Da'awa Committee Anchau

Da'awa Committee Anchau Mun bude Wannan shafi ne saboda fadakarwa, ilmantarwa da tarbiyya irin ta addinin Islama gamida hadin kan matasa musulmi.

12/04/2022

🍒ADDINI NASIHA NE🍒

Manzon Allah (S.a.w) yace:
"Shi Azumi Da Kuma Al-qur'ani, Su na Ceton Bawa, A Ranar Qiyama".
[Sahi'hul Ja'mi-is Sagir; 3882]

Allah Ya Karbi Ibadun Mu, Yasa Azumin Mu Da Alqur'ani Su Cecemu Ranar Gobe Kiyama.

🤝BARKANMU DA DARE🤝

23/02/2021

ALHADITHUR RABI'U WA THALATHUNA (34)
An Abi Sa'idil Kudriyyi (RA): Kala: Sami'itu Rasulallahi (SAW) yaKulu: "Man ra'aa minkum munkaran falyugayyirhu bi yadihi, fa'in lam yastati'i fa bi lisanihi, fa'in lam yastati'i fa bi Kalbihi, wa dhalika ad'aful imani". Rawahu Muslimu.

HADISI NA TALATIN DA HUDU (34)
An rawaito daga Abi Sa'idil Khuduriyyu (RA) ya ce: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Wanda ya ga abin Ki a cikinku, to lalle ne ya canza shi, da hannunsa, idan kuwa ba zai iya ba, to da harshensa, idan kuma ba zai iya ba, ya Ki abin a zuciyarsa. Yin haka kuma shi ne mafi rauni imani. Muslimu ne ya rawaito shi.

17/12/2020

*A KOWACE RANA DAN ADAM YANA HADUWA DA JARABAWA GUDA UKU(3)*

*Na farko 1*

*Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka.*
*Idan kudinsa ya ragu zai tuhuma bayan kuɗi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.*

*Na biyu 2*

*kullum yana cin arzikin Allah in halal yaci za'a tambaye shi in haram ne za'ayi masa azaba akai bai san karshen hisabin mai zai kasance ba.*

*Na uku 3*

*kullun yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira k**ar yadda ya damu da duniya Bai san makomarsa ba shin Aljanna ce ko wuta.*

*GASKIYA*

*Babu abunda zai amfane ka sai sallar ka/ki da kyawawar aikin ka/ki*

*Duniya kwana uku(3) ce*

*Jiya: Mun ganta ba zata dawo ba*

*Yau: Muna cikinta ba zata dauwama ba zata wuce*

*Gobe: Bamusan ina zamu kasance ba.*

*ka kyautata wa kowa, ka zauna da kowa lafiya, ka yawaita Afuwa da sadaka domin ni da kai dasu duk Matafiya ne*

*Bissalam!!!*

*BARKANMU DA ASUBASHI,

30/11/2020

SALLAR WALLAHA

Sallar Wallah:-
"Tana cikin sallolin nafila mafi falala wadda Manzon Allah ﷺ yayi a aikace kuma ya kwadaitar akanyinta,sunnace mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah ﷺ da yake kiyayeta hatta a lokacin Bulaguro".

*HUKUNCIN SALLAR WALLAHA*
Sallar Wallaha sunnace mai karfi wadda aka kwadaitar akan kowane musulmi ya raya wannan Sallar domin dacewa da abu biyu koyi da Manzon Allah ﷺ da bin Umarnin da kuma dacewa da falala da lada mai yawa.

●بن باز رحمه الله:-
Yana cewa:-
*"Sallar Wallah sunnace ta Manzon Allah s.a.w mai karfi wadda ya aikata ta kuma ya kwadaitar da Sahabbansa akan aikita ta"*.

Allah yana cewa:
*{ وَالضُّحَى}[الضحى:1]*
*Allah yana rantsuwa da Hantsi ko wallaha idan Allah yayi rantsuwa da wani abu to yana nuna girmama wannan abu da matsayinsa awajan Allah".

*DAGA CIKIN FALALAR SALLAR WALLAHA*
Hadisan Manzon Allah ﷺ masu yawa sunzo masu bayyana falalar sallar wallaha, ga kadan daga cikinsu;-

1-Yazo acikin Hadisil Qudsy,Allah mai girma da Buwaya yana cewa:-
*{Dan Adam,kayi min Raka'o'i guda hudu a farkon yini,zai isarmaka wannan yinin zuwa karshensa}*
@أخرجه الترمذي (475).

