TNL Hausa

TNL Hausa An samar da wannan kafar ce domin bayar da labarai kamar yadda suke ba tare da nuna wani bambanci ko son rai ba. Haka ma muna fassara wato Translation.
(1)

HARIN ’YAN BINDIGA: Gwamna Lawal Ya Ziyarci Bungudu, Ya Sake Jaddada Matsayar Gwamnatinsa Kan Yaƙi Da Ta'addanciGwamnan ...
07/08/2026

HARIN ’YAN BINDIGA: Gwamna Lawal Ya Ziyarci Bungudu, Ya Sake Jaddada Matsayar Gwamnatinsa Kan Yaƙi Da Ta'addanci

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga tattaunawa ko yin sulhu da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba, yana mai jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan da s**a dace domin murƙushe matsalar rashin tsaro a jihar.

A ranar Alhamis, gwamnan ya kai ziyarar jaje Ƙaramar Hukumar Bungudu, domin ta'aziyya ga iyalan waɗanda harin 'yan bindiga ya shafa, da Masarautar Bungudu, da kuma al'ummar yankin baki ɗaya.

Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, ziyarar ta fara ne a fadar Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, inda Gwamna Lawal ya bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara.

Ya ce, ya je Bungudu ne domin jajanta wa iyalan waɗanda s**a rasa 'yan uwansu, da Sarkin Bungudu, da kuma ɗaukacin al'ummar yankin sakamakon harin 'yan bindigar da ya afku a makon da ya gabata.

Gwamnan ya bayyana cewa abin da ya faru wata jarrabawa ce daga Allah Maɗaukakin Sarki, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa za a yi nasarar shawo kan matsalar.

Ya ce, gwamnatin jihar na ci gaba da karkata dukkan ƙarfinta da albarkatunta wajen kawo ƙarshen ta'addanci da ayyukan 'yan bindiga.

Gwamna Lawal ya kuma buƙaci al'umma da su ci gaba da nuna haƙuri, yana mai cewa yaƙi da rashin tsaro na buƙatar jajircewa tare da yawaita addu'a.

Ya yi addu'ar Allah Ya bai wa iyalan mamatan juriyar wannan babban rashi, tare da roƙon Allah Ya gafarta wa waɗanda s**a rasa rayukansu.

Har ila yau, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da waɗanda s**a jikkata, tare da yin duk mai yiwuwa domin ganin an kuɓutar da duk mutanen da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.

Da yake mayar da martani, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, ya gode wa Allah bisa bai wa Jihar Zamfara gwamna da ke nuna damuwa da halin da jama'a ke ciki tare da ɗaukar matakan da s**a dace domin kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Sarkin ya ce kasancewarsa mamba a Kwamitin Tsaro na Jihar Zamfara, yana sane da irin ƙoƙarin da gwamnan ke yi wajen yaƙi da 'yan bindiga, yana mai bayyana tabbacin cewa za a yi nasarar shawo kan matsalar.

Ya kuma gode wa gwamnan bisa ziyarar jajen, yana mai cewa hakan ya ƙara wa al'ummar Bungudu ƙarfin gwiwa.

Yayin ziyarar tasa, Gwamna Lawal ya kai ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Bello Umar Bungudu, da sauran iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu a harin.

RASUWAR SAMIRA ISA MODIBBO DA ABIN DA TA KOYA MANARasuwar matashiya Samira Isah Modibbo babban rashi ne. Duk da ta shafe...
06/08/2026

RASUWAR SAMIRA ISA MODIBBO DA ABIN DA TA KOYA MANA

Rasuwar matashiya Samira Isah Modibbo babban rashi ne. Duk da ta shafe rayuwarta tana fama da amosanin jini ( ), ba ta taba bari cutar ta hana ta cimma burinta ba. Ta rayu tana hidimtawa al’umma, tana taimakon mata, yara da marasa galihu har zuwa karshen rayuwarta.

