Alfaidha Tijjaniyya Reporters

Alfaidha Tijjaniyya Reporters Broadcast & Media Production Company

WA'AZIN SABUWAR SHEKARA 1448AHA madadin Young Muslim Congress of Nigeria (YMCN), Reshen Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagoran...
29/06/2026

WA'AZIN SABUWAR SHEKARA 1448AH

A madadin Young Muslim Congress of Nigeria (YMCN), Reshen Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Alkali Abdullahi Maikano, muna farin cikin gayyatar ɗaukacin al'ummar Musulmi zuwa Wa'azin Sabuwar Shekara ta 1448AH.

Wuri: Zawiyar Sheikh Ahmad Makaranta, Titin Premia, Tudun Wada, Gusau.

Rana: Lahadi, 12 Muharram 1448AH (28/06/2026)

Lokaci: 8:30 na dare.

Shirin Taro

Malami Mai Jawabi: Alkali Jabbi Sheikh Balarabe Gwandu.

Mai Ta'aliki: Alkali Umar Balarabe Gusau.

Maudu'i: Muhimmancin Addu'a wajen Samar da Tsaro da Zaman Lafiya.

Mai Masaukin Baƙi: Khalifa Sheikh Mansur Sheikh Ahmad Makaranta.

Baƙi na Musamman

Shugaban Taro: Hon. Sanusi Bala Gusau (Sarkin Dawaki Mai Tuta Gusau).

Babban Baƙo na Musamman: CP Ahmad Muhammad Bello (Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Zamfara).

Uban Taro: Alh. Nura Muhammad Kabir Dan Baba (Baraden Gusau, Uban Ƙasar Tudun Wada).

Allah Ya ba mu ikon halarta. Amin.
Sanarwa: Mal. Mansur Abubakar Gusau.

Assalamu alaikum warahmatullah PRESS RELEASE Tijjaniyya Muslim Students' Association of Nigeria (TIMSAN), ATBU Chapter h...
29/06/2026

Assalamu alaikum warahmatullah

PRESS RELEASE

Tijjaniyya Muslim Students' Association of Nigeria (TIMSAN), ATBU Chapter has embarked on the noble mission of constructing its permanent Masjid, a place that will serve as a centre for Salah Qur'an, Da'wah, Islamic learning, and spiritual development for generations of students to come.

We humbly appeal to alumni, students, parents, well-wishers, and the entire Muslim Ummah to support this blessed project.

No contribution is too small. Every naira you give is a Sadaqah Jāriyah whose reward continues as long as people benefit from this mosque.

🏦 Account Details

Account Name:
Tijjaniyya Muslim Students Association of Nigeria (ATBU)

Bank: FCMB

Account Number: 4866926011

📞 For Enquiries: 0803 898 4434

Kindly donate, share this post widely, and encourage others to be part of this lasting legacy.

The Messenger of Allah ﷺ said:

عَنْ عُثْمَانَ بْنِ عَفَّانَ رضي الله عنه، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ ﷺ قَالَ:

مَنْ بَنَى لِلَّهِ مَسْجِدًا، بَنَى اللَّهُ لَهُ مِثْلَهُ فِي الْجَنَّةِ

Whoever builds a mosque for the sake of Allah, Allah will build for him a house like it in Paradise."

May Allah (SWT) accept our efforts, multiply your rewards, forgive our shortcomings, and grant everyone who contributes a magnificent house in Al-Jannah. Āmīn.

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Haruna Idris, Muhammad Mubarak, Rayyanu Shafiu
17/06/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Haruna Idris, Muhammad Mubarak, Rayyanu Shafiu

Fassarar Deewanin 'Maulanah Sheikhul Islam, Alhaji Ibrahim Nyass Alkaulakhy RTA' Zuwa Harshen HausaBissmillahir Rahamane...
12/06/2026

Fassarar Deewanin 'Maulanah Sheikhul Islam, Alhaji Ibrahim Nyass Alkaulakhy RTA' Zuwa Harshen Hausa

Bissmillahir Rahamaneer Raheem -
Wa Sallallahu Alan Nabiyil Kareem

- Harful Aleep:

Darasi Na Hudu (004)

٢٢ ـ فَـآثَــرْتُ حُبَّ الْمُصْطَفَى دُونَ غَــيْـرِهِ
وَلَــــوْ أُمَّ كَــلْــثُـومٍ وَلَــوْ كَـــانَ مَــرْيَـمَــا

