03/02/2025
SHURAFA SUN SHIRYA GAGARUMIN MAULUDI A KADUNA
A yau Lahadi, 03/08/1446, dandalin Shurafa na Harka Islamiyya karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na na kasa su ka shirya gagarumin Mauludin Annabi Muhammad (S) da imam Ali (as) da sayyida fadima (s a), Mauludin ya gudana ne a 'Hall' na NUT, Magadishu da ke garin Kaduna.
Mauludin Wanda ya 'kayatar tare da faranta ran Masoya duka mahalarta taron, ya Sami bakuncin Manyan mutane da kuma malamai daban_daban, inda su ka baje kolin jawabai na falalar ahlul baiti a.s
Sayyid Badamasi Ya'akub, Dan uwa ga Jagoran Harka Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne ya fara gudanar da jawabi a wurin Taron, Shehin Malamin ya tabo bangarori da dama, Cikin jawabin ya tabo bangaren darajar Sayyada Zahra (Sa), ya yi bayani dangane da Bara'a da wilaya, Sannan Kuma ya ja hankalin Mahalarta Taron dangane da Kiran mutane zuwa ga son Ahlul Bait (As), Sannan ya hankaltar da 'yan uwa dangane da jarabawoyin da ke fuskantowa da duk Wanda yace zeso ahlul baiti
Daga bisani sharif sidi Al-Alawi Kano ya gabatar da nashi jawabin, Shima ya tabo janibobi da dama dangane da darajar Ahlul Bait (As), sannan se akaba Shaikh Abdul Hameed Bello Abun magana shima shehin ya gabatar da nashi jawabin, Inda ya fara da tunawa mutane dangane da wasiyyar da Manzon Allah (S) ya barwa Al'umma Kafin barinshi Duniya, wato Kur'ani da Ahlul Bait, ya yi bayani bangaren Bara'a da wilaya, sannan ya ja hankalin Mahalarta dangane da yada soyayyar Ahlul Bait Cikin Al'umma, ya yi magana dangane da sadaukarwa da Kuma hadin Kai.
Bayan kammala jawabin shehin malaminne akabawa Malam Yahya makaho inda yace shima ba a barshi a baya ba, ya zo wurin tare da bayar da gudummawarshi a wurin Taron, Inda ya rera wake ga Annabi Muhammad (S).
Sannan Fasto Yohanna Yd Buru ya yi Dan takaitaccen jawabi tare da sanyawa Taron albarka da fatan Allah ya maimaita mana na shekara Mai zuwa.
Bayan haka, Shareef Isa Ikon Allah, Wanda aka bashi jawabi Mai taken Dangantar Imam Ali (As) da Alkur'ani Mai girma'. , Malamin yayi takaitaccen bayani dangane da Imam Ali (As), Sannan ya sanarwa Mahalarta Taron mafarkin da yayi da Imam Ali (As) Kafin fitowarshi wurin Taron, bayan haka ya farantawa Mahalarta Taron da maganar tabbatar Addin Musulunci a wannan nahiya.
Bayan haka, Shareef Ahmad Rufa'i Shima ya yi jawabi, yayin da ya fara da maganar Manzon Allah (S) Wanda ya ke cewa "Ku ladabtar da 'Ya'yanku akan abubuwa guda uku, Son Annabinku, son Ahlul Bait da karatun Alkur'ani Mai girma"!. Ya ja hankalin Mahalarta sosai gaske dangane da riko da Ahlul Bait.
Malam Salisu Khalifa ya farantawa Mahalartan zukata da kasidu na yabon Ahlul Bait (As), bayan shi Yaran Sayyida Sun yi 'Display tare da wasu bakin da su ka gudanar da wakokin Sayyida (As)
Malama Jamila Auwal (Uwar gidan Malam Mukhtar Sahabi Kaduna) ta yi jawabi dangane da Sayyida Zahra (S A), Inda fado daraja na Wanda aka sawa sunan Sayyida Zahra tare da dabi'un da ya kamata ta lizimta domin kowa da Ita Sayyida Zahra (As).
Daga bisani Wakilin 'yan uwa na garin Kaduna, Malam Aliyu Umar Tirmizi ya Dora da nashi jawabin, Inda ya yi godiya ga Allah ta'ala dangane da kasancewarsu Masu Imani da Wilaya, Sannan ya ja hankalin 'yan uwa dangane da Sallah a Kan lokaci.
Daga karshe an yanka Alkaki tare sannan aka yi addu'a aka sallami kowa.
SHURAFA FORUM MEDIA KADUNA
2/2/2025
3/8/1445