06/08/2026
Allah Ya yi wa Samira Isah Modibbo rasuwa a yau, kuma za a gudanar da jana’izarta da ƙarfe 9 na safe a gidansu da ke bayan Government Secondary School, Makarfi Road, lamba 16 Kangiwa Road, layin Asibitin MSK, Rigasa, Kaduna
Samira Isah Modibbo ta kasance ƙwararriyar mai harkar fasaha da kasuwanci, ƙwararriyar ayyukan ci gaba da kuma jagorar al’umma, wadda ta samu horo a fanni da dama
Ta shafe sama da shekaru da dama tana aiki a fannonin jin ƙai da ƙungiyoyin sa-kai, inda ta ba da gudunmawa wajen ƙarfafa mata, ilimi da fasaha a Najeriya.
A tsawon shekarun da ta yi tana gudanar da ayyukanta, Samira ta jagoranci tare da tallafa wa ƙungiyoyi da dama wajen aiwatar da ayyukan da s**a taimaka wajen sauye-sauyen manufofi, tare da ilmantarwa da ƙarfafa mata, ƙananan yara mata da yaran da ba sa zuwa makaranta sama da dubu 27.
Allah Ya jiƙanta da rahama, Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa iyalanta da ‘yan uwanta haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.