28/11/2025
An gurfanar da wani matashi mai suna Ayuba Isa a Babbar Kotun Jihar Kano, bisa tuhumarsa da caka wa abokinsa Ibrahim Dan Larai, wuƙa har lahira saboda yawan tashinsa sallar asuba da yake yi.
Bayan sauraron shaidu uku a zaman kotun na yau, Alƙalin kotun, Mai Shari'a Dije Abdu Aboki, ta ɗage shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Janairun 2026.
Tun da farko an gurfanar da wanda ake zargin ne, bayan caka wa abokinsa wuƙa, lokacin da ya je tashinsa su tafi sallar asuba a masallaci, lamarin da ya fusata Ayuban har ya kai ga caka wa abokin nasa wuƙa.