27/10/2024
Tafasa Aurenshi Saboda Yaki Siyan Mata Waya Ta Dubu Dari Hamsin 150K.
Daga: Freelancer Aboro ✍️
Yau 26/10/2024 akayi wani abun ban mamaki a Cikin garin shanga Dake Jihar Kebbi wata yarinya mai suna Sadiya tafasa Auren saurayinta indai bazai Siyan mata waya ta 150K.
Jama'a sun hallara ɗaurin aure kwatsam sai ga labarin amaryar ta fasa auren Saboda yaki ya siyan mata waya babba ta dubu dari da Hamsin-150
Kafin Auren al'ummar karamar hukumar mulki ta Shanga sun shinfida dokar cewa yazama wajibi sai anyi Awo na gwajin jini (Test) ga angon da kuma amarya domin tabbatar da lafiyar ko wannen su.
Amaryar tayi amfani da wannan damar tace ita bazataje awon ba sai angon ya saya mata waya ta naira dubu ɗari da hamsin(150k) sannan zataje wurin awon kuma ita kaɗai ake jira akawo awon a ɗaura auren angon kuma baida halin sayen wayar ga lokacin na kurewa, kawai sai amaryar ta yanke hukuncin idan babu wayar ita ta fasa auren kuma haka ya faru.
Da yake shi Allah a koda yaushe mai adalci ne ga bayin sa, nan take cikin ƙawayen amaryar tace idan shi angon ya amince ta yarda a ɗaura auren da ita, abinda zai baku mamaki shine ita ƙawar amaryar sunan su daya da amaryar watau (SADIYA) Alhamdulillah cikin yardar Allah da ikon sa yan'uwan ƙawar amaryar duk sun yarda sun amince kuma an ɗaura aure.
Daga gefen gidan angon kuma uwar marayun shanga Hajiya. Saudatu Abdullahi Shanga, uwa ga ango ta ɗauke ma uwayen amaryar nauyin kayan ɗaki gaba ɗaya kuma taba amaryar kuɗi Naira dubu hamsin (50k) idan taje gidan mijin ta ta nemi sana'a domin ta taimakama mijinta, Allah ya saka da alkhairi Amin.
Daga ƙarshe muna masu addu'a tareda fatan alkhairi Allah ya sanya ma wannan aure albarka ya kuma basu zuri'a ɗayyaba, Allah ya h**e ma wannan angon abin ciyar da ita.kamar yadda daily news Hausa ta wallafa a shafinta na sada zumunta a yau.