22- Na Za6i Son Abin Za6in Allah Annabi Muhammadu SAW Koma Bayan Wanin Sa,
Koda Kuwa Ummu Kulthumu ce, ko Kuma Maryama

٢٣ـ فَـوَالـلّٰـهِ مَـا فِـي الْـقَلْـبِ حَـظٌّ لِـغَـيْـرِهِ
فَــغَـيْـرُ رَسُــولِ الـلّٰــهِ لَــيْـسَ لِــتَـعْــلَـمَـــا

23- Ina Rantsuwa da Allah Babu Rabon Wanin Annabi SAW a Zuciya tah,
Wanin Manxon Allah SAW Bai ta6a Zamowa a Cikin Zuciyata ba Dan Ku Sani.

٢٤ـ أَشَارَ إِلَى مُـزْنٍ فَـسَـالَ مُـسَـرْمَـدًا
وَإِذْ رَامَ مَـسْـكَ الْـمَـاءِ أَمْـسَـكَ مُـلْـهَـمَا

24- Yayi Nuni (SAW) Zuwa ga Girgije, Sai ya Ya Zubdo da Ruwan Sama a take,
Haka Kuma Yayin da Yaso tsayar da Ruwan yayi Nuni Gare Shi (SAW) Nan take ya tsaya.

٢٥ـ وَإِنَّ قُـرَيْـشًـا عَـيَّـبُـوهُ وَصَـغَّــــرُوا
وَشُـقَّ لَــهُ ذَا الْـجَـوُّ بَــــدْرًا مُـعَـظَّـمَــا

25- Kuma Haqiqa Qurayshawa Sun Aibata Annabi SAW, Sun Wulakanta Shi,
Sai Allah ya tsaga Sama Saboda Shi SAW (tsagewar Wata Gida Biyu) Cikakken Wata Mai Girma da Daukaka

٢٦ـ وَرُدَّتْ لَـهُ شَـمْـسٌ بُـعَـيْــدَ غُـرُوبِـهَــا
وَإِذْ كَـذَّبُــوا قَـدْ أَنْـزَلَ الْـحَــقُّ مُـحْـكَـمَـا

26- Kuma an Dawo Masa da Rana Bayan Faduwar ta (SAW), Kuma a Lokacin da Kafirai S**a Karyata (Mu'ujizojinsa), Sai Allah Ya Saukar da tabbataccen Hukunci (na Alkur'ani domin gasgata shi)

٢٧ـ وَهَـدَّمَ أَحْـزَابًـا بِـرَمْـيَــــةِ كَــفِّـــهِ
فَـيَا عَـجَـبًا مِـنْ رَمْـيِـهِ حِـيـنَ هَـدَّمَــا

27- Kuma ya tarwatsa Runduna ta Dakarun Abokan Gaba da Jifa guda ɗaya Da Yayi da tafin Hannun Sa Mai Albarka
Mamakin Wannan Jifa tashi SAW a Lokacin da ta ruguza Kafirai

٢٨ـ هَـدَى الـلّٰـهُ أَقْـوَامًـا بِــنُــورِ خَــوَارِقٍ
وَبِـالـسَّـيْـفِ يَـهْـدِي اللّٰهُ مَـنْ كَانَ أَجْـرَمَا

28- Allah Ya shiryar da Al-ummomi da Hasken Mu'ujizar Sa (Na Abubuwan al'ajabi) SAW,
Kuma da Kaifin Takobi Yake shiryar da Wanda ya kasance mai taurin Zuciya da Barna

Mu Hadu A Kashi Na Biyar (5)

Allah ya Qara Cika Zukatan mu da Soyayyar Shugaba SAW, Iyalan Gidan Sa tsarkaka, Sahabbansa Masu Daraja Da Shehu Da Shehu RTA

16/05/2026

Mahajjatan Bana Dan Girman Allah Idan kunje Madeena Ku Gaida min Masoyi Na Annabi Muhammadu SAW 💕
Ngd Sosai 🙏

Fassarar Deewanin 'Maulanah Sheikhul Islam, Alhaji Ibrahim Nyass Alkaulakhy RTA' Zuwa Harshen HausaBissmillahir Rahmanee...
18/04/2026

Fassarar Deewanin 'Maulanah Sheikhul Islam, Alhaji Ibrahim Nyass Alkaulakhy RTA' Zuwa Harshen Hausa

Bissmillahir Rahmaneer Raheem - Wa Sallallahu Alan Nabiyil Kareem

- Harful Aleep:

Darasi Na Uku (003)

١٥- وَوَاللّٰهِ لاَ تُلْفِي لِأَحْمَــدَ ثَانِـيًا
فَأَحْمَدُ فَرْدٌ جَوْهَرٌ لَنْ يُقَسَّـمَا

15. Kuma Ina Rantsuwa da Allah Ba Zaka Samu na Biyun Ahmadu (SAW) Ba,
Domin Kuwa Ahmadu (SAW) Shi kadai Ne tsaftataccen Jauhari da Matsayin sa Bai Zamu Abin Rabawa ba.

