05/08/2025
Mu Duba Kanmu: Lokaci Ya Yi Da Zamu Fara Saukakawa Junanmu
A kwanakin baya na sayi tunkiya da naira 70,000. Yau, cikin ‘yan watanni kacal, kudinta ya kusa naira 130,000. Amma abin takaici, yadda ake yankin tsire a da, haka ake yankin har yanzu – ba a rage ba, ba a kara ba.
Wake kuwa, a bara kwano daya na kai naira 5,000. Yanzu ko naira 3,000 bai kai ba. Amma duk da haka, farashin kosai da sauran kayan abinci bai sauka ba.
Kaya na sauka a kasuwa, amma masu sayar da abinci sun nace akan tsohuwar tsada. Ba a saukakawa juna. Amma da zarar an samu karuwar kudi – ko dai saboda canjin gwamnati ko hauhawar farashi – nan take sai mu kara kudi. Idan kuwa kaya sun sauka, sai mu yi shiru tamkar babu wani sauyi.
Wannan dabi’ar mu ce ke sa rayuwa ta ƙara wahala. A wasu lokuta, ba lallai sai mun zargi shugabanni ba – domin mu kanmu muna zaluntar junanmu.
Lokaci ya yi da zamu duba zuciyarmu. Idan kaya sun tashi, muna da hujja. Idan sun sauka, me zai hana mu saukakawa juna?
Da zamu rika taimakon kanmu, da rayuwa ta fi sauki.