15/07/2025
Allah Ya ji kan Buhari: A Bar Gaskiya ta yi Halinta
Muhammadu Buhari ya rasu — tsohon shugaban da ya shigo da sunan wanda zai tsirantar da al’umma, amma ya bar ta cikin bakin ciki, talauci, da rashin gaskiya.
Ya sha neman mulki. Ya dauki alkawura. Ya samu amincewar talakawa. Amma abin da ya bari?
– Matasa ba aiki.
– Ƙananan ‘yan sanda da sojoji suna azabtuwa.
- Cire manyan ‘Yan Sanda daga tsarin CPS na zalunci
– Kudin fansho ya zama arzikin wasu barayi
– Manoma, malamai, ma’aikata — dukkansu sun zama marasa ƙarfi a garuruwansu.
– Gwamnatinsa ta zama mafaka ga barayi da azzalumai.
Ya rasu a asibitin ƙasar waje — abin da yawancin talakawa ba su da damar zuwa ko mafarkin samu idan ba su da lafiya.
Amma Dole Mu Fadi Gaskiya:
A al’adance kuma a addinance, muna addu’a ga matattu. Amma mu ‘Yan Gaskiya ba za mu binne Gaskiya ba. Idan ka yi mulki ka jawo mutuwar wasu, ka jawo wahala, ka karya alkawura — to babu wanda ya isa ya wanke ka a tarihi.
Gaskiyar da muke Gudu:
Yafiya ba gazawa bane. Amma tunanin cewa ba za mu yi kamar ba’a zalunci talaka ba don mutum ya koma ga ubangiji — hakan ne ke sa azzalumai da barayi su ci gaba da cin zarafinmu su na satar arzikinmu.
Mu roƙi gafara a matsayin Musulmi — amma ba za mu karyata tarihi ba.
Buhari bai zama waliyi ba saboda ya rasu. Kuma ba zai tsira daga abunda yayi a tarihi ba.
✊🏽 Dan Bello | ‘Yan Gaskiya