10/07/2026
Ministan tsaron Najeriya Janr Christopher Musa mai ritaya, ya yi kira ga sojoji da su rika kashe ƴan ta'adda da sauran ƴan bindiga da zatar sun ci karo da su ba tare da jiran umarni daga kowa ba - ko kuma a ɗauke su a matsayin masu aikata laifuka irin na ta'addanci.
Musa wanda ya yi wannan kira ranar Laraba a Sokoto, yayin bikin kaɗɗamar da motoci masu sulke 62 da babura 320 da gwamnatin jihar ta saya, domin rabawa hukumomin tsaro daban-daban da ke aiki a jihar, ya ce "Ina mai tabbatar da cewa, duk wanda ya ƙi harbi ko kashe wani ɗan fashi ko ɗan ta'adda da sunan yana jiran umarni, mu ma za mu ɗauke ka a matsayin ɗan ta'adda.
RRC Hausa Facebook _ hoto-RFI Hausa