasa , we are going to discuss on the potential of non oil export in Nigeria. With guest from Nigerian export promotion council .

Yau a Shirin na Inda ba kasa Zamu tattauna kan damar maki na kasuwancinci abubuwan ba na man fetur a kasuwannin duniya . Tare da shugaban sashin tsare tsare da manufofi Hukumar Kula da cigaban kasuwancinci a kasashen waje Lawal Shehu Dalhat da Shugaban sashin kasuwanci na hukumar Akintunde folorunso.

Address

7 Yakubu Gowon
Kaduna

Telephone

08154923002

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Radio Nigeria Karama FM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Radio Nigeria Karama FM:

Share