
17/07/2025
Ko makiyan Buhari sun san bai yi sata ba - Akpabio
Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya kwatanta marigayi Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na gari wanda ya mulki Najeriya ba tare da satar duƙiyar ƙasa ba.
Akpabio, ya bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar zartaswa da aka gudanar a Abuja don yi wa Marigayi Buhari addu'o'i, ya ce masu s**arsa ma sun san cewa bai yi almubazzaranci da duƙiyar ƙasa ba lokacin da yake mulki.