١٦- عَلَيْــــــهِ صَلاَةُ اللّٰهِ ثُـــمَّ سَلاَمُـــــــهُ
مَعَ الْآلِ وَالصَّحْبِ الْكِرَامِ ذَوِي الـنَّـمَا

16. Salatin Allah da amincin Sa su tabbata ga Annabi SAW
Tare da Iyalan Sa Da Sahabbansa masu Girma, Ma'abota Matsayi.

١٧- فَإِنْ تَسْأَلُونِي عَنْ حَبِيبِي وَسَـيِّدِي
فَطَـهَ حَبِيبُ اللّٰهِ مَـا الْغَـيْرُ مَا وَمَا

17. Idan Kuka tambayeni Dangane da Masoyina (Wane ne) Kuma Shugabana?
Sai Nace Shine Ɗaha (tsarkin Allah), Masoyin Allah, Babu Wani Banda Shi SAW (Ni Ban San Wanin Sa ba).
١٨- فَوَقْتِي وَسَـاعَاتِي صَـرَفْتُ لِــذِكْرِهِ
صَلاَةً وَمَدْحًا مِنْهُ قَدْ صِرْتُ جَيْلَمَا

18. Kunga Lokaci na da Sa'o'ina Duk Na Sarayar dasu Cikin Ambaton Sa SAW,
Yi Masa Salati tare da Rera Wakokin Yabo S**a Sanya na Qara Narke a Cikin Soyayyar Sa.

١٩- فَمَنْ رَامَ دَرْكِي فِي اشْتِيَاقِ نَبِـيِّنَا
فَقَـدْ رَامَ أَمْرًا مُــسْتَحَــالاً مُحَرَّمَــا

19. Duk Wanda yayi Nufin ya Riske ni a Cikin Shauqin Soyayyar da Nake Yiwa Annabin mu SAW,
Haqiqa ya Nufi Wani Al'amari Korarre Abun Haramtawa.

٢٠- كَمَنْ رَامَ مَسْكَ الْبَــــدْرِ يَوْمًـا بِأَصْبُـــعٍ
وَمَنْ رَامَ عَوْدَ الْأَمْـــسِ يَوْمـــاً وَأَيْوَمَــا

20. Kamar wanda yayi Nufin kamo wata da ƴan yatsun sa ne a Wata Rana,
Ko Kaman wanda ya nemi (Jiya da ta Wuce) ta Dawo Yau, ko Kuma ta Dawo Har Abada.

٢١- كَـمَـنْ رَامَ دَرْكَ الْوَصْـفِ أَيْـضًا قَدْ أَكْـثَرُوا
وَلَـكِـنَّـهُـمْ قَـــــدْ غَـــــادَرُوا مُتَـــــرَدَّمَــــا

21. Kamar yanda Mutane da yawa S**a yi Kokarin Siffanta Shi SAW, sai dai Kuma sun bar abin da aka riga aka yi Bayani ne kawai (ba su iya kawo wani sabon abu da zai bayyana dukkan Girmansa ba) SAW.

Mu Hadu a Darasi na Hudu (4)

Allah Ya qara mana Soyayyar Manzon Allah SAW da Iyalan Gidan Sa Da Dukkan Sahabban sa Baki Daya, Ameen 🤲

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Khalifa Abubakar Dandume, Harisu Kabiru, Alhaji Gidado Mu...
11/04/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Khalifa Abubakar Dandume, Harisu Kabiru, Alhaji Gidado Musa, Khalil Abdullahi, Alhaji Poli, Cisse Aliyu, Mukhtar M Adam, Mintasir Adamu Abdullahi

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Khalifa Abubakar Dandume, Harisu Kabiru, Alhaji Gidado Mu...
08/04/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Khalifa Abubakar Dandume, Harisu Kabiru, Alhaji Gidado Musa, Khalil Abdullahi, Alhaji Poli, Cisse Aliyu, Mintasir Adamu Abdullahi