"Wannan yana bayyana mana dukkan wanda yayi sallar Wallaha raka'a hudu a farkon yini to Allah zai isar masa zuwa karshen yinin da kariyarsa da taimakonsa na musamman".

الطيبي رحمه الله تعالى:
Yana cewa;
*An zan isar maka al'amuranta da shagulgulanka da baka kariya da kiyayeka daga abin ki bayan sallarka ta wallaha har zuwa karshen yini,......"*.
@تحفة الأحوذي :2/478

2-Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Jikin mutum akwai gabobi guda 360,kuma an dora masa yin sadaka akan kowace gaba)* sai Sahabbai s**a ce masa:
"Wa zai iya sauka wannan nauyi ya Manzon Allah ??" sai yace;
*(Goge majinar ko kakin da akayi a masallaci,ko dauke wani abin cutarwa daga akan hanya,idan kuma mutum bai sami damaba,to yayi sallah raka'a guda biyu na Wallaha ya isar masa)*
@الألباني رحمه الله ,صحيح الترغيب

3-Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Babu mai kiyaye Sallar wallaha sai bayin Sallah masu yawan

13/09/2019

T...

07/09/2019

BABU WURIN GUDU DAGA ALLAH SAI ZUWA GARE
SHI
Idan mutane s**a samu kansu cikin wani
mawuyacin hali na takura da matsi, to kada su ta'ba
tunanin akwai wata mafita a wurin wani ba a Allah
ba, ko kuma su d'auka wani abu daban ne zai kawo
musu sauqi
Da dama mutane s**an yaudari kansu da kansu, ta
inda suke yin magani daban cuta daban, ah magani
daban cuta daban mana!
Mutane ne s**a aikata aikin sa'bo qiri-qiri suna sane
wannan abu Allah ya hana, amma s**ayi mirsisi
s**a rufe idanuwansu s**a aikata, sai Allah ya
jarrabe su da wasu wahalhalu da takura gami da
matsin rayuwa, kawai sai suke jingina lamarin ga
wani abu daban, kaga anan mafita kawai shine su
yarda har zuciyarsu cewa sak**akon munanan
ayyukansu ne maqasudin shigar su wancan
mawuyacin halin.
Wallahi inda zamu yarda maqasudin shigar mu halin
matsi dalilin sa'bon mu da miyagun ayyukanmu ne
da mun k**a hanyar samun sauqi, domin wallahi
babu wurin gudu daga Allah sai dai zuwa gare shi,
halin da muke ciki wallahi babu mai fitar da mu sai
Allah.
Mu koma ga Allah zai bamu mafita mu samu sauqin
wahalhalun rayuwa insha Allah, domin d'orawa wani
ko wasu alhakin mawuyacin halin da al'umma ke
ciki kuskure ne, magana ta gaskiya sa'bon mune ya
jawo mana, kuma istigfari gami da kyawawan
ayyuka ne kawai zamu samu sauqin qunci da
matsin rayuwa.
Don haka 'yan'uwa wallahi muji tsoron Allah.
***************************
Allah ya kawo mana mafita daga dukkan halin
matsin rayuwa da muke ciki, ya kawo mana aminci
a rayuwar mu.
Ameen

05/08/2019

Abu Huraira reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
ﺛَﻠَﺎﺛَﺔٌ ﻟَﺎ ﻳُﻜَﻠِّﻤُﻬُﻢْ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺰَﻛِّﻴﻬِﻢْ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﻨْﻈُﺮُ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻢْ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏٌ ﺃَﻟِﻴﻢٌ ﺷَﻴْﺦٌ ﺯَﺍﻥٍ ﻭَﻣَﻠِﻚٌ ﻛَﺬَّﺍﺏٌ ﻭَﻋَﺎﺋِﻞٌ ﻣُﺴْﺘَﻜْﺒِﺮٌ
There are three to whom Allah will not speak on the Day of Resurrection, nor will He purify them, nor will He look at them: an old man who commits adultery, a king who lies, and an arrogant person in poverty.
Source: Sahih Muslim 107, Grade:
Sahih:

May Almighty Allãh guide us to the right path.

Address

Anchau Kubau LGA
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Da'awa Committee Anchau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category