29/10/2025
Labari mai zafi, Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya naɗa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, a matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa kuma Pro-Chancellor na Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua, Katsina.
Wannan Hadi Sirika ɗin nan ne — wanda ya jagoranci hayar jirgin sama da ya fi tsada a duniya: Nigeria Air! Mutumin da ya kashe biliyoyin Naira don ya nuna mana jirgi ɗaya da aka aro daga Habasha, aka liƙa masa tambarin Najeriya Air, aka yi hoto da shi, sannan bayan kwana biyu jirgin ya koma Habasha aka daye tambarin Najeriya, aka mayar da na Ethiopia don ya ci gaba da aikin sa.
Yanzu wannan mutumin ne za a ba mukamin kula da ilimi da tarbiyya!
Wannan ba labari ba ne — wasa ne da hankali.
Farfesa Sirika, Shugaban Sashen “Jirgin da Bai Tashi Ba”
Ko kun tuna da rubutun PhD dinsa:
“Yadda Za Ka Ƙaddamar da Kamfanin Jirgin Sama Ba Tare da Kana da Jirgi Ba.”
Kuma Ya yi nasara sosai — biliyoyi sun bace, amma murmushi bai gushe ba.
Yanzu wannan mutumin ne zai jagoranci jami’a — don koyar da dalibai gaskiya da shugabanci!
Kun fahimci abun dariyar?
Mutumin da ya aro jirgi yanzu yana son ya aro girma da daukaka daga jami’a.
Saboda haka Da Farfesa Sirika a gaba, jami’ar za ga sababbin tsare tsare a zama sabuwar makarantar na kwasa-kwasai na LOOTONOMICS 101.
Darasi na 1: Gabatarwa ga Shirye-shiryen Jirgin Sama Marar Jirgi (AVN101)
Darasi na 2: Yadda Ake Batar da Kudin Jama’a Cikin Salo (PFDT204)
Darasi na 3: Hanyar Kare Kai Bayan An K**a Ka (CCS311)
Darasi na 4: Ci Gaba da Neman Mukamai bayan abun kunya (GOV401)
Dalibai za su yi graduation da takardar shaidar karatu na gogewa a “strategic mismanagement.”
Mutumin da ya ƙaddamar da jirgin da bai taɓa tashi ba, yanzu zai fara kula da ilimi. A Najeriya, gazawa ba ya jawo hukunci sai dai karin mukamai da girma.
Idan ka lalata wani bangare, za a ba ka wani bangare na daban shima ka lalata. Ba rabo ba ne — siyasar sake amfani da shara ce. Daga ma’aikatar da ta ƙone, zuwa jami’ar da ta rushe. Da gaske, Najeriya ta koma “recycling center” na masu sata da rashin kunya. Idan muka duba Fannin Karatun “Rabon Ganima”A nan ne zamu fahimci cewa: Idan ka sace cikin jirgi, sai a ba ka makaranta. Idan ka lalata lafiya, sai a ba ka ma’aikatar gidaje. Idan ka lalata noma, sai a tura ka majalisa. Suna tafiyar da gwamnati kamar ‘yan amshin shata — sai dai kujerun an yi su da kasafin kuɗin talakawa.
Gwamna Radda zai iya naɗa masani, mai hangen nesa, ko kwararren malamin da ya sadaukar da rayuwarsa ga ilimin dalibai. Amma a’a, ya zaɓi wanda ya kashe kuɗin ƙasa don nuna mana hoton jirgin aro. Wannan ba naɗi ba ne — koyarwa ce ta lalacewa.
Yara za su koyi cewa za ka iya “ɓatar” da miliyoyi, ka lalata ma’aikata sannan a dauki wata sabuwar kujerar a ba ka da AC mai sanyi.
Jami’a ba wurin bincike ba ce yanzu — wurin goge laifi ne. Wanda ake zargi da sata, sai a ba shi mukami; wanda ya yi gaskiya, a kore shi.
Kuma za mu ga hotonsa a bangon jami’a an rubuta: “Don Gagarumar Gudunmawarsa a Fannin Ƙirƙirar Jirgin da Bai Taɓa Tashi. A karshe, Najeriya ƙasa ce da ke ɗora mutunci a kan wawa,
da ke bauta wa waɗanda s**a cinna mata suta.
Kuma duk lokacin da aka ce “an naɗa wani tsohon mai laifi,”kar ka tambaya me yasa — ka tambaya me zai lalata a gaba? Saboda idan wannan hauka ta ci gaba, nan da ɗan lokaci,
dalibai ba za su zama marasa aikin yi ba —
za su zama marasa mutunci da digiri a sata!
Kuma mutumin da ya aro jirgi zai zama wanda ke sa hannu a takardar kammalawarsu. Karfin Jama’a, sabuwar duniya.
Daga Dan Bello