10/10/2025
Gaban nin Babban taron ACF Wazirin Dutse ya jaddada bukatar hadin kai, da zaman lafiya.
Daga; Babangida Aliyu Abdullahi
Kaduna
Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF), Alhaji Bashir M. Dalhatu, Wazirin Dutse, ya bayyana godiya ga mambobin kungiyar bisa jajircewarsu wajen kare manufofin hadin kai, zaman lafiya da cigaban Arewa.
Yayin jawabin sa a taron Kwamitin Amintattu da aka gudanar a ranar Talata, 7 ga Oktoba, 2025, a cibiyar ACF dake Kaduna, ya ce taron nasu ya hada da shugabannin jihohi, sakatarori da mambobin kungiyar Arewa saboda muhimmancin batutuwan da aka shirya tattaunawa a kai.
Ya bayyana cewa manyan abubuwan da s**a mamaye ajandar taron su ne batun tsarin yadda jami’an ACF ke hulɗa da kafafen watsa labarai, da kuma shirin bikin cika shekaru 25 da kafa kungiyar da za a haddasa daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Nuwamba, 2025.
Alhaji Dalhatu ya jaddada bukatar samar da tsayayyen tsarin sadarwa domin kaucewa sabanin juna a maganganun jami’an kungiya, inda ya bayyana cewa Kwamitin Amintattu ne ke da hakkin tsara da tabbatar da irin wadannan ka’idoji.
Ya kuma tunatar da tanadin kundin tsarin mulkin ACF da ke baiwa Kwamitin ikon yanke hukunci mai ɗaurewa kan lamurran cikin gida.
Game da shirin bikin cika shekaru 25, Wazirin Dutse ya bayyana cewa ana sa ran taron zai mayar da hankali wajen tara kudade don gina babban ofishin ACF na kasa, kaddamar da asusun tallafi na mata da matasa, da kuma gabatar da littattafai da ke bayyana tarihin kungiyar.
Dalhatu ya yaba wa kwamitocin shirye-shirye bisa irin kokarinsu, tare da kira ga dukkan mambobin ACF su halarci wannan gagarumin biki a Kaduna a matsayin jakadu nagari na kungiya.
Alhaji Dalhatu ya kuma tunatar da mambobin ACF su ci gaba da zama tsaka-tsaki a siyasa, yana mai jaddada cewa duk da cewa mambobi na iya kasancewa cikin jam’iyyun siyasa daban-daban, ACF a matsayinta na kungiya tana nan daram a matsayin mara goyon bayan kowace jam’iyya.
Ya bayyana cewa rawar da kungiyar ke takawa ita ce bayyana irin nagartattun halayen da ake bukata daga ‘yan takara da kuma tallafawa dimokuraɗiyya, kyakkyawan mulki da hadin kan kasa.
Shugaban Kwamitin Amintattu ya nuna damuwa kan yawaitar kafa kungiyoyi a Arewa da ke da manufofi makamancin na ACF. Ya ce irin wadannan ƙungiyoyi suna rage karfin hadin kan Arewa, tare da kira ga wadanda suke kafa kungiyoyin irin haka da su dawo cikin ACF.
Ya tunatar da cewa a shekara ta 2000, manyan shugabannin Arewa, ciki har da tsoffin shugabannin kasa, gwamnoni, sarakuna da malamai, sun hade kungiyoyi da dama domin kafa ACF bisa ruhin hadin kai da cigaba.
Dangane da matsalar tsaro, Alhaji Dalhatu ya bayyana godiya ga dakarun soji da jami’an tsaro saboda sadaukar da rayukansu wajen yaki da ta’addanci da ‘yan bindiga. Ya roki Allah Ya jikan wadanda s**a rasa rayukansu, tare da kira da a ci gaba da sabunta dabaru domin rage asarar rayuka da tabbatar da zaman lafiya a Arewa baki daya.
Wazin na Dutse ya kuma nuna takaici kan matsalolin da s**a taso a matatar man Aliko Dangote, yana mai kiran su a matsayin yunƙurin lalata tattalin arzikin kasa.
Ya ce matatar man ta taimaka wajen kawo karshen karancin mai da daidaita tattalin arziki, don haka gwamnati ta dauki matakin gaggawa don kare muradun jama’a.
A karshe, Wazirin Dutse ya gode wa mambobin da s**a halarci taron, zahiri da ta yanar gizo saboda jajircewarsu wajen ci gaban kungiyar ACF.