Ahalan Wasahalan

Fassarar Deewanin 'Maulanah Sheikhul Islam, Alhaji Ibrahim Nyass Alkaulakhy Attijjany RTA' Zuwa Harshen HausaBissmillahi...
07/04/2026

Fassarar Deewanin 'Maulanah Sheikhul Islam, Alhaji Ibrahim Nyass Alkaulakhy Attijjany RTA' Zuwa Harshen Hausa

Bissmillahir Rahmaneer Raheem - Wa Sallallahu Alan Nabiyil Kareem

- Harful Aleep:

Darasi Na Biyu (002)

٨- فَـنَشْأَتُهُ كَنْزِيَّةُ الْـحَقِّ وَحْــدَهُ
لِـذَاكَ أَتَانَـا قَــاسِمًا وَمُقَــسَّمَا

8- Sa'annan Faruwar Sa SAW ita ce taskar Gaskiya shi kaɗai
Saboda Haka ne ma Yazo Mana Shine mai Rabo, kuma Shine Mai Raba Dukkan Rabon Duniya da Lahira.

٩- فَـآيُ جَمِيـعِ الرُّسْلِ آيُ مُحَمَّدٍ
فَمِنْـهُ إِلَيْـهِ كُـلَّ شَـأْنٍ مُعَمَّمَــا

9- Sa'annan Ayoyin Dukkan Manzannin Allah (Mu'ujizoji), Ayoyin Annabi Muhammad SAW ne (Mu'ujizojin Sa ne)
Kuma Dukkan Lamura daga Gare Shi Suke Wanzuwa Izuwa Gare Shi Baki ɗaya, SAW.

٠١- مَوَاهِبُ رَبِّ الْعَرْشِ طَهَ مُحَمَّدٌ
وَرَحْمَتُهُ هُوَ الرَّحِـيمُ فَـأَكْرِمَـــا

10- Kyaututtukan Ubangijin Al'arshi, Shine Ɗaha Annabi Muhammadu SAW
Kuma shine Rahamar Sa, Shine Mai Yawan Jinƙai, Dan Haka Ka Kai Matuqa Cikin Girmama Shi SAW.

١١- بَشِيرٌ نَذِيرٌ مُقْسِطٌ وَهْوَ قَاسِـــمٌ
جَوَادٌ كَرِيمٌ بَاسِطُ الْكَفِّ مُنْعِمَــا

11- Manzon Allah SAW mai Bushara ne, Mai Gargaɗi, Mai Kaiwa Matuqa Wajen Adalci, Kuma Shine Mai Raba Dukkan Alkhairan Ubangiji
Mai Yawan Kyauta ne, Mai Girman Karamci, mai shinfiɗa tafin Baiwa ne ga Dukkan Halitta, Mai Ni'imtarwa ne SAW.

١٢- مُقَفًّى أَمِينٌ وَهْـوَ فِي الرُّسْـلِ مُجْتَبًى
حَبِــيـبُ إِلَــــهِ الْعَـرْشِ بَــدْءاً وَمَخْتَمَا

12- Cikamakin Annabawa ne Shi SAW, Amintaccen Ubangiji Kuma Amintaccen Bayin Sa, Kuma Shi Zaɓaɓɓe ne a Cikin Dukkan Manzanni Baki Daya,
Masoyin Ubangijin Al'arshi tun daga Farko Har Zuwa Karshe SAW

١٣- وَأَبْيَضُ يُسْتَسْقَى الْغَمَامُ بِوَجْهِــــهِ
بِهِ نَارَ لَيْلُ الْجَهْلِ إِذْ كَـانَ مُــظْـلِمَــا

13- Kuma Shi (Annabi SAW) Mai Farin Fuska ne Wanda Ake Neman Shayar da Ruwan Sama (A Wajen Allah) da Albarkar Fuskar sa SAW,
Da Shi ne Aka Haska Daren Jahilci a Lokacin da yake Cikin tsananin Duhu (ta Hanyar Bayyanar Hasken Muslumci)

١٤- قُلُوبَ جَمِيـعِ الْخَلْقِ أَحْيَا بِنُورِهِ
وَأَلْسُـنَهُمْ أَحْـيَا فَــزَكَّـى وَعَلَّمَـــا

14- Zukatan Dukkan Halitta an Rayata ne Da Hasken Sa (Saboda Hasken Sa Ya Darsu a Ciki) SAW
Kuma ya raya Halsunansu, ya tsarkake su, kuma ya koyar da su Ilimai, SAW.

Mu Hadu a Darasi na Uku (3)

Allah qara mana Soyayyar Manzon Allah SAW da Iyalan Gidan Sa Da Dukkan Sahabban sa, Ameen 🤲

Fassarar Deewani Zuwa Harshen HausaDarasi Na Daya (001)Bissmillahir Rahmaneer Raheem - Wa Sallallahu Alan Nabiyil Kareem...
06/04/2026

Fassarar Deewani Zuwa Harshen Hausa
Darasi Na Daya (001)

Bissmillahir Rahmaneer Raheem - Wa Sallallahu Alan Nabiyil Kareem

- Harful Aleep:

١- أَبَى الْقَلْـبُ إِلاَّ أَنْ يَكُـونَ مُتَيَّــمًا
حَــلِيـفَ غَـرَامٍ بِالـنَّبِـيِّ مُهَيَّمَــــا

1- Zuciya ta ƙi komai, Sai dai ta zamo Abar Gigitarwa
Ina ma'abocin Dimaucewa Cikin tsananin Bege da Soyayyar Annabi SAW

٢- أَبِيتُ بِلَيْلِ التِّمِّ سَــهْرَانَ مُنْشِـــــدًا
لِـذِكْرِ الَّذِي قَدْ طَـابَ بَدْءًا وَمَخْتَمَـا

2- Ina kwana cikakken dare, ba tare da bacci ba, ina tsara yabo
Don Ambaton wannan da ya daɗaɗa farkon halitta da ƙarshenta (SAW).

٣- أُسَاجِلُ فِيهِ الْوُرْقَ لَيْلِي وَجِيرَتِي
نِيَامٌ وَجَفْنِي كَالْمَذَانِــبِ مَغْرَمَــــا

3- Ina gogayya da kucciya, yayin da Makwabta na
ke barci, Idanu na Sun Zama Kamar Indararo Wajen Zubar da Hawaye Saboda Begen Manzon Allah.

٤- أُنَظِّمُ دُرَّ اللَّفْظِ فِي ذِكْــرِ وَصْفِـــهِ
وَأَحْسِنْ بِوَصْفِ الْبَدْرِ دُرًّا مُـنَـظَّمَـــا

4- Ina tsara lu'a lu'an Lafuzza Cikin Ambaton Siffofin Sa SAW
Kuma ku kyautata wajen siffanta Wannan Watan Mai tsananin Haske, lu'u lu'i abun tsarawa SAW.

٥- مُحَمَّدُ مِفْــتَاحُ الْفُتُــوحَاتِ سَيِّــــدِي
وَخَاتِمُ سِلْكِ الرُّسْلِ خَـتْـمًـا مُقَـدَّمَــــا

5- Annabi Muhammadu SAW Mabuɗin Dukkan Ababen Buɗewa Shugabana,
Kuma shine Cikamakin Zurin Manzanni Cikamaki kuma Abun Gabatarwa, SAW

٦- بِـهِ نَالَ كُلُّ الْأَنْـبِـيَـاءِ مَـنَالَـهُمْ
بِـهِ زِينَةُ الْحَضَرَاتِ وَقِّرْ وَعَظِّمَا

6- Da Albarkar Sa ne dukkan Annabawa S**a Samu Abinda S**a Samu
Kuma da shi ne Aka ƙawata Halarar Ubangiji SWT, ka ga girman Annabi SAW kuma Ka Kai Matuƙa Cikin Girmama Shi SAW.

٧- رَسُولٌ مِنَ الْمَوْلَى وَآدَمُ لَمْ يَكُنْ
وَيَبْقَى رَسُولاً دَائِـمًا وَمُـعَـظَّمَـــا

7- Shi Dai Manxon Allah ne SAW tun Annabi Adamu Bai Wanzu ba (tun Kafin a Halicci Annabi Adamu)
Kuma Zai Cigaba da Wanzuwa a Matsayin Manxo Har Abada Abin Girmamawa SAW.

Mu Hadu a Darasi na Biyu (2)

Allah qara mana Soyayyar Manzon Allah SAW da Iyalan Gidan Sa Da Dukkan Sahabban sa, Ameen 🤲

Address

No. 001 Zawiyya Giwa, Giwa L G
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alfaidha Tijjaniyya Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Alfaidha Tijjaniyya Reporters:

Shortcuts

Share