
26/09/2025
Ƙasar Saudiyya ta haramta ƙara kuɗaɗen haya har na tsawon shekaru Biyar
Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Muhammad bn Salman ne ya bayar da umarnin dakatar da ƙarin kuɗin haya na tsawon shekaru 5 a birnin Riyadh da ke ƙasar.
Wannan doka wadda za ta fara aiki daga ranar 25 ga Satumbar 2025, za ta shafi gidajen zama da kuma wurare sana’a da dai sauransu.
Dokar ta ce ko kaɗan masu gidajen ba za su iya ƙara kuɗin haya ba har zuwa tsawon shekarun nan biyar cur da a ka ambata.
Har wa yau, kowane mai haya zai ci gaba da biyan kuɗin da yake biya kai tsaye ba tare da ƙari ba tsawon shekarun kuma mai gida ba shi da ikon karɓe gidansa daga hannun ɗan haya a tsakanin shekarun sai dai idan ta k**a mai gidan ne zai koma gidansa da zama ko kuma ɗan haya ya fita a karan kansa ko kuma idan gidan ne ya samu wata matsala ta daban.