Samira ta yi fice a fannin ci gaban al’umma, ilimi da fasaha. Ta taimaka wajen ilmantar da dubban mata da ’yan mata, tare da jagorantar ayyukan da s**a canza rayuwar mutane da dama a Arewacin Najeriya.

Rayuwarta ta nuna mana cewa karfin hali da kyakkyawar manufa kan iya danne nauyin kalubale. Ko da tana cikin jinya, ta ci gaba da rayuwa mai amfanar da mutane. Hakika wannan matashiya ta bar tarihi mai kyau da ba za a manta da shi ba.

KIRA: Rasuwarta ta sake tunatar da mu muhimmancin gwajin genotype kafin aure. A matsayinmu na masu fadakarwa da wayar da kan al’umma, ina kira da iyaye da matasa su tabbatar sun san matsayin kwayoyin halittarsu kafin aure, domin rage yawan yaran da za a haifa da amosanin jini a nan gaba.

Allah Ya yiwa Samira rahama, Ya sa Aljanna ce makomarta. Ameen.

Wadanda ke fama da kowacce irin cuta kuma, Allah ya ba su sauki. Ameen.

06/08/2026

Sakataren Kungiyar Mahauta ta Jihar Kano Alhaji Usman Aliyu yana dhawartar matasan kasan nan su guji amfani da miyagun kwayoyi tare da godiya ga Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf

Sunana Comrade Jawad Abdussalam. Ni Dan kishin arewa ne kuma mai son ganin matasa sun Dogara da kansu. Munyi Alkawarin K...
05/08/2026

Sunana Comrade Jawad Abdussalam.

Ni Dan kishin arewa ne kuma mai son ganin matasa sun Dogara da kansu.

Munyi Alkawarin Koda hakan zai zamo karshen numfashin mu Amma sai mun kawo peace, unity and joyful a cikin matasan mu na Arewacin Nigeria Insha Allahu.

Ana nuna halin ko in kula da Rayuwar matasa a Nigeria musamman a Arewa, Idan baka da connection duk experience da exposure da kake dashi ya tashi a banza. Muna nan akan wannan matsalar Insha Allahu sai mun kawo karshen ta a Nigeria.

Mu yan Arewa ne, Kuma tarihin Nigeria almost 70% daga Arewa ya samo asali, Amma sakacin mu da nuna halin ko in kula ya jawo mana koma baya a Arewa,

Saboda haka Ina Kira ga matasan Arewa da su farka daga dogon baccin da suke yi su dukufa wajen neman yancin su na yan kasanciiii.

NI DAN AREWA NE MAI KISHIN AREWA.

COMR JAWAD ABDUSSALAM ✍️

05/08/2026

Gwamnati zata kashe naira miliyan dubu 178 da doriya wajen sake gina hanyar Kaduna zuwa birnin Gwari mai tsawon kilomita 122 inji Gwamna Senator Uba Sani

04/08/2026

Alhaji Nasidi Kano wanda ya wakilci AA Rano wajen kaddamar da kittafan Fulani Rukayya Salihi Bayero wacce ta rubuta littafai uku rigis da s**a da Gimbiya Ta Gari Madubin Ilimi da kuma The Agoney of a Mother sai kuma The Minaret Fundation of Moral Codes and Social Life kuma aka kaddamar da su asabar din 1 ga watan August a North West University.

04/08/2026

Mace mai kamar maza, Fulani Rukayya Salihi Bayero wacce ta rubuta littafai uku rigis da s**a da Gimbiya Ta Gari Madubin Ilimi da kuma The Agoney of a Mother sai kuma The Minaret Fundation of Moral Codes and Social Life kuma aka kaddamar da su asabar din 1 ga watan August a North West University.

31/07/2026
31/07/2026

Shin wace gudummuwa Fulani da makiyya suke bayarwa a Arewacin Nijeriya dama duniya baki daya, za a tattauna wannan batun a Taron da Majalisar Dunkin duniya ta shirya a Mangiliaya domin duba wannan batu in ji Abdulhamid Tahir Hamid a Kano.

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TNL Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to TNL Hausa:

Shortcuts

Share