12/09/2022
(TALLA)
Allah Ya kawo mu sabon mako, a yau ma na zo muku da wanda ni Petra Akinti Onyebule na ƙirƙireshi domin sanar daku al'amuran da s**a shafi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC tare da abokin takararsa, a kowanne mako, a duk ranar Lahadi.
Kamar yadda kuka sani, maƙasudin shi ne kawar da duk wasu gutsuri tsoma da ƙarairayi game shige da ficen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da tabbatar da bamu baiwa duk wasu masu nufinsa da sharri daman kitsawa da yaɗa ƙarairayi akansa ba.
A ranar Lahadi, 4 ga watan Satumbar 2022, ɗan takarar jam'iyyar APC a matakin shugabancin ƙasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya tarbi manyan baƙi a gidansa dake Asokoro, Abuja, da s**a haɗa da tsofaffin gwamnonin jihohin Yobe da Abia, watau Sanata Ibrahim Gaidam da Sanata Orji Uzor Kalu.
Sai kuma ranar Litinin, 5 ga watan Satumbar 2022, inda jakadiyar haɗaɗɗiyar daular Birtaniya a Najeriya, Catorina Lian tare da ƴan rakiyarta s**a ziyarce shi a ofishin yaƙin neman zaɓensa dake Abuja. Catorina ta kai masa wannan ziyara ne domin tattauna manufofin ƙasar Birtaniya ga Najeriya bayan zaɓen 2023.
A ranar Talata, 6 ga watan Satumbar 2022 kuwa, Tinubun ne tare da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima da shugaban yaƙin neman zaɓensa, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar ne s**a gana da shuwbagabannin jam'iyyar APC a sakatariyar jam'iyyar dake Abuja. A yayin ganawar, cikin ƙuzari da ƙwarewa wajen salon magana da nuna sanin makaman aiki, Tinubu ya bayyana manufofinsa tare nanata yaƙininsa na APC za ta lashe zaɓukan 2023.
Har wa yau, a ranar Talatan, ɗan takarar shugabancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu rakiyar abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima, shugaban yaƙin neman zaɓensa, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, shugabar mata ta jam'iyyar, Dakta Betta Edu, Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa, mataimakinsa, Umar Namadi Danmodi, mataimakin shugaban APC na ƙasa shiyyar kudu, Emma Nnekwu da tsohon shugaban EFCC, Malam Nuhu Ribaɗu sun kai ziyarar jajantawa jihar Jigawa bisa ambaliyan ruwa da aka samu wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 51 tare da lalata kadarori da dama.
Sai kuma ranar Juma'a, 9 ga watan Satumbar 2022 inda Asiwaju Tinubu tare da abokin takararsa Kashim Shettima, da Kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da wasu jagororin yaƙin neman zaɓensa s**a gudanar da sallar Juma'a a masallacin Sanusi Ɗantata dake Abuja.
Bugu da ƙari, Tinubu da Shettima sun karɓi baƙoncin ƙungiyar manoma masu goyon bayan Asiwaju daga shiyyoyi shidda na Najeriya a ofishin yaƙin neman zaɓensa dake Abuja. A jawabinsa yayin ganawar, Tinubu ya yi alƙawarin kashe maƙudan kuɗaɗe a harkar noma tare da sarrafa amfanin gona domin tabbatar da samun ƙarin isashshen abinci a Najeriya.
Kamar yadda na saba, ba zan ƙarƙare ba sai na nanata muhimmancin kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna dake tsakanin BAT da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima. Su kaɗai ne a yanzu za a iya cewa tabbas abokan takara ne, kuma hakan abin a yaba ne.
Ku kasance tare da ni a mako mai zuwa don cigaban . Na barku lafiya.