10/02/2025
ABINDA MUKE NEMAN BAYANINSA AWAJEN WASU
Munsan dai maulanmu sheikh ibrahim Nyssa RTA, shine wanda ya nada sarkin kano Muhammad sunusi 1 amatsayin khalinsa, a nigeria, wanda kowa yasan haka,
Hakanan munsan khalifansa sheikh abdullahi nyass shine wanda ya nada khalifa sheikh ishaq rabiu khadumul qur"an a matsayin khalifa bayan wafatin khakifa sunusi 1,
Munsan khalifa sheikh Muhammad mahi nyass shine wanda ya nada sarkin kano na yanzu khalifa Muhammad sunusi 11 amatsayin khalifa bayan wafatin khakifa sheikh ishaq rabiu,
ABIN LURA
Khalifa sheikh abdullahi Nyasa ya nada nada sheik ishaq rabiu khalifancin ne bisa dorawa akan abinda Mahaifinsa ya assasa, tareda amincewar dukkan yan uwansa, kamar yadda yazo kano musamman yafada kuma har yanzu munada record din majalasinsa akan haka,
Khalifa sheikh Muhammad mahi Nyasa
Ya nada sarkin kano sheik Muhammad sunusi 11 khalifa ne Shima bisa dorawa akan turban da yasamu saboda akwai khalifofi guda biyu wadanda s**ayi zamani da khalifa shekh ishaaq rabiu wato khalifa shekh Ahmad dam,da khakifa sheikh tijjani nyass, kuma dukkansu sunyi rayuwa cikin baiwa khalifa sheikh ishaq rabiu goyon baya,
Don haka khalifa sheikh mahi yayi nuni da cewa ya nada khalifa Muhammad sunusi 11
ne bisa amincewar dukkan yan uwansa kamar yadda yafada da bakinsa,,
ABIN TAMBAYA
Iidan kana ganin akwai kuskure gameda nadin khalifa a nigeria to wanene yayi kuskuren?
Idan kana ganin yanada kyau idan babba yabar
baya, yakamata su daura akan abinda yakeyi ne ko su dakatar?
Munada manyan gidajen shehunnanmu wanda s**a rayu da shehu , wadanda alokacin suna tare sune kowa yasani manya Wanda s**afi kusa dashi, kuma har yanzu manyan khalifofinsu suna nan amma bamu taba jin wani gida yafito yayi jayayya da abinda yayan shehu s**ayi ba meyasa sai bangare guda?
MATSAYARMU
Mu mun tashi wajen shehunnnamu ne da umurnin cikakken biyayya ga yayan shehu,
Kuma suna nuna mana su amatsayin biyayya garesu biyayya ga shehune kai tsaye rainasu kuma raina shehu